Farashin Mai Ya Sauka Sosai bayan Dakatar da Yakin Amurka da Iran

Farashin Mai Ya Sauka Sosai bayan Dakatar da Yakin Amurka da Iran

  • Farashin ɗanyen man fetur ya yi mummunar faɗuwa bayan dakatar da arangamar Amurka da Iran, inda Brent ya sauka da kaso 11.3 cikin 100
  • Shugaba Donald Trump ya ce Amurka ta dakatar da hare-hare ne bisa buƙatar Iran, amma ya yi barazanar ci gaba da kai farmaki idan ba a cimma sabon tsagaita wuta ba
  • Masana sun yi gargadin cewa har yanzu barazanar hare-hare a mashigar Hormuz da Bahar Maliya na iya sake dagula kasuwar man fetur ta duniya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Washington, D.C. – Farashin ɗanyen man fetur a kasuwannin duniya ya yi ƙasa sosai bayan an samu an dakatar da arangamar da ke tsakanin Amurka da Iran.

Faɗuwar farashin ita ce mafi girma tun farkon watan Afrilun 2026, inda farashin Brent, wanda ake amfani da shi a matsayin ma'aunin duniya, ya sauka da 11.3% yayin da ɗanyen man Amurka ya ragu da kusan 7%.

Kara karanta wannan

Trump ya yi maganganu da aka 'gano' makaman Amurka na neman karewa

Mutane na layin gidan mai
Yadda abubuwan hawa ke shai mai a Najeriya. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

CNN ta rahoto cewa wannan sauyin ya biyo bayan sanarwar shugaban Amurka, Donald Trump, cewa ƙasarsa ta dakatar da sababbin hare-hare kan Iran bisa buƙatar gwamnatin Tehran.

Trump ya yi barazanar kai hari

Trump ya bayyana cewa dakatar da hare-haren ba yana nufin rikicin ya ƙare ba, yana mai gargadin cewa Amurka za ta ci gaba da kai farmaki idan ba a cimma sabon yarjejeniyar tsagaita wuta ba.

Sai dai ma'aikatar harkokin wajen Iran ta ce a halin yanzu babu wata tattaunawa da ake yi tsakaninta da Amurka kan batun sulhu.

A lokaci guda kuma, an sanar da cewa jami'an Isra'ila da Lebanon za su gana a birnin Rome mako mai zuwa domin ci gaba da tattaunawar aiwatar da yarjejeniyar zaman lafiya da Amurka ke shiga tsakani.

Har yanzu akwai fargabar yaki

Duk da raguwar farashin mai, masana sun bayyana cewa har yanzu kasuwar na fuskantar rashin tabbas saboda yiwuwar ƙarin hare-hare a yankin Gabas ta Tsakiya.

Kara karanta wannan

Amurka ta fara fuskantar matsalar makamai, Trump ya dakatar da hare hare kan Iran

Rahoton BBC ya nuna cewa zirga-zirgar jiragen ruwa ta mashigar Hormuz ta yi ƙasa sosai idan aka kwatanta da yadda take kafin rikicin.

Shugaba Donald Trump
Donald Trump yayin taron siyasa a Amurka. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Masana na Deutsche Bank sun yi gargadin cewa hare-haren da mayaƙan Houthi za su iya kai wa tankokin mai na Saudiyya a mashigar Bab al-Mandeb na iya janyo tangarɗa ga hanyoyin fitar da mai ta Tekun Fasha da Bahar Maliya a lokaci guda.

Trump ya je kamfen a Amurka

A wani labarin, mun ruwaito cewa shugaban Amurka, Donald Trump, ya ce ya fi iyayen ma'aikatan masana'antar motoci a jihar Michigan taimaka musu wajen inganta rayuwarsu.

Trump ya yi wannan furuci ne yayin wani jawabi da ya gabatar a jihar Michigan, inda ya kare manufofinsa kan tattalin arziki tare da nuna goyon baya ga ɗan takarar jam'iyyar Republican, Mike Rogers.

Kalaman shugaban sun jawo muhawara, yayin da masu sukar sa suka ce jawabin ya fi kama da gangamin yaƙin neman zaɓe fiye da bayani kan manufofin gwamnati.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng