Yan Sanda Sun Yi Musayar Wuta ana Tsaka Da Garkuwa da Mutane a Hanyar Kano
- Rundunar yan sanda sun ceto wasu daga cikin mutane 13 da aka yi garkuwa da su bayan harin 'yan bindiga a hanyar zuwa Kano
- Wasu ƴan bindiga da su ka yi kwanton bauna a hanyar sun tare wata mota ɗauke da fasinjoji akalla 20 kafin a yi gumurzu da su
- Rundunar ta bayyana cewa an dauki lokaci ana fafatawa a tsakanin yan bindiga da jami'an kafin a kai ga ceto wasu fasinjoji
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Rundunar 'Yan Sandan Jihar Kano ta sanar da ceto fasinjoji tara bayan da wasu da ake zargin 'yan bindiga ne suka kai hari kan motar haya a kan hanyar Jos zuwa Kano.
Mai magana da yawun rundunar, SP Abdullahi Haruna, ne ya bayyana hakan a cikin wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin 27 ga wagan Yuli, 2027.

Source: Facebook
Jaridar Punch ta wallafa cewa sanarwar ta ce lamarin ya faru ne ranar 26 ga Yulin 2026 da 5.30 na yamma, bayan jami'in kula da ofishin 'yan sanda na Doguwa (DPO) ya samu kiran gaggawa.
Yan sandan Kano sun kai dauki
Jaridar Daily Post ta ruwaito cewa wasu mahara sun tare motar Toyota Hiace mai lambar rajista BKK 6824 XA a yankin dajin Falgore da ke karamar hukumar Doguwa, tsakanin Gate Two Safer Highway da Dogo Dutse.
Sanarwar ta ce:
"Bisa ga rahoton da aka samu, wasu mutum biyar da ake zargin 'yan bindiga ne dauke da adduna da bindiga guda daya sun tare hanya, suka kai hari kan motar tare da yin garkuwa da fasinjoji 13 cikin mutum 20 da ke cikinta."
Rundunar ta ce nan take DPO ya tattara jami'an rundunar na musamman suka nufi wurin da lamarin ya faru, inda suka yi musayar wuta da maharan.
Sanarwar ta kara da cewa:
"Sakamakon daukar matakin gaggawa da jami'an 'yan sanda suka yi cikin hadin kai, an samu nasarar ceto mutum tara. Daga baya kuma wani namiji ya tsere daga hannun masu garkuwa. Abin takaici, har yanzu mutum uku na hannun masu garkuwa, wadanda suka hada da namiji daya da mata biyu."
Yan sanda sun mika jama'a asibiti
An ce an garzaya da wadanda aka ceto zuwa Asibitin Kwararru na Doguwa domin duba lafiyarsu, kuma suna samun kulawa yayin da aka tabbatar da cewa yanayinsu ya daidaita.
Rundunar ta ce ta kara tura jami'an musamman tare da karfafa tattara bayanan sirri domin kubutar da sauran mutanen da ke hannun masu garkuwa da kuma cafke wadanda suka tsere.

Source: Original
A cewar sanarwar:
"Wannan gagarumar nasara ta nuna kudurin Rundunar 'Yan Sandan Najeriya karkashin jagorancin Sufeto Janar na 'Yan Sanda na tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyi ta hanyar daukar matakin gaggawa da kuma hadin gwiwa da al'umma."
Kwamishinan 'Yan Sandan Jihar Kano, Ibrahim Bakori, ya yaba wa mazauna yankin da masu amfani da hanyar saboda ba da sahihan bayanan gaggawa.
Ya kuma tabbatar wa al'ummar jihar cewa rundunar za ta ci gaba da kare rayuka da dukiyoyi.
Yan sanda a Filato sun yi korafi
A baya, mun kawo labarin cewa yan sandan MOPOL da ke aikin samar da zaman lafiya a jihar Filato sun ce ba a biya su alawus na watanni bakwai ba har yanzu.
Jami'an bayyana wadanda su ke zargi a cikin 'yan sanda da karkatar da kudin alawus da gwamnatin Filato ke fitarwa domin a ba su kamar yadda doka ta tanada.
Sun roki Sufeto Janar na 'Yan Sanda Kayode Egbetokun da ya gaggauta duba na tsanaki tare da kawo masu dauki domin a bibiya tare da sakin hakkinsu.
Asali: Legit.ng


