An Goyi Bayan Harbe 'Yan Ta'adda da Zarar an Gan Su ba Tare da Jiran Izini ba
- Sanata Adams Oshiomhole ya ce ya kamata jami'an tsaro su riƙa harbin masu aikata laifi masu ɗauke da makamai nan take ba tare da wata shakka ba
- Tsohon gwamnan jihar Edo ya soki abin da ya kira nuna sassauci daga Sufeto Janar na 'Yan Sanda kan batun amfani da makamai
- Ya kuma ce rashin tsaro ne babban ƙalubalen da ka iya kawo cikas ga sake zaɓen Bola Tinubu, yana mai buƙatar a ɗaura wa hafsoshin tsaro alhakin kawo ƙarshensa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
FCT, Abuja – Sanata mai wakiltar Edo ta Arewa, Adams Oshiomhole, ya bayyana cewa ya dace jami'an tsaro su riƙa harbin masu aikata laifi da ke ɗauke da makamai nan take idan suka ci karo da su.
Hakan na zuwa ne yayin da Najeriya ke cigaba da fama da matsalolin tsaro da suka kawo hasarar rayuka da duniyoyi a fadin kasar.

Source: Twitter
Oshiomhole ya bayyana hakan ne yayin wata hira da ya yi da gidan talabijin na TVC, inda ya kuma soki abin da ya kira nuna sassauci daga Sufeto Janar na 'Yan Sanda, Olatunji Disu, kan batun amfani da makamai.
Oshiomhole ya soki 'yan sanda
Tsohon gwamnan jihar Edo ya ce bai ga dalilin da zai sa a nuna wata damuwa ba idan jami'an tsaro suka harbi masu aikata laifuffuka masu ɗauke da makamai.
Punch ta rahoto cewa kalaman nasa sun zo ne bayan rundunar 'yan sanda ta fayyace cewa Sufeto Janar bai bayar da umarnin "harbi nan take ba" sai dai ya yi nuni da tanade-tanaden dokar su da ke tsara lokacin da jami'an tsaro za su iya harbi.
Sanatan ya kuma yabawa Hukumar Tsaro ta DSS kan ɗaukaka ƙarar wata shari'a da kotu ta yanke hukuncin ɗaurin rai da rai maimakon hukuncin kisa ga wasu da aka samu da laifi.

Source: Twitter
A cewarsa, alkalai su riƙa aiwatar da doka yadda ta tanada ba tare da barin ra'ayinsu na ƙashin kansu ya rinjaye su ba.
Magana kan sake zaɓen Tinubu
Oshiomhole ya bayyana cewa babban abin da ka iya kawo cikas ga yunƙurin shugaban ƙasa, Bola Ahmed Tinubu, na sake lashe zaɓe shi ne matsalar rashin tsaro.
Ya buƙaci shugaban ƙasar ya sanya wa hafsoshin tsaro wa'adin kawo ƙarshen rashin tsaro cikin watanni masu zuwa tare da tabbatar da cewa ana tantance aikinsu bisa sakamakon da suke samarwa.
Ya ƙara da cewa gwamnatin Tinubu ta riga ta ɗauki matakan inganta tattalin arziki, amma matsalar rashin tsaro ce har yanzu ke ci gaba da damun 'yan Najeriya.
'Yan bindiga sun kashe mutum 30
A wani labarin, mun ruwaito cewa wasu 'yan bindiga sun kai hari ƙauyen Naridon da ke ƙaramar hukumar Kaura a jihar Kaduna, inda suka kashe akalla mutum 30 tare da jikkata wasu da dama.
Wani mazaunin yankin, Derek Christopher, ya ce wannan ba shi ne karon farko da aka kai wa ƙauyen hari ba, yana mai zargin gwamnati da gaza kare al'ummar yankin.
Wani mazaunin yankin mai suna Raphael Joshua ya ce an kai gawarwakin waɗanda aka kashe wani asibiti da ke kusa, yayin da ake shirye-shiryen yi masu jana'iza.
Asali: Legit.ng


