Yadda Jami'ai Suka Yi Dauki ba Dadi da Yan Bindiga 200 a Katsina

Yadda Jami'ai Suka Yi Dauki ba Dadi da Yan Bindiga 200 a Katsina

  • Jami'an tsaro hadin gwiwa sun samu nasarar kashe 'yan bindiga da dama yayin da aka dakile hari a kauyen Guga da ke jihar Katsina
  • Rahotanni sun ce fiye da 'yan bindiga 200 ne suka yi zuga wajen kai harin ƙarƙashin jagorancin kasurgumin dan ta'adda, Idi Abasu Aiki
  • Gwamnatin Katsina ta tabbatar da mutuwar mafarauta biyar tare da yabawa sadaukarwarsu wajen kare rayuka da dukiyoyin al'umma

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Katsina – Fiye da mutum 40 da ake zargin 'yan bindiga suka mutu a ranar Lahadi bayan jami'an tsaro da hadin gwiwar mafarauta da rundunar KSCWC suka fatattaki wani gagarumin hari da aka kai kauyen Guga da ke ƙaramar hukumar Bakori a jihar Katsina.

Majiyoyi sun shaida cewa lamarin ya faru da 5.40 na yammacin ranar 26 ga Yuli, 2026 lokacin da fiye da 'yan bindiga 200 dauke da manyan makamai suka kutsa cikin al'ummar.

Kara karanta wannan

'Yan daba sun afka dakin kwanan dalibai mata na jami'ar ATBU, an yi barna mai girma

Sojoji sun kora yan ta'adda
Wasu daga cikin dakarun sojin Najeriya a jihar Borno Hoto: JORIS BOLOMEY/AFP via Getty Images
Source: Getty Images

Jaridar Punch ta kawo labarin cewa J'jami'an tsaro sun bayyana harin a matsayin harin ramuwar gayya da aka tsara a kan al'ummar yankunan.

Yadda yan bindiga suka kai hari Katsina

The Nation ta wallafa cewa rahotannin sirri sun ce shahararren shugaban 'yan bindiga, Idi Abasu Aiki, ne ya jagoranci harin tare da wasu mayaƙa masu alaƙa da ƙungiyar Ado Aleru da ke aiki daga jihar Zamfara.

A cewar rahotannin sirri, manufar maharan ita ce su murƙushe mafarauta da jami'an KSCWC da ke kare yankin kafin su faɗaɗa harin zuwa garin Bakori da sauran ƙauyukan da ke kusa.

Sai dai bayan samun bayanan sirri tun kafin harin, jami'an tsaro sun shirya martanin haɗin gwiwa wanda ya haifar da mummunan musayar wuta, lamarin da ya tilasta wa maharan ja da baya bayan sun yi asara mai yawa.

An kashe wasu daga cikin dakarun sa kai a Katsina
Taswirar jihar Katsina mai fama da matsalar yan bindiga Hoto: Legit.ng
Source: Original

Binciken jami'an tsaro ya nuna cewa an kashe sama da 'yan bindiga 40 a fafatawar, yayin da bayanan sirri na baya suka tabbatar da cewa kusan manyan kwamandoji takwas na wannan ƙungiyar masu aikata laifuffuka suna cikin waɗanda aka kashe.

Kara karanta wannan

Yan sanda sun yi musayar wuta ana tsaka da garkuwa da mutane a hanyar Kano

Majiyoyin sun kuma bayyana cewa Idi Abasu Aiki ya samu munanan raunukan harbin bindiga da aka ce na iya jefa rayuwarsa cikin haɗari yayin musayar wutar.

Dalilin sabon hari a Katsina

Wannan farmaki ya biyo bayan wata arangama da aka yi a ranar 7 ga Yuli 2026 a kauyen Dawan Laila, inda aka ce wannan ƙungiyar ta 'yan bindigar ta yi asara mai yawa bayan gumurzu da masu sa kai na tsaro.

A halin yanzu, jami'an tsaro sun fara aikin share fage a yankin domin kwato makamai da sauran kayan da 'yan bindigar suka bari yayin da suke tserewa tare da kara sa ido.

A gefe guda, gwamnatin jihar Katsina ta tabbatar da cewa mafarauta biyar sun rasa rayukansu a yayin aikin, bayan sun faɗa hannun maharan lokacin da suka fita wajen fagen daga domin yin wasu sayayya na kansu.

Gwamnatin ta bayyana mafarautan da suka mutu a matsayin jarumai masu kishin ƙasa da suka sadaukar da rayuwarsu wajen kare al'ummominsu, tare da miƙa ta'aziyya ga iyalansu.

Sojoji sun gwabza da yan bindiga a Katsina

Kara karanta wannan

Yan sandan MOPOL sun nemi agajin Sufeton Ƴan sanda watanni 7 da hana su alawus

A baya, kun samu labarin cewa sojojin saman Najeriya (NAF) sun kammala bincike na ƙarshe na karɓar rukunin farko na jiragen yaƙi guda uku samfurin M-346 daga ƙasar Italiya domin taimaka wa bangaren tsaro.

Wannan mataki zai taimaka sosai wajen inganta ƙwararrun ma'aikata da kuma ɗaga darajar NAF wajen kai hare-hare cikin sauri da kare ƙasa daga farmakin yan ta'adda da sauran bata gari da ke addabar jama'a.

Wannan na zuwa ne a zamanin gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu a matsayin wani ɓangare na kokarin zamantar da kayan aikin soji na ƙasa domin tukarar matsalolin rashi tsaro da ake fama da su.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng