Kwankwaso da Wasu Gwamnonin Najeriya da Suka Taba Mikawa Mataimakansu Mulki
Kano - A siyasar Najeriya, dangantaka tsakanin gwamna da mataimakinsa tamkar wasan kwaikwayo ce mai cike da sarkakiya; wasan ne da ke bukatar biyayya, ɓoye buri, da kuma nuna dabarun neman mulki a taka tsan-tsan.
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.
Mataimakan gwamnoni da dama sukan zauna a innuwar iyayen gidansu, suna kwantar da kai matsayin amintaccen bawa da ke jiran ranar da za a ba shi ragamar masarauta.

Source: Twitter
Mataimaka da dama suna share shekaru takwas suna biyayya da fatan idan lokacin da wa'adin maigidansu ya zo kare wa, zai naɗa su a matsayin magada, in ji rahoton Leadership.
Yayin da amincewa da goyon baya daga gwamna kan iya zama silar nasara ga mataimakansu, a hannu daya kuma, goyon bayan na iya zama silar shan kaye mai raɗaɗi a ranar zaɓe.
Gwamnonin da suka goyi bayan mataimakansu
A wannan rahoto, Legit Hausa ta jero wasu gwamnonin Najeriya da suka goyi bayan mataimakansu suka zama gwamnoni, da wadanda goyon bayansu bai yi tasiri ba a rumfar zaɓe:
1. Rabiu Musa Kwankwaso (Kano)

Source: Twitter
Tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, ya tsaya tsayin daka wajen ganin mataimakinsa, Abdullahi Umar Ganduje, ya gaje shi a zaɓen 2015.
Kwankwaso ya yi amfani da dukkan ƙarfinsa da tasirin jam’iyyar APC na wancan lokacin wajen ba wa Ganduje damar samun nasara.
A zaɓen 2015, Ganduje ya doke babban ɗan takarar PDP, Salihu Sagir Takai, bayan ya samu ƙuri'u 1,546,434 yayin da shi Takai ya samu kuri'u 509,726 kamar yadda Channels TV ta ruwaito.
Duk da irin wannan kauna da ke tsakaninsu, baraka ta zo ta shiga tsakanin Kwankwaso da Ganduje, lamarin da ya sa suka koma abokan gaba.
2. Ahmad Sani Yerima (Zamfara)

Source: Twitter
Idan ana maganar goyon bayan mataimaki har ya ci zabe cikin lumana, to ba za a manta da Jihar Zamfara ba, inda Gwamna Ahmad Sani Yerima (1999–2007) ya goyi bayan mataimakinsa, Mahmud Aliyu Shinkafi ya lashe zaben gwamna.
Da taimakon ikon gwamnati da na jam’iyyar ANPP, Shinkafi ya lashe zaɓen 2007 ba tare da ya sha wata wahala ba, in ji rahoton Daily Trust.
Shinkafi ya mulki Zamfara na tsawon shekaru huɗu, kodayake daga baya ya sauya sheƙa zuwa jam'iyyar PDP, matakin da aka yi zargin ya kawo karshen zumuncin siyasarsa da Yerima.
3. Mohammed Badaru Abubakar (Jigawa)

Source: Twitter
A jihar Jigawa ma, tsohon gwamna Mohammed Badaru Abubakar ya ba da mamaki wajen marawa mataimakinsa, Umar Namadi, baya a zaɓen 2023.
Tun farko, Namadi mutumin Badaru ne tun yana kwamishinan kuɗi, sannan ya zama mataimakinsa a 2019.
Saboda amincin da ke tsakaninsu, Namadi ya sami tikitin APC cikin sauƙi kuma ya lashe zaɓen gwamna da gagarumin rinjaye, inda ya samu kuri'u 618,449, cewar rahoton Premium Times.
4. Abdullahi Umar Ganduje (Kano)

Source: Twitter
Kaddara ta juya wa Ganduje baya lokacin da ya so ya kwaikwayi abin da Kwankwaso ya yi masa. Shi ma ya tsayar da mataimakinsa, Nasiru Yusuf Gawuna, domin ya gaje shi a zaɓen 2023.
Duk da iko da kuɗin da aka ce Ganduje ya narka a takarar Gawuna, hakan bai kai shi ga gaci ba, ya sha kaye a hannun ɗan takarar NNPP, Abba Kabir Yusuf, da tazarar ƙuri'u da suka haura 100,000.
Kodayake an tafi kotu har zuwa matakin ƙarshe, Kotun Ƙoli ta tabbatar da cewa Abba Kabir ne halastaccen gwamnan Kano, in ji rahoton ICRI.
5. Babajide Sanwo-Olu (Legas)

Source: Twitter
Yanzu idanu sun koma jihar Legas, inda Gwamna Babajide Sanwo-Olu ya riga ya zaɓi mataimakinsa, Dr. Obafemi Hamzat, a matsayin magajinsa a 2027.
Wannan sanarwa da aka yi a watan Afrilun 2026 ta sami babban goyon baya daga manyan iyayen jam'iyyar, ciki har da Shugaba Bola Tinubu, in ji rahoton Vanguard.
Sanwo-Olu ya bayyana cewa Hamzat mutum ne mai ilimi da sanin aiki, kuma ya cancanci ya jagoranci Legas. Tuni dai ƙungiyoyi daban-daban a jihar suka fara gangamin ganin cewa wannan buri ya tabbata.
Rikici tsakanin gwamnoni da mataimakansu
A wani labari, mun ruwaito cewa, rikicin siyasa tsakanin wasu gwamnoni da mataimakansu na barazana game ci gaba da kasancewarsu zuwa zaben 2027.
A jihohi kamar Niger da Taraba, matsaloli irin su rikici tsakanin shugabanni da rashin lafiya na iya hana mataimakan gwamnoni tsayawa.
Duk da kyakkyawar alaka a Plateau, shekarun mataimakiyar gwamna Josephine Piyo na iya hana ta ci gaba da takara mai zuwa.
Asali: Legit.ng


