Rikicin Kwankwaso da Ganduje ya ruruta ayyukan yan bangan siyasa a jihar, jama’a sun koka
Al’ummar jihar Kano sun fara kokawa sakamakon yadda ayyukan yan daba da kauraye dake bangan siyasa suka yi dawayya a jihar tun bayan barkewar rikita rikitan siyasa tsakanin Ganduje da Kwankwaso.
Wani bincike da jaridar Daily Trust ta yi ya nuna magoya bayan gwamnan jihar Abdullahi Umar Ganduje, da na tsohon gwamnan jihar, Sanata Kano ta tsakiya, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso sun yi fito na fito da juna ba sau daya ba, ba sau biyu ba, wanda yayi sanadiyyar raunata mutane da dama.
KU KARANTA: Yadda wani tsohon janar na rundunar Sojan sama yayi amfani da matarsa suka yi watandan naira miliyan 4,000
A shekarar da ta gabata, yan Kwankwasiyya da yan Gandujiyya sun far ma juna a kofar Kudu na gidan Sarkin Kano a yayin bikin hawan daushe, inda aka raunata tsohon sakataren gwamnatin jihar, Rabiu Suleiman Bichi da dan uwansa, hadimin Kwankwaso Yunusa Dangwani da Kwamared Aminu Abdulsalam.
Majiyar Legit.ng ta ruwaito an sake baiwa hammata iska a unguwar Chiranchi, inda aka jikkata mutum biyu, ciki har da kannen tsohon shugaban jam’iyyar APC na jihar, Abdullahi Abbas, bugu da kari a ranar Lahadi 4 ga watan Feburairu, an kara karawa a sakatariyar jam’iyyar, inda aka jikkata wasu matasa.
A garin Dawakin kudu ma an raunata mutane biyar a yayin wata kaurewa da aka yi a ranar litinin 5 ga watan Feburairu tsakanin Kwankwasawa da yan Gandujiyya,tare da babbaka shaguna da dama a garin Kwanar-Talatar Jido.
Wasu mazauna jihar Kano da majiyar mu ta tuntuba sun bayyana damuwarsu game da ire iren fadace fadacen da ake yi a jihar saboda siyasa, inda suka yi kira ga hukumomin da abin ya shafa da su dage don magance matsalar.
Wani mutumin Kano, Aminuddeen Yusuf Gandun Albasa yace “Iyaye na da muhimmin rawa da zasu taka wajen magance matsalar, ya zama dole su sanya idanu kan yayansu, su san inda suke zuwa, da kuma abokansu.”
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng