'Yan Bindiga Sun Yi Wa Jami'an Tsaro Kofar Rago, an Rasa Rayuka a Musayar Wuta

'Yan Bindiga Sun Yi Wa Jami'an Tsaro Kofar Rago, an Rasa Rayuka a Musayar Wuta

  • Wasu ‘yan bindiga sun yi kwanton bauna ga jami’an tsaro da ke sintiri a karamar hukumar Riyom ta jihar Plateau
  • Rahotanni sun nuna cewa maharan sun kashe jami’an tsaro biyu tare da kwace bindigoginsu a yayin harin
  • Jami’an tsaro sun kaddamar da bincike da sintiri a kauyukan da ke kusa domin gano maharan da suka kawo harin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da takwas a aikin jarida

Jos, Plateau - Wasu ‘yan bindiga sun yi kwanton bauna ga jami’an tsaro da ke sintiri a kan wata hanya a jihar Plateau.

'Yan bindigan sun farmaki jami'an tsaron ne a kan hanyar Ganawuri zuwa Sabon Gida da ke karamar hukumar Riyom ta jihar Plateau.

'Yan bindiga sun kashe jami'an tsaro
Taswirar jihar Plateau, tarayyar Najeriya Hoto: Legit.ng
Source: Original

Rahoton Vanguard ya nuna cewa ‘yan bindigar sun kashe jami’an tsaro biyu tare da kwace bindigoginsu na aiki.

Majiyoyin tsaro sun bayyana cewa lamarin ya faru ne da safiyar ranar Talata, 4 ga watan Agustan 2026 lokacin da jami’an tsaro hudu daga wurare biyu daban-daban suka kafa shingen bincike a kan hanyar.

Kara karanta wannan

'Yan ta'addan Lakurawa sun kai hari a Sokoto, an kashe jami'an tsaro da fararen hula

Yadda 'yan bindiga suka kai harin

Majiyoyin sun ce bayan kammala aikin, jami’an sun kama hanyar komawa wuraren aikinsu daban-daban.

Sai dai jami’ai biyu ba su koma ba, lamarin da ya sa takwarorinsu suka fara bincike domin gano inda suke.

Daga bisani, an gano gawarwakin jami’an biyu a wurin da aka kai harin, yayin da aka tabbatar da cewa an kwace bindigoginsu na aiki.

Sai dai, daga baya an gano babur din da jami’an tsaron suka yi amfani da shi.

An fara neman maharan

Bayan harin, jami’an tsaro sun kaddamar da bincike a kauyukan da ke kewaye domin gano maharan tare da kwato bindigogin da suka sace.

A lokacin wallafa wannan rahoto, ba a tabbatar da sunayen jami’an tsaron da aka kashe a hukumance ba.

Haka kuma, kokarin samun karin bayani daga kakakin rundunar ‘yan sandan jihar Plateau, SP Alfred Alabo, da jami’in yada labarai na Operation Enduring Peace, Kyaftin Chinonso Polycarp Oteh, bai yi nasara ba.

Kara karanta wannan

An kashe dan siyasa da 'yan bindiga suka kai kazamin hari Filato da dare

Karanta wasu karin labaran kan 'yan bindiga

'Yan bindiga sun hallaka jami'an tsaro
Shugaban rundunar 'yan sandan Najeriya, Olatunji Disu Hoto: Nigeria Police Force
Source: Facebook

'Yan bindiga sun sace basarake

A wani labarin kuma, kun ji cewa yan bindiga sun sace dagacin ƙauyen Patiko, Mallam Haruna Abubakar, a gundumar Zugurma da ke karamar hukumar Mashegu a jihar Neja.

Wani mazaunin yankin mai suna Aliyu Usman ya bayyana cewa ‘yan bindigar sun mamaye ƙauyen ne da tsakar daren ranar Juma’a, 31 ga watan Yulin 2026.

Maharan wadanda suke dauke da makamai sun riƙa harbe-harbe ba gaira ba dalili tare da kewaye gidan hakimin kafin su tafi da shi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com