Juyin Mulki: Yadda aka Raba N700m don Kifar da Gwamnatin Tinubu
- Masu bincike sun zargi tsohon gwamnan Bayelsa, Timipre Sylva, da bayar da gudunmuwar kuɗi domin yunkurin juyin mulkin 2025 ta hannun wani kamfani
- Rahotanni sun ce an raba sama da N700m ga jami'an soja, malamai da wasu fararen hula bisa umarnin Kanal Mohammed Ma'aji
- Ana zargin kuɗaɗen sun ci gaba da fita har bayan kama jagoran yunkurin juyin mulkin da jami'an kasar nan suka yi a ranar 29 ga Satumban 2025
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja - Sabbin bayanai daga binciken jami'an tsaro sun bayyana yadda ake zargin an raba kuɗaɗen da tsohon gwamnan jihar Bayelsa, Timipre Sylva, ya bayar domin tallafa wa yunkurin juyin mulkin da aka ce ya ci tura a shekarar 2025.

Kara karanta wannan
2027: Yadda Tinubu, Atiku da sauran ƴan takara ke shirin amfani da tsofaffin gwamnoni
Rahoton ya ce masu binciken sojoji suna zargin Sylva, wanda aka bayyana a matsayin babban mai ɗaukar nauyin shirin, da tura kuɗaɗen ta hanyar kamfanin Purple Waves wani kamfani da ke Abuja mai harkokin gidaje, filaye da gine-gine.

Source: Facebook
Rahoton da ya kebanta ga Premium Times ya bayyana cewa daga asusun kamfanin ne aka ce aka tura kuɗaɗen zuwa hannun wani 'dan canji, Abdullahi Sani Mohammed, wanda ake zargin ya raba kuɗaɗen bisa umarnin Kanal Mohammed Ma'aji, wanda ake zargi yana cikin jagororin shirin.
Yadda aka raba kudin juyin mulki
Rahoton ya ce an samu fiye da N5bn a asusun Purple Waves daga mabambantan hanyoyi kafin aka fara fitar da kuɗaɗen a watan Satumban 2025.
Takardun bincike sun nuna cewa tsakanin 10 zuwa 30 ga Satumban 2025, an gudanar da ma'amaloli 47, inda aka tura sama da N700m zuwa ga mutane da kamfanoni daban-daban.
Masu bincike sun ce an tsara fara aiwatar da juyin mulkin ne a ranar 1 ga Oktoba,2025 ranar samun 'yancin kan Najeriya, ko kuma 4 ga Oktoba, kafin shirin ya rushe bayan kama Kanal Ma'aji a ranar 29 ga Satumba 2025.
Sai dai rahoton ya ce duk da kama shi, Abdullahi Sani Mohammed ya ci gaba da tura kuɗaɗe ga waɗanda aka tsara za su karɓa har zuwa 30 ga Satumba, 2025 bisa umarnin da aka ce Ma'aji ya ba shi tun kafin a kama shi.

Source: Facebook
A bayanin da ya bayar wa masu bincike, Abdullahi Mohammed ya ce ya daɗe yana hulɗar kasuwancin canjin kuɗi da Kanal Ma'aji kafin wannan lamari.
Ya ce:
"Wani lokaci Oga Ma'aji kan kira ni ya tambayi farashin Dala. Wani lokaci kuma ya kan sayi $1,000, $3,000, $10,000 ko $9,000."
Ya ƙara da cewa:
"Babbar Dala da ya taɓa sayar mini ita ce $40,000 da kuma $50,000."
Wadanda aka turawa kudin juyin mulki
Daga baya ne, a cewarsa, Ma'aji ya sanar da shi cewa wasu mutane za su tura kuɗi cikin asusun kamfaninsa yayin da ake ci gaba da shiri.
Ya ce:
"Oga Ma'aji ya kira ni wajen ranar 18 ga Satumba 2025 ya ce mutanensa za su saka kuɗi a asusun. Da na duba sai na ga N150,000,000 a asusun A&A Express da ke Providus Bank."
Ya ce daga baya aka sake tura wani N150m, wanda ya sa kuɗin suka kai N300m, sannan aka ci gaba da tura wasu N100m, N50m, N100m da wani N50m zuwa wasu asusunsa.
Rahoton ya ce gaba ɗaya Abdullahi Mohammed ya karɓi N785m daga Purple Waves tsakanin 20 ga Satumba zuwa 2 ga Oktoban 2025.
Masu bincike sun ce an tura kuɗaɗen zuwa hannun jami'an soja masu aiki da waɗanda suka yi ritaya, malamai da aka nemi su yi addu'o'i, da kuma wasu fararen hula da aka ba ayyuka daban-daban.
Daga cikin waɗanda aka ambata akwai:
- Laftanar Kanal Shamsudeen Bappah – N5m
- Laftanar Felix Sunday Stephen – N5m
- Laftanar Aminu John – N10m
- Manjo Mundi Usman – N10m
- Squadron Leader Zuzu Noel Goddy – N1m
- Squadron Leader Sani Bubara Adamu – N1m
Rahoton ya ce ana zargin wasu kamfanoni ma sun karɓi kuɗaɗe, ciki har da Cutzbytz Cakes, wanda aka ce ya karɓi kuɗaɗe sau uku.
Haka kuma, an ce wani malamin addini, Goni Bukar, ya karɓi kusan N50m, inda masu bincike suka ce an ware kuɗin ne domin neman goyon bayan addu'a ga shirin.
Zargin da ake yi kan juyin mulki
A baya mun kawo labarin cewa ana ci gaba da sake samun sababbin bayanai game da zargin tsohon gwamna da ake zargi da hannu a juyin mulki da aka shirya za a yi a 2025 domin hambarar da Tinubu.
Takardun bincike sun nuna Kanar Mohammed Ma’aji ya ce tsohon gwamnan ya fara ƙin shiga shirin, amma daga baya ya canja ra'ayi bayan tattaunawa da aka yi da shi tare da bayyana mana wasu batutuwa.
Tsohon gwamnan ya musanta zargin hannu a shirin juyin mulki, yana mai cewa shi mai bin tsarin dimokuraɗiyya ne da shugaban kasa kuma har yanzu yana kasar waje inda ya fake ya ki dawo wa Najeriya
Asali: Legit.ng


