2027: Matsalolin da Ka Iya Hana Wasu Mataimakan Gwamnoni Komawa Kujerunsu
- Rikicin siyasa tsakanin wasu gwamnoni da mataimakansu na barazana game ci gaba da kasancewarsu zuwa zaben 2027
- A jihohi kamar Niger da Taraba, matsaloli irin su rikici tsakanin shugabanni da rashin lafiya na iya hana mataimakan gwamnoni tsayawa
- Duk da kyakkyawar alaka a Plateau, shekarun mataimakiyar gwamna Josephine Piyo na iya hana ta ci gaba da takara mai zuwa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Rahoton rikici tsakanin mataimakin gwamnan jihar Niger, da ubangidansa, Mohammed Umaru Bago, ya sake nuna matsalolin da ke tsakanin gwamnoni da mataimakansu.
Wannan rikici yawanci yana fitowa ne daga zargi na rashin biyayya, shisshigi daga wasu ‘yan siyasa, ko raunin karfin siyasa daga bangaren mataimaka.

Asali: Facebook
Mataimakan gwamnoni da ka iya rasa kujerunsu
A halin yanzu, gwamnoni 16 na iya neman tazarce a 2027, amma akwai alamun cewa wasu ba za su ci gaba da takara da mataimakansu na yanzu ba, cewar Daily Trust.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Baya ga Niger inda ake zargin akwai bambanci a fili, akwai wasu jihohi da ake ganin rashin jituwa duk da cewa ba a bayyana ba sosai.
1. Gwamna Bago da Garba - Niger
A jihar Niger, alakar da ke tsakanin Gwamna Umaru Bago da Yakubu Garba na nuna cewa mataimakin ba zai koma kujerarsa a 2027 ba.
Wasu majiyoyi sun ce masu fada a ji daga yankin Niger ta Gabas sun hada kai da gwamna don rage karfin siyasar Garba kafin 2031.
Majiyoyi sun ce tuni ake shirye-shirye domin canja Garba a matsayin mataimakin gwamna a zaben 2027.
Sakin jerin sunayen ‘yan takarar APC na kananan hukumomi ya kara dagula alaka, domin ana tunanin an cire dan takarar Garba daga jerin.
A karshe, an zabi Isyaku Bawa a maimakon Babangida Wasa Kudo wanda Garba ke marawa baya a karamar hukumar Shiroro.
Wasu na ganin cewa ana ci gaba da bincike a kasa domin samo wanda zai maye gurbin Yakubu Garba a 2027.

Asali: Twitter
2. Dakataccen Gwamna Fubara da Odu - Rivers
A jihar Rivers, rikicin siyasa tsakanin Gwamna Fubara da tsohon gwamna Nyesom Wike na iya hana Farfesa Ngozi Odu takara tare da gwamnan ya 2027.
An ce tsohon gwamna Peter Odili ne ya bayar da sunan Farfesa Odu lokacin da Odili da Wike ke jituwa da juna.
Tun daga 2023 Odu ta kasance mai biyayya ga Fubara duk da rikicin siyasa da ke tsakanin Fubara da Wike.
Kafin dakatar da Fubara daga aiki a watan Maris 2025, an yi rade-radin cewa Odu ta yi murabus, amma ta musanta hakan.
Ta yi shiru dangane da Wike, amma tana ci gaba da nuna biyayyarta ga dakataccen gwamna, Fubara.
Wani jigo na siyasa ya ce yuwuwar sharadin sulhu tsakanin Wike da Fubara shi ne a sauya mataimakiya da wanda Wike ya fi so.

Asali: Facebook
3. Gwamna Mutfwang da Piyo - Plateau
A Plateau, akwai jituwa sosai tsakanin Gwamna Caleb Mutfwang da mataimakiyarsa Josephine Piyo tun 2023.
Ta wakilce shi a lamuran gwamnati da dama, kuma babu wani rikici da aka ruwaito tsakaninsu zuwa yanzu.
Wani dan siyasa ya ce alakar su tafi duk wata alaka da aka gani tsakanin gwamna da mataimaki tun 1999.
Duk da haka, wasu na ganin Gwamna Mutfwang ba zai kara tsayawa tare da Piyo a 2027 saboda shekarunta ya kai 68.
A kwanan nan, wasu sun bukaci ta yi murabus kuma a nemo wanda zai gaje ta daga yankinta ko kabilarta.
An ambaci sunaye irinsu Dachung Musa Bagos da Simon Mwadkwon a matsayin masu iya maye gurbinta.

Asali: Facebook
4. Gwamna Kefas da Alkali - Taraba
A jihar Taraba, matsalar lafiya da mataimakin gwamna Alhaji Aminu Alkali ke fama da ita na hana hadin kai tsakaninsa da Gwamna Agbu Kefas.
Alkali ya kwashe kusan wata hudu a waje kafin dawowarsa kwanan nan, inda aka fara da jinyarsa a Abuja sannan aka tafi da shi Masar.
Duk da 2027 da saura tukuna, ana sa ran lafiyarsa za ta iya inganta kafin lokacin da kuma yiwuwar sauya tunani, cewar Leadership.

Asali: Facebook
Gwamna ya magantu kan alakarsa da mataimakinsa
Kun ji cewa gwamna Mohammed Umaru Bago ya musanta raɗe-raɗin da ke yawo cewa alaƙa ta yi tsami tsakaninsa da mataimakinsa, Yakubu Garba.
Gwamna Bago ya ce shi da Kwamred Yakubu Garba jirgi ɗaya ya dauko su kuma manufarsu ɗaya ta kawo ci gaba.
Bago ya bayyana cewa dangantakarsa da mataimakin gwamnan tana da kyau da armashi, inda ya buƙaci jama'a su yi watsi da jita-jita.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng