'Kuskuren da Atiku, Obi da Kwankwaso Ke Yi da Zai ba Tinubu Mulki a Sauƙi'

'Kuskuren da Atiku, Obi da Kwankwaso Ke Yi da Zai ba Tinubu Mulki a Sauƙi'

  • Tsohon jigo a jam'iyyar ADC a Najeriya, Salihu Lukman ya yi gargadin cewa yana adawa na tafka kuskure a zaben 2027
  • Ya ce rabuwar kai da fifita burin kai tsakanin manyan 'yan adawa na raunana kokarin kayar da APC, duk da yadda jama'a ke korafin matsin tattalin arziki
  • Lukman ya bukaci shugabannin adawa su koma teburin tattaunawa su kafa tsayayyen kawance, yana gargadin cewa rashin yin haka zai jawo masu matsala

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Wani tsohon jigo a jam'iyyar ADC, Salihu Mohammed Lukman ya yi gargadi kan zaben 2027 da ake tunkara.

Lukman ya bayyana damuwa cewa rashin hadin kai tsakanin shugabannin adawa zai iya tabbatar da sake zaben Shugaba Bola Ahmed Tinubu a 2027.

An gargadi Atiku, Obi da Kwankwaso kan zaben 2027
Atiku Abubakar, Shugaba Bola Tinubu da Rabi'u Kwankwaso. Hoto: Atiku Abubakar, Bayo Onanuga, Rabi'u Musa Kwankwaso.
Source: Facebook

A cikin wata sanarwa da ya fitar a Abuja ranar Alhamis, Lukman ya ce duk da korafin da jama'a ke yi kan manufofin tattalin arzikin gwamnatin APC, 'yan adawa na maimaita kuskuren baya, cewar Punch.

Kara karanta wannan

APC ta fara zare ido ga wasu na kusa da Tinubu game da zaben 2027

Gargadin tsohon ɗan ADC ga Kwankwaso, Atiku

Ya bayyana cewa Atiku Abubakar, Peter Obi, Rabiu Musa Kwankwaso da Rotimi Amaechi suna daga cikin shugabannin da ya kamata su ajiye burinsu domin samar da hadin kai.

Lukman ya ce rashin hadin kan 'yan adawa ne ya taimaka wa APC samun nasara a zabukan baya, yana mai cewa irin wannan yanayi na sake bayyana gabanin zaben 2027.

Ya tambaya cewa idan manufarsu ita ce kayar da APC da Tinubu, me ya sa ba za su iya fahimtar cewa rabuwar kai tana nufin mika nasara ga jam'iyya mai mulki ba.

Ya ce:

"Rashin haɗin kai tsakanin jam’iyyun adawa ne ya fi jawo nasarar zaɓen APC. Haka wannan yanayin yake sake bayyana yanzu, inda manyan jagororin adawa guda biyu da suka yi takara a baya suka sake fitowa a matsayin 'yan takara da za su fafata da Shugaba Tinubu."

Kara karanta wannan

APM ta ce Tinubu ya tara malaman addini ya sharara masu karya

Lukman ya gargadi ƴan adawa a Najeriya
Jigon ADC a Najeriya, Salihu Lukman. Hoto: ADC Nigeria.
Source: Facebook

'Son rai da ƴan adawa ke da shi'

Salihu Lukman ta kara da cewa bambancin da ke tsakanin manyan 'yan siyasar adawa ba shi da yawa, yana zargin cewa yawancinsu sun fi mayar da hankali kan neman tikitin takara, cewar Tribune.

Ko da yake ya amince cewa jama'a na fama da matsin tattalin arziki, Lukman ya ce babu tabbacin cewa 'yan adawa za su kawo sauyi idan ba su gina jam'iyya mai karfi ba.

Ya gargadi cewa idan ba a samar da hadin kai ba, masu kada kuri'a za su kara rasa kwarin gwiwa, sannan ya bukaci shugabannin adawa su cimma yarjejeniya domin tunkarar zaben 2027 tare.

Gargadin APC ga masu mukamai a gwamnatin Tinubu

Mun ba ku labarin cewa jam'iyyar APC ta yi gargadi ga wasu mukarraban Bola Tinubu yayin da ake shirin zaben 2027 da ake tunkara a Najeriya.

Shugaban APC Nentawe Yilwatda ya ce masu mukaman siyasa ba za su kira kansu ƙwararru kawai ba tare da taka rawar siyasa a mazabunsu ba.

Shugabannin kananan hukumomi sun ce suna da goyon bayan shugabanni da dama, tare da burin tabbatar APC ta samu akalla kashi 70 na kuri'un 2027.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.