Faston da Ya Buga da Tinubu a Fadar Shugaban Kasa Ya Sake Magana

Faston da Ya Buga da Tinubu a Fadar Shugaban Kasa Ya Sake Magana

  • Cardinal John Onaiyekan ya ce babu wata sabuwar amsa da zai bai wa Fadar Shugaban Ƙasa kan takaddamar da ta biyo bayan ganawarsu da Bola Tinubu
  • Malamin addinin ya bayyana cewa abin da bishop-bishop ɗin ke jira yanzu shi ne ganin ko gwamnatin Tinubu za ta yi amfani da shawarwarin da suka gabatar wajen inganta mulki
  • Onaiyekan ya jaddada cewa ba don kare muradun mabiya Katolika kaɗai suka gana da shugaban ƙasa ba, illa don isar da damuwar 'yan Najeriya game da shugabanci da walwalar jama'a

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja – Archbishop na Cocin Katolika a Abuja, Cardinal John Onaiyekan, ya ce shi da takwarorinsa na Ƙungiyar Bishop-Bishop na Katolika ta Najeriya (CBCN) sun riga sun isar da saƙonsu ga shugaban ƙasa Bola Ahmed Tinubu.

Kara karanta wannan

Fadawa Tinubu 'gaskiya' na neman jefa malaman addini a cikin matsala

Ya ce ba su da niyyar shiga musayar yawu da masu magana da yawun gwamnati, domin abin da ya fi muhimmanci a gare su shi ne ko gwamnati za ta gyara salon mulkinta.

Shugaba Bola Ahmed Tinubu
Lokacin da malaman addinin Kirista suka gana da Bola Tinubu. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Vanguard ta rahoto cewa Onaiyekan ya bayyana hakan ne yayin wata hira da shirin Frontline na gidan rediyon Eagle 102.5 FM da ke Ilese-Ijebu a jihar Ogun.

Onaiyekan ya yi watsi da martanin Tinubu

Da aka tambaye shi game da sukar da Fadar Shugaban Ƙasa ta yi wa bishop-bishop ɗin, Onaiyekan ya ce ba zai yi ce-ce-ku-ce kan lamarin ba.

Ya ce:

"Ba zan ma amsa wannan tambayar ba. Ba mu da wata amsa gare su. Mun riga mun yi magana, kuma abin da muke jira kawai shi ne ko maganganunmu za su yi tasiri kan yadda suke gudanar da mulki."

Ya ƙara da cewa duk abin da masu magana da yawun gwamnati ko magoya bayanta suke faɗa, alhakinsu ne, ba nasa ba.

A cewarsa, martanin da 'yan Najeriya suke bayarwa a kafafen sada zumunta ya isa ya nuna yadda jama'a suke kallon batun.

"Ba don Katolika kaɗai muka je ba"

Kara karanta wannan

Alkawarin da Shugaba Tinubu ya yi ga yan Najeriya game da addininsu

Cardinal Onaiyekan ya bayyana cewa bishop-bishop ɗin ne suka nemi ganawa da shugaban ƙasa, kuma sun shafe watanni suna jiran a ba su damar ganawar.

Ya ce manufar ziyarar ba wa'azi ba ce ko ƙoƙarin jawo shugaban ƙasa zuwa Cocin Katolika, sai dai gabatar masa da damuwarsu kan yadda ake tafiyar da ƙasa.

Daily Post ta rahoto ya ce:

"Ba mu je can a matsayin bishop-bishop na Katolika masu neman biyan wata buƙatar cocinmu ba. Mun je ne a matsayin shugabannin addini da ke da alhakin faɗin gaskiya ga kowa."
Shugaba Bola Ahmed Tinubu
Shugaba Bola Tinubu da Kashim Shettima. Hoto: Bayo Onanuga
Source: Facebook

Hadimin Tinubu ya soki Onaiyekan

A wani labarin, mun ruwaito cewa mai taimaka wa shugaban ƙasa Bola Tinubu kan harkokin yaɗa labarai, Temitope Ajayi, ya soki Cardinal John Onaiyekan kan bayyana abin da ya faru a ganawar sirri tsakanin shugaban ƙasa da bishop-bishop ɗin Katolika.

Ajayi ya ce bai dace shugaban addini ya fito yana ba da nasa fassarar abin da ya gudana a taron ba, yana mai cewa hakan ya saɓa da martabar da ake tsammani daga irin wannan matsayi.

Sai dai Onaiyekan ya dage cewa manufar ganawar ita ce isar da damuwar bishop-bishop kan tattalin arziki, tsaro da walwalar 'yan Najeriya, ba wai shiga takaddama da gwamnati ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng