Yadda tsohon Mataimakin Gwamnan jihar Kano ya canza gidan siyasa sau 6 a shekara 7

Yadda tsohon Mataimakin Gwamnan jihar Kano ya canza gidan siyasa sau 6 a shekara 7

  • A ranar 16 ga watan Nuwamba, 2021, aka ji Hafizu Abubakar, ya tsallaka zuwa bangaren Ibrahim Shekarau
  • Tsohon Mataimakin Gwamnan jihar Kano, Abubakar, ya bayyana dalilinsa na barin Dr. Abdullahi Ganduje
  • Farfesa Abubakar ya sauya-sheka daga APC zuwa PDP zuwa PRP, sai kuma ya sake dawowa jam’iyyar APC

Jaridar Daily Trust ta rahoto Farfesa Hafizu Abubakar yana bayanin abin da ya sa ya bar tsagin mai girma gwamna Abdullahi Umar Ganduje, ya bi tawagar G7.

Hafizu Abubakar yace ya bi tawagar masu adawa da tsagin gwamnati ne domin su ne a kan gaskiya, yace suna tafiya da kowa a siyasance yadda ya kamata.

“Maganar gaskiya abin da ke faruwa a jam’iyyar APC, abin takaici ne. Ba haka mu da duk magoya bayanmu, muka sa rai ba.” - Hafizu Abubakar.

Read also

Rikicin APC a Kano ya dauki sabon Salo yayin da mataimakin gwamna Ganduje ya koma tsagin Shekarau

Kowa ya san cewa jagororin APC suna fita taro suna cewa jam’iyya ta mutane uku ce a Kano – Gwamna, mai dakinsa da shugaban jam’iyya.”

Amma kafin abin da ya faru, Farfesan da ake yi wa lakabi da ‘Dan Waliyyin Allah, ya sauya-sheka kusan bila-adadin a tarihinsa, ya saba canza gida a siyasar Kano.

Tsohon Mataimakin Gwamnan jihar Kano
Farfesa Hafizu Abubakar Hoto: @officialprofhafiz
Source: Facebook

Tarihin sauya-sauyen shekarar Hafizu Abubakar

Tsakanin 1999 zuwa 2014, Hafizu Abubakar, ‘dan jam’iyyar PDP ne. Kafin zaben 2015 ya bi tsohon gwamnan Kano na lokacin, Rabiu Kwankwaso zuwa APC.

Farfesan ya cigaba da zama a APC mai mulki har zuwa Agustan 2018, inda sabaninsa da Abdullahi Ganduje ya sa ya bar kujerar mataimakin gwamna.

Bayan ‘yan watanni Abubakar ya nemi takarar gwamna a PDP, ganin hakan ba zai yiwu ba, ya raba jiha da tsohon mai gidansa, Kwankwaso a karshen shekara.

Read also

APC ta ja wa Marafa kunne da kakkausar murya, ta bayyani matakin da za ta dauka a kan shi

Daga nan Abubakar ya koma jam’iyyar PRP da sa ran zai hada-kai da Salihu Sagir Takai. Da tafiyarsu ta gagara, sai aka yi ta rade-radin ya tsallaka zuwa SDP.

Bayan zabe kuma sai aka ji Hafizu Abubakar ya dawo jam’iyyar APC. A Nuwamban 2021 ne ya sake raba jiha da gwamna Abdullahi Ganduje, ya bi ‘yan taware.

Farfesa ya bi banza bakwai a Kano?

Kwanakin baya aka ji wasu jagororin jam’iyyar APC na reshen Kano sun yi zama da kwamitin Mai Mala Buni inda suka kai karar gwamna Abdullahi Ganduje.

‘Yan jam’iyyar da suka ja daga sun hada da Sanatan Kano ta tsakiya, Ibrahim Shekarau, Sanata Barau Jibrin, Sha'aba Ibrahim Sharada da kuma Hon. Tijjani Jobe.

Source: Legit.ng

Online view pixel