2023: Ganduje ya bayyana ainahin dalilin da yasa ya tsayar da Nasiru Gawuna don ya gaje sa

2023: Ganduje ya bayyana ainahin dalilin da yasa ya tsayar da Nasiru Gawuna don ya gaje sa

  • Gwamna Abdullahi Ganduje na jihar Kano ya bayyana dalilinsa na tsayar da Nasiru Gawuna a matsayin wanda yake so ya gaje shi
  • Ganduje ya ce Gawuna mutum ne mai tsananin biyayya da kuma sanyin hali tare da sanin ya kamata
  • Har ila yau, Ganduje ya bayyana cewa sun bi ka'idojin jam'iyya wajen zabar shi a matsayin dan takarar maslaha

Kano - Gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya bayyana cewa yana so mataimakinsa, Nasiru Yusuf Gawuna, ya gaje sa ne saboda biyayyarsa.

Daily Trust ta rahoto yadda gwamnan da wasu shugabannin jam’iyyar suka tsayar da Gawuna domin ya mallaki tikitin takarar gwamna na jam’iyyar APC sannan suka lallashi kwamishinan karamar hukuma, Murtala Sule-Garo ya hakura ya zama abokin takararsa.

Kara karanta wannan

Babu abin da zai hana PDP karbe mulkin Najeriya a 2023, In ji Ayu

Siyasar Kano: Ganduje ya bayyana ainahin dalilin da yasa ya tsayar da Nasiru Gawuna don ya gaje sa
Siyasar Kano: Ganduje ya bayyana ainahin dalilin da yasa ya tsayar da Nasiru Gawuna don ya gaje sa Hoto: @aaibrhim1
Asali: Facebook

An gabatar da hukuncin a taron masu ruwa da tsaki na jam’iyyar a ranar Talata sannan aka amince da shi gaba daya.

Sai dai gwamnan ya shaidawa masu ruwa da tsaki na jam’iyyar APC a Kano a ranar Talata cewa ya yanke kan Gawuna ne bayan kammala tattaunawa da dukkan masu ruwa da tsaki na jam’iyyar, inda ya kara da cewa, an bi dukkan ka’idojin jam’iyyar kafin cimma matsayar.

Shin kana da labarin da ka/ki ke son an wallafa ma ka/ki? Ka tuntubemu a info@corp.legit.ng!

An nakalto gwamnan na cewa:

“Kamar yadda gwamna ya sa mataimakinsa ya zama gwamna. A wannan karon, mataimakina Dr Nasiru Yusuf Gawuna shine zabinmu a zaben gwamna na 2023. Hakazalika zai yi takara tare da Murtala Sule Garo a matsayin abokin takararsa.”

Ganduje ya kuma bayyana Gawuna a matsayin cikakken salihi wanda ya san abin da yake daidai da wanda yake ba daidai ba. Mutum mai aminci kuma mai biyayya sosai, rahoton Vanguard.

Kara karanta wannan

Gwamnan Kano, Abdullahi Ganduje, ya karbi Fom din takara kujerar Sanata

Akwai aiki: Mai harin Gwamna a APC bai yarda da zabin da Ganduje ya yi na dauko Gawuna ba

A wani labarin, Inuwa Waya wanda yana cikin ‘yan gaba-gaba wajen neman gwamna a jihar Kano a karkashin jam’iyyar APC ba zai fasa yin takara a 2023 ba.

Daily Nigerian ta rahoto Inuwa Waya yana nuna zai kalubalanci matsayar da Gwamna Abdullahi Umar Ganduje ya dauka na fito da wanda yake so ya gaje shi.

Waya ya shaidawa jaridar zai saye fam din neman shiga takarar gwamna a jam’iyyar APC mai mulki, duk da gwamna yana tare da Nasiru Yusuf Gawuna.

Asali: Legit.ng

Online view pixel