Abubuwan da za Su Hana NDC Tarwatsewa bayan Sauya Shekar Kwankwaso
Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso da darikar siyasar Kwankwasiyya sun sauya sheka zuwa jam'iyyar NDC bayan sun bar ADC da aka karfafa domin ta kawar da Bola Tinubu daga Aso Villa.
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano - Bayan sauya shekar da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, Kwankwasiyya da Peter Obi suka yi zuwa NDC dukkaninsu sun bayyana cewa abin da ya kore su daga jam'iyyunsu na baya ne suka sake korarsu daga ADC.
A watan Maris, 2022 ne Kwankwaso ya tattara kayansa tare da magoya bayan Kwankwasiyya daga jam'iyyar PDP zuwa NNPP.

Source: Twitter
Sai dai rahoton jaridar Thisday na 2023 ya bayyana cewa manyan NNPP sun fara zargin Sanata Rabiu Musa Kwankwaso da kokarin mamaye komai a jam'iyyar, lamarin da ya jawo rikice-rikice.
Bayan Kwankwaso ya tattara ya sauya sheka zuwa ADC, a nan ma an fara samun rigingimun da suka kai ga zuwa har Kotun Koli.
Matsalolin da Kwankwasiyya ta fuskanta a ADC
Jaridar Daily Trust ta bayyana wasu daga cikin matsalolin da suka tilastawa Kwankwaso da mutanensa barin jam'iyyar suna da yawa. sun hada da:
1. Shugabanci
Daga cikin matsalolin da suka kori Kwankwaso, Peter Obi da mutanensa daga ADC da aka hadu a ciki da niyyar fatattakar Shugaban kasa Bola Tinubu akwai rikicin shugabanci.
Hukuncin Kotun Kolin Najeriya ya bayyana cewa dukkanin bangarorin ADC da ke takaddama a kan shugabanci su koma kotun kasa.
Wannan al'amari ya sanya su Kwankwaso hango matsala a jam'iyyar, inda suka shiga fargaba kan rasa wanda suke so, wato David Mark ya ci gaba da rike ADC.
2. Takara
Na biyu daga cikin matsalolin da aka fuskanta a ADC shi ne batun bangaren kasar nan da jam'iyyar za ta mika wa takarar shugaban kasa a babban zabe mai zuwa.
Premium Times ta ruwaito cewa Sanata Rabiu Musa Kwankwao da sauran wadanda sauran wadanda suka bar ADC sun bayyana cewa sun fara hango sashen da za a mika wa takara, kuma batun bai masu dadi ba.
Baya ga wadannan, su Kwankwaso sun ji storon gwamnatin Bola Tinubu za ta hana ruwa gudu ta hana ta hanyar soke rajistar jam'iyya
Yadda NDC za ta kaucewa matsalolin ADC
Bayan sauya shekar Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, Daily post ta wallafa cewa an fara samun masu adawa da mika ragamar shugabanci ga Kwankwasiyya kacokan a Kano.

Source: Facebook
Daga cikin abubuwan da suka fara rusa hadakar yan adawa a ADC akwai batun Nafiu'u Bala, wanda ke ganin an yi masu ture kaza kwashe kwai.
Daga cikin abubuwan da Kwankwasiyya za ta yi a NDC don kauce wa hakan akwai;
1. Magance rikicin shugabanci
Jaridar Punch ta kawo rahoton yadda NDC ta fara shawo kan wannan barazana ta shugabanci kamar yadda aka samu a ADC.
Magance matsalar shugabanci, musamman wanda zai kai ga zuwa a kotu gabanin fara harkokin siyasar 2027 zai taka rawa wajen dunkule NDC gabanin zaben.
2. Warware batun takara
'Daya daga cikin kalubalen da Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso zai fuskanta shi ne ya nemi takarar shugaban kasa, musamman yayin da ake muhawarar cewa Kudu ne ya dace ya kara shekara hudu a Aso Rock.
A baya jaridar The Cable ta ruwaito Kwankwaso na cewa zai koma jam'iyyar da za ta ba shi takarar mataimakin shugaban kasa ne kawai a Najeriya.

Source: Twitter
Yayin aka rika zargin ADC na take-taken ba wa 'dan Arewa takara, wannan ya kara ta'azzara matsala a jam'iyyar.
NDC za ta iya kaucewa wannan matsala ta hanyar mika takara ga 'dan Kudu, yayin da Sanata Kwankwaso zai iya samun damar zuwa a mataimakin gwamna.
Legit ta samu ganawa da Habib Mai Lemo, Mai magana da yawun Kwankwasiyya, wanda ya bayyana cewa akwai muhimman abubuwa da za su hana sake faruwar matsalolin da aka fuskanta a haɗakar adawa ta ADC.
Ya kuma yi zargin cewa Gwamnatin shugaba Bola Ahmed Tinubu da jam’iyyar APC ne suka taka rawa wajen jawo matsalolin shugabanci da suka addabi jam’iyyar ADC a baya.
Ya ce:
“Ko su wancan matsalolin, mafi yawansu ƙirƙirar su aka yi. Gwamnati ce ta yi amfani da wasu mutane tare da amfani da hukumomi domin tabbatar da cewa an haifar da waɗannan matsalolin.”
Game da rikicin shugabanci, ya ce zai yi wahala a samu rabuwar kai a NDC kamar yadda aka samu a ADC.

Kara karanta wannan
NDC: Kwankwaso ya mika sakon kar ta kwana gabanin rufe rajistar jam'iyyu a Najeriya
A kalamansa:
“Babu maganar wani da zai ce maka wannan jam’iyya tasa ce ko ta wani. Za ta zama jam’iyya ce da gaba ɗayanmu muka taru muka gina ta tare.”
Rikici ya tunkaro jam'iyyar NDC
A baya, mun wallafa cewa daya daga cikin manyan jam'iyyar ADC, Dr. Umar Ardo ya ce zai ci gaba da shari’a kan sahihancin rajistar jam’iyyar adawa ta NDC jim kadan bayan sauya shekar Sanata Rabiu Musa Kwankwaso.
Ya zargi NDC da rashin cika sharuddan rajista na INEC inda ya ce ba zai hakura ba sai ya tabbatar da cewa ya bi lamarin kamar yadda ya sha kai tsofaffin shugabannin kasar nan kamar Muhammadu Buhari gabab kotu.
Dr. Umar Ardo, wanda jigo ne a jam'iyyar ADC kuma makusancin tsohon dan takarar shugaban kasa Atiku Abubakar ya kalubalanci sahihancin jam'iyyar NDC yayin da ya sha alwashin ci gaba da bin shari'ar.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


