Zaben 2027: 'Dan Takarar Gwamnan PDP a Gombe Ya Fice daga Jam'iyyar

Zaben 2027: 'Dan Takarar Gwamnan PDP a Gombe Ya Fice daga Jam'iyyar

  • Akwai alama rikicin cikin PDP reshen jihar Gombe ya kara dagulewa bayan mai neman takarar gwamna kawo karshen zamansa a cikinta
  • Honarabul Ahmed Mohammad Yayari, da ya nemi takara gwamna a Jihar Gombe na jam’iyyar PDP a tsagin da Kabiru Tanimu Turaki ya ce ba zai iya zama a jam'iyyar ba
  • Ficewar tasa na zuwa ne yayin da PDP kan ɗan takarar gwamna na 2027 inda wasu ke kallon Farfesa Ibrahim Pantami ya yi masu kutse

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Gombe – Honarabul Ahmed Mohammad Yayari, ɗan takarar gwamnan Jihar Gombe na jam’iyyar PDP a tsagin da Kabiru Tanimu Turaki ke jagoranta, ya rabu da am’iyyar.

Yayari, wanda aka fi sani da Sardauan Gona, ya sanar da ficewarsa ne a wata wasiƙa mai kwanan wata 11 ga Agusta 2026, wadda ya aika wa shugaban PDP na mazaɓar Kalshingi da ke Ƙaramar Hukumar Akko.

Kara karanta wannan

Zaben 2027: Obi, Kwankwaso sun zauna da yan takarar gwamna 25 a NDC

Ahmed Mohammad Yayari ya fice daga jam'iyyar PDP
Hon Ahmed Mohammed Yayari da ya nemi takara a PDP Hoto: Ahmed Yayari
Source: Facebook

Rabiu Goro ya wallafa wasikar ficewa daga jam'iyyar a shafinsa na Facebook, inda Yayari ya ce ya yanke shawarar barin PDP ne bayan ya yi dogon nazari tare da tuntubar iyalansa, abokansa, shugabannin al’umma da magoya bayansa.

Dan takarar PDP ya bar jam'iyya

Jaridar Aminiya ta wallafa cewa dan takarar bai bayyana takamaiman dalilin da ya sa ya bar jam’iyyar ba, sannan bai bayyana jam’iyyar ko tafiyar siyasar da zai bi a nan gaba ba.

Yayari ya kuma gode wa shugabannin PDP da mambobin jam’iyyar bisa goyon baya da haɗin kai da suka nuna masa a lokacin da yake cikinta.

Ya buƙaci a cire sunansa daga kundin mambobin PDP na mazaɓar Kalshingi inda ya fito tare da yi wa sauran yan jam'iyya da ya bari fatan alheri.

PDP ta karbi takardar murabus

Rahotanni sun tabbatar da cewa shugaban PDP na mazaɓar Kalshingi, Alhaji Baba, ya karɓi wasiƙar murabus ɗin Yayari a ranar 12 ga Agusta.

Kara karanta wannan

Dan takarar NDC: 'Abin da ya sa Najeriya ke bukatar Obi da Kwankwaso'

Ahmed Yayari shi ne dan takarar gwamnan PDP tsakin Tanimu Turaki
Tanimu Turaki, shugaban tsagin PDP a Najeriya Hoto: Kabiru Tanimu Turaki
Source: Twitter

Tsagin Kabiru Tanimu Turaki ya gabatar da Yayari a matsayin ɗan takararsa na gwamnan Gombe a watan Yunin 2026 duk da cewa akwai Farfesa Isa Ali Pantami.

Ficewar Yayari daga PDP na zuwa ne a daidai lokacin da jam’iyyar ke fama da rikicin cikin gida da takaddama kan wanda zai wakilci ta a zaɓen gwamnan jihar na 2027.

Murabus ɗin Yayari na iya ƙara dagula rikicin PDP a Gombe, tare da haifar da ƙarin tambayoyi kan makomar yaƙin neman zaɓen jam’iyyar a jihar.Ɗan takarar gwamnan Gombe na tsagin Turaki, Ahmed Mohammad Yayari, ya fice daga PDP.

Ana shirin karfafa Pantami

A wani labarin, kun ji cewa ana matsa wa tsohon gwamna Sanata Muhammad Danjuma Goje ana so ya sanar da fita daga jam'iyya mai mulkin Najeriya ta APC ya wuce zuwa PDP domin mara wa Farfesa Isa Pantami baya a zaben 2027.

Tsohon gwamna Ibrahim Hassan Dankwambo da Pantami na kokarin ganin Sanata Goje ya koma PDP bayan APC ta kasa ba shi tikitin takara kuma hakan zai karfafaf masu baki daya wajen tunkarar APC.

Kara karanta wannan

'Lokaci ya wuce da za a zabi mutum saboda Kwankwaso': 'Dan Majalisar Kano

Wasu daga cikin 'yan PDP na ganin cewa komawar magoya bayan Goje da abokan siyasarsa daga kananan hukumomi da shiyyoyin sanata uku na jihar zuwa PDP za ta kara wa jam’iyyar karfi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng