Shugaba Bola Tinubu Ya Tabo Maganar Raba Najeriya saboda Sabani
- Shugaba Bola Tinubu ya yi tabo maganar bambance-bambancen addini da kabila da ake fama da shi a wasu daga cikin sassan kasar
- Tinubu ya ce akwai bukatar tattaunawa da fahimtar juna domin hakan na da muhimmanci wajen tabbatar da zaman lafiya da hadin kan Najeriya
- Shi ma shugaban APC, Nentawe Yilwatda, ya gargadi ’yan siyasa kan amfani da addini da kabila domin samun riba ta siyasa da raba mutane da zaman lafiya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Shugaba Bola Tinubu ya bukaci ’yan Najeriya da su hada kai wajen kare hadin kan kasar, yana mai cewa babu wani bambanci da ya isa ya zama dalilin raba Najeriya.
Tinubu, wanda Mataimakin Shugaban Majalisar Dattawa, Barau Jibrin, ya wakilta, ya bayyana hakan ne a ranar Talata 11 ga watan Agusta, 2026 yayin taron kasa da kasa kan tsaro.

Source: Facebook
The Cable ta ruwaito cewa kungiyar Jama’atu Izalatil Bid’ah Wa Iqamatus Sunnah (JIBWIS) ce ta shirya tare da hadin gwiwar Muslim World League.
Tinubu ya yi magana kan hadin kai
A ruwayar Daily Post, Shugaban ya ce gwamnati na kokarin magance kalubalen tsaro da ke addabar Najeriya tare da hada kai da sauran kasashe domin tabbatar da zaman lafiya a duniya.
Ya ce duk da bambance-bambancen da ke tsakanin ’yan Najeriya, ya kamata su ci gaba da tattaunawa domin kare hadin kan kasar.
“Gwamnati ta kuduri aniyar tabbatar da cewa mun kasance dunkulalliyar kasa duk da bambance-bambancenmu, komai irin bambancin da yake akwai. Ya kamata mu tattauna kuma mu ci gaba da zama a wannan kasa, mu kuma bar ta ta kasance dunkulalliyar kasa.”
Tinubu ya yabi kungiyar Musulmi
Tinubu ya bayyana taron a matsayin mai muhimmanci saboda yawan kalubalen tsaro da duniya ke fuskanta, yana mai cewa shawarwarin da za a gabatar a taron za su taimaka wajen samun zaman lafiya mai dorewa a matakin yanki.

Kara karanta wannan
Saƙon da Bola Tinubu ya tura wa 'yan ɗariƙar Tijjaniyya a Najeriya da wasu ƙasashe

Source: Facebook
Ya kuma yaba wa Muslim World League saboda hadin gwiwar da ta yi da JIBWIS tare da zabar Najeriya a matsayin kasa ta farko da za ta karbi bakuncin taron.
A nasa bangaren, Shugaban Jam’iyyar APC na kasa, Farfesa Nentawe Yilwatda, ya gargadi shugabannin siyasa da su guji amfani da addini da kabilanci wajen neman moriyar siyasa.
An kakabawa Tinubu haraji
A baya, mun kawo labarin cewa gwamnatin jihar Kogi ta amince da Naira miliyan 150 a matsayin kuɗin yada fastoci da sauran abubuwan talla na yan takarar shugaban kasa a 2027.
’Yan takarar Sanata za su biya Naira miliyan 50, ’yan majalisar wakilai Naira miliyan 30, yayin da ’yan majalisar jiha za su biya N5m, inda gwamnati ta ce za a cire tallan siyasar da aka sanya ba tare da izini ba.
Kwamishinan Yada Labarai da Sadarwa na jihar, Kingsley Fanwo, ne ya bayyana hakan a Lokoja bayan wani taron masu ruwa da tsaki da masu gudanar da harkokin tallace-tallacen siyasa a jihar.
Asali: Legit.ng
