Ana Wata ga Wata: Rahoton Amurka Ya Tabbatar da Zargin Atiku kan Gwamnatin Tinubu

Ana Wata ga Wata: Rahoton Amurka Ya Tabbatar da Zargin Atiku kan Gwamnatin Tinubu

  • Atiku Abubakar ya ce wani rahoton Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ya tabbatar da korafe-korafen da ya yi kan gwamnatin Bola Tonubu
  • Rahoton ya nuna damuwa kan rashin cikakken bayani kan kudaden shiga da kashe-kashen da gwamnatin Najeriya ta yi a bara
  • Dan takarar shugaban kasa na ADC ya ce ‘yan Najeriya na da hakkin sanin yadda ake tara da kashe kudaden gwamnati

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau daNkullum

Abuja, Nigeria - Dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya ce wani sabon rahoton Amurka ya tabbatar da maganarsa kan gwamnatin Shugaba Bola Tinubu.

Atiku ya ce rahoton, wanda ma'aikatar harkokin wajen Amurka ta fitar, ya tabbatar da damuwar da ya dade yana bayyana wa kan rashin gaskiya da cikakken bayani wajen tafiyar da kudaden Najeriya.

Atiku.
Dan takarar shugaban kasa na jam'iyyar ADC, Atiku Sbubakar yana jawabi ga magoya bayansa a Abuja Hoto: Atiku Abubakar
Source: Facebook

Mataimakin Atiku kan harkokin yada labarai, Paul Ibe, ne ya bayyana hakan a wani sako da ya wallafa a shafinsa na X ranar Alhamis, 13 ga Agustan 2026.

Kara karanta wannan

Shugaba Tinubu ya maida hankali kan samar da ayyuka masu gwaɓi ga matasan Najeriya

Tun farko dai, rahoton Amurka ya soki gwamnatin tarayya kan rashin samar da cikakken bayani cikin lokaci game da kudaden shigarta da kuma abubuwan da ta kashe kudi a kansu.

Rahoton Amurka ya nuna damuwa

A cewar rahoton, gwamnatin Najeriya ta samar da kasafin kudin da aka amince da shi da kuma rahoton karshen shekara ga jama’a, ciki har da sanya su a intanet.

Sai dai rahoton ya ce gwamnati ba ta wallafa daftarin kasafin kudin zartarwa cikin lokacin da ya dace ba.

Ya kuma bayyana cewa takardun kasafin kudin ba su samar da cikakken bayani kan kudaden shiga da kashe-kashen gwamnati ba, sannan ba su yi cikakken bayani kan kudaden da ake warewa bangaren zartarwa ba.

Rahoton ya kuma nuna cewa a wasu lokuta ainihin kudaden shiga da kashe-kashen gwamnati ba su yi daidai da alkaluman da aka tanada a kasafin kudin da aka amince da shi ba.

Rahoton ya kuma nuna damuwa kan matsayin Ofishin Akanta-Janar na Tarayya, inda aka ce bai cika ka’idojin kasa da kasa na samun cikakken ‘yancin gudanar da aikinsa ba.

Kara karanta wannan

ADC ta yi zargin ana shirin kama wani babba a jam’iyyar bayan El Rufai

Atiku ya ce an tabbatar da zarginsa

Atiku ya dade yana zargin gwamnatin Shugaba Bola Ahmed Tinubu da kasa cika ka’idojin gaskiya, rikon amana da bayyana bayanan da suka shafi kudaden gwamnati.

Da yake martani kan rahoton, Atiku ya ce abin da rahoton ya kunsa ya kara tabbatar da damuwar da ya dade yana bayyana wa yan Najeriya.

Ya ce:

“Wannan rahoto ya tabbatar da abin da muke ta fada: cewa ‘yan Najeriya sun cancanci sanin daga ina kowace kobo take zuwa da kuma inda ake kashe ta. Kudadenmu ne, ba kudaden Shugaba Bola Tinubu da iyalansa da abokansa ba.”
Bola Tinubu.
Shugaban kasar Najeriya, Bola Ahmed Tinubu a fadar Aso Rock, Abuja Hoto: @OfficialABAT
Source: Facebook

Tsohon mataimakin shugaban kasar ya jaddada cewa bayyana gaskiya kan harkokin kudade na da muhimmanci ga masu zuba jari, kungiyoyin bayar da tallafi da kuma hukumomin tantance darajar bashi na kasa da kasa.

Atiku ya sake sukar gwamnatin Tinubu

A wani labarin, kun ji cewa Atiku Abubakar ya ce babu wata farfaganda da za ta iya ɓoyetsananin matsin tattalin arzikin da 'yan Najeriya ke fuskanta

Dan takarar ADC a zaben 2027 ya kalubalanci gwamnatin Bola Tinubu kan ci gaba da karɓo bashi duk da ikirarin ƙaruwa a kudaden shiga bayan an cire tallafin mai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262