Dubu Ta Cika: Yadda aka Kama Dan Bindiga Yana Cire Kudin Fansa a POS

Dubu Ta Cika: Yadda aka Kama Dan Bindiga Yana Cire Kudin Fansa a POS

  • Wani mai garkuwa da mutane da ya yi zaton ya ci bulus ya fada komar jami'an tsaro a wurin cire kudin fansa daga asusun bankinsa
  • Yan sandan jihar Kwara sun cafke wani da ake zargin yana cikin kungiyar masu garkuwa da mutane a lokacin da ya ke dab da karban kudin
  • An kama Muhamodu Sanni ne yayin da yake kokarin cire kudin fansa da aka biya bayan sace wasu mazauna Obudu da ke jihar Kwara hankali kwance

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kwara – Rundunar ’Yan Sandan Jihar Kwara ta ce ta cafke wani da ake zargin yana cikin kungiyar masu garkuwa da mutane.

An kama shi ne a yayin da yake kokarin cire kudin fansa da aka biya bayan sace wasu mazauna kauyen Obudu da ke Karamar Hukumar Ilorin ta Gabas.

Kara karanta wannan

Bidiyo: Sojoji sun yi gumurzu da 'yan ta'adda a daji, sun ceto mutane

Yan sanda sun kama mai garkuwa da mutane a Kwara
Sufeto Janar na yan sadan Najeriya Tunji Disu Hoto: Nigeria Police Force
Source: Twitter

Daiy Trust ta wallafa cewa rundunar ta ce an kama wanda ake zargin, mai suna Muhamodu Sanni, a wani wajen POS bayan gudanar da bincike bisa bayanan sirri kan harin da aka kai kauyen ranar 28 ga Yuli, 2026.

Yadda 'yan bindiga suka shiga Kwara

A ruwayar jaridar Punch, an ruwaito ’yan sandan sun ce mutane uku ne aka sace lokacin da wasu ’yan bindiga dauke da makamai suka kai farmaki kauyen.

Kakakin rundunar, SP Adetoun Ejire-Adeyemi, ta ce binciken ya mayar da hankali ba kawai kan wadanda suka yi garkuwar ba, har da hanyoyin da kungiyar ke amfani da su wajen sadarwa, tura kudade da karbar kudin fansa.

Yan sanda sun ci gaba da bincike a Kwara
Wasu daga cikin yan sandan Najeriya Hoto: Nigeria Police Force
Source: Facebook

Ta ce hakan ne ya kai ga cafke Sanni a lokacin da yake kokarin cire kudin da ake alakanta shi da lamarin sace mutanen.

An tona asiri a jihar Kwara

Rundunar ta ce bayan kama Sanni, ya taimaka wajen samun karin bayanai kan yadda kungiyar ke gudanar da ayyukanta na garkuwa da mutane.

Kara karanta wannan

Nasara daga Allah: Sojoji da yan sanda sun rutsa yan bindiga fiye da 200 ta sama da ƙasa

Ta ce:

"A lokacin bincikenmu, Sanni ya tona asirin sauran yan kungiyarsa da suka hada da Aminu and Uma."

’Yan sandan sun ce suna gudanar da binciken cikin sirri, yayin da suke tantance tare da tabbatar da bayanan da suka samu daga wanda ake zargin kafin daukar wasu matakan aiki.

Kwamishinan ’Yan Sandan Kwara, Ojo Adekimi, ya tabbatar wa mazauna jihar cewa rundunar za ta ci gaba da farautar kungiyoyin masu aikata laifuka da kuma wadanda ke taimaka masu.

'Yan bindiga sun yi barazana

A wani labarin, kun ji cewa 'yan uwan aƙalla mutane 176 da ’yan ta’adda suka sace a ƙaramar hukumar Kaiama ta jihar Kwara sun sake roƙon gwamnati ta gaggauta kuɓutar da su.

’Yan uwansu sun ce sun tara sama da Naira miliyan 155 domin biyan kuɗin fansa, amma ana zargin masu garkuwar sun ƙi karɓar kuɗin saboda bai kai yadda suka nema a biya su ba.

An ce ’yan ta’addan sun yi barazanar aurar da matan da suke ganin kyawawa ne tare da kashe sauran waɗanda suke riƙe da su, sannan su hallaka sauran da su ke ganin ba sa bukata.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng