Tinubu Ya Samu Saƙon Gayyata daga Kasar Waje, An Fadi Abin da Ake Nema daga Najeriya
- Firaministan kasar Indiya, Narendra Modi, ya gayyaci Shugaba Bola Ahmed Tinubu zuwa taron shugabannin BRICS na shekarar 2026
- Za a gudanar da taron ne a New Delhi da ke kasar ta Indiya daga ranar 12 zuwa 13 ga watan Satumba, 2026
- Jakadan Indiya a Najeriya ya ce halartar Najeriya na da muhimmanci saboda matsayinta a nahiyar Afirka da tattalin arzikin duniya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Firaministan Indiya, Narendra Modi, ya gayyaci Shugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, zuwa taron shugabannin kungiyar BRICS da za a gudanar a New Delhi.
Rahotanni sun nuna cewa sn shirya gudanar da taron ne daga ranar 12 zuwa 13 ga watan Satumba, 2026.

Source: Getty Images
The Nation ta ruwaito vewa Babban jakadan Indiya a Najeriya, Abhishek Singh, ne ya bayyana hakan a Abuja, inda ya ce Indiya na neman kara rawar da Najeriya ke takawa a harkokin tattalin arziki da siyasa na duniya, musamman BRICS.

Kara karanta wannan
Shugaba Tinubu ya maida hankali kan samar da ayyuka masu gwaɓi ga matasan Najeriya
Indiya na son Najeriya ta taka rawa
Singh ya ce halartar Najeriya na da matukar muhimmanci saboda kasancewarta daya daga cikin manyan kasashen Afirka ta fuskar tattalin arziki da kuma daga cikin kasashen da suka fi yawan jama'a a duniya.
Ya bayyana fatan cewa Shugaba Tinubu zai jagoranci tawaga mai karfi zuwa taron. Singh ya ce:
“An gayyaci dhugaban Najeriya, Bola Ahmed Tinubu, GCFR, zuwa taron BRICS da za a gudanar a New Delhi nan da ‘yan makonni, kuma muna matukar fatan Mai Girma Shugaban Kasa zai jagoranci wata babbar tawaga zuwa taron.”
Ya ce Najeriya a matsayinta na kasa abokiyar huldar BRICS na da muhimmiyar rawar da za ta taka saboda matsayinta na daya daga cikin manyan kasashen tattalin arziki a Afirka da kuma yawan jama'a.
BRICS za ta tattauna manyan batutuwa
Indiya ce ke jagorantar BRICS a shekarar 2026, inda ake sa ran taron zai mayar da hankali kan kalubalen duniya, hadin gwiwar tattalin arziki da kuma tuntubar kasashen abokan huldar kungiyar.
Singh ya ce Najeriya da Indiya na kuma goyon bayan burin juna a Majalisar Dinkin Duniya.

Source: Twitter
Ya bayyana cewa Najeriya ta nuna goyon bayanta ga yunkurin Indiya na samun kujerar mamba a Kwamitin Tsaro na Majalisar Dinkin Duniya, yayin da Indiya ita ma ta nuna goyon bayanta ga hakan
Indiyawa 60,000 na zaune Najeriya
Jakadan ya kuma bayyana irin gudunmawar al'ummar Indiya da ke zaune a Najeriya, inda ya kiyasta cewa kimanin Indiyawa 60,000 ne ke zaune a kasar.
Ya ce da dama daga cikinsu ‘ya’ya ne da jikokin mutanen Indiya da suka zauna a Najeriya tun da dadewa, kuma yanzu sun samu gindin zama a cikin al'ummar Najeriya.
Ya yaba wa gwamnatin Najeriya da jama'ar kasar kan samar wa al'ummar Indiya yanayin da suka samu damar bunkasa.
Ana so BRICS ta sa baki a rikicin Iran
A wani labarin, kun ji cewa shugaban Iran, Masoud Pezeshkian, ya yi wata tattaunawa da Firayim ministan India, Narendra Modi.
A wannan tattaunawa ta wayar tarho, shugaban Iran ya bukaci ƙungiyar kasashen BRICS ta taka rawar gani wajen dakatar da rikicin Gabas ta Tsakiya.
A nasa bangaren, Firaministan Indiha ya nuna damuwa kan yadda rikicin ke kara tsananta, yana mai jaddada bukatar a kare zaman lafiya da kwanciyar hankali a Gabas ta Tsakiya.
Asali: Legit.ng
