An Gudu ba a Tsira ba: Guguwa Ta Tunkaro NDC Awanni da Sauya Sheƙar Kwankwaso da Obi
- Daya daga cikin manyan jam'iyyar ADC, Dr. Umar Ardo ya ce zai ci gaba da shari’a kan sahihancin jam’iyyar adawa ta NDC
- Ya zargi NDC da rashin cika sharuddan rajista na INEC jim kadan bayan jagororin siyasa irinsu Peter Obi da Rabiu Musa Kwankwaso suka sauya sheka
- Dr. Umar Ardo ya ce ya taba kai ƙara kan shugabanni kamar su Goodluck Jonathan da Muhammadu Buhari a baya saboda haka ba zai fasa ba
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
FCT Abuja – Tsohon ɗan takarar gwamna a jihar Adamawa kuma jigo a jam’iyyar ADC, Dr. Umar Ardo, ya bayyana cewa zai ci gaba da fafutuka domin ganin ya samu nasara a shari’ar da yake yi da jam’iyyar NDC.
Jam’iyyar NDC ta fara jan hankalin jama’a ne bayan da tsofaffin ‘yan takarar shugaban ƙasa, Sanata Rabi’u Musa Kwankwaso da Peter Obi, suka fara nuna sha’awar komawa cikinta.

Source: Facebook
Jaridar Vanguard ta wallafa cewa a ranar Lahadi, 3 ga watan Afrilu, shekarar 2026, Kwankwaso da Obi suka sauya sheka a hukumance daga ADC zuwa NDC.
Sun bayyana cewa sun sauya shekar ne sakamakon rikicin shugabanci da ya dabaibaye tsofaffin jam’iyyunsu, wanda ya tilasta masu barin ADC domin neman mafita a NDC.
Ana zargin ADC da rashin rajista
A wata hira da ya yi da DCL Hausa ta wallafa a shafin Facebook, Dr. Umar Ardo ya ce yana shari’a da NDC ne saboda a cewarsa ba ta cika sharuddan da Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC) ta gindaya ba.
Ya bayyana cewa shi ba mutum ba ne da za a yaudara cikin sauƙi, yana mai cewa ya dade yana shiga kotu domin neman gaskiya.
Dr. Ardo ya ce:
“Sau 15 ina zuwa kotu, na kai Jonathan kotu, na kai Buhari kotu. Saboda haka ni ba a amfani da ni kawai; dole a yi gaskiya.”

Source: Facebook
Umar Ardo ya kara da cewa yana da yakinin cewa jam’iyyar NDC ba ta cika ka’idojin da kundin tsarin mulkin Najeriya ya shimfiɗa wajen rajistar jam’iyya ba.
Ardo ya kalubalanci sahihancin NDC
Dr. Umar Ardo ya kalubalanci sahihancin jam’iyyar NDC a matsayin cikakkiyar jam’iyya da aka yi wa rajista bisa dokokin INEC.
Ya bayyana cewa:
“Akwai wata jam’iyya da ta taba samun rajista ba tare da ta rubuta bukatar yin rajista ba? NDC ta je ta karɓi rajista ba tare da ta gabatar da buƙata a rubuce ba. Ba ta cika ka’idojin da INEC ta shimfiɗa ba, haka kuma ba ta bi tanadin kundin tsarin mulkin Najeriya ba. Wannan ne ya sa na kai ƙara a kanta.”
Ya bukaci a nuna masa wata jam’iyya a Najeriya da ta zama cikakkiyar jam’iyya ba tare da an yi mata rajista yadda doka ta tanada ba
Ana fatan samun alheri a sauya shekar Kwankwaso
A wani labarin, mun wallafa cewa daya daga cikin matasan ADC kuma tsohon hadimin gwamnan Kano, Salihu Tanko Yakasai ya ce kada a karaya da sauya shekar Rabi'u Musa Kwankwaso.
Sanata Kwankwaso da tsohon dan takarar shugaban kasa Peter Obi da sun jagoranci magoya bayansu zuwa jam'yyar NDC a ranar Lahadi 3 ga watan Mayu na shekarar 2026 a babban birnin tarayya.
A martaninsa, Salihu Tanko Yakasai ya bayyana cewa hakan zai iya jawo wani alheri mai gwabi da dukkanin yan adawa a Najeriya gababin zaben 2027 yayin da za a raba hankalin jam'iyya mau mulki.
Asali: Legit.ng


