NDC: Kwankwaso Ya Mika Sakon Kar Ta Kwana gabanin Rufe Rajistar Jam'iyyu a Najeriya
- Tsohon gwamnan Kano, Sanata Rabiu Kwankwaso ya bukaci magoya baya su gaggauta yin rajista da jam’iyyar NDC gabanin wa'adin hukumar INEC
- Ya yi kiran ne bayan shi da tsohon gwamnan Anambra, Peter Obi suka sanar da sauya sheka daga hadakar adawa ta ADC zuwa NDC karkashin Serieke Dickson
- Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya jaddada muhimmancin yin rajista kafin karshen wa'adin, musamman ga wadanda ke da niyyar kawo canji a Najeriya
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa, Sanata Rabiu Musa Kwankwaso, ya yi kira ga masoyansa da kuma magoya bayan tsohon gwamnan Anambra, Peter Obi, da su gaggauta yin rajista da jam’iyyar NDC.
Ya bayyana cewa akwai buƙatar a yi hakan domin sai wanda ya yi rajista ne kawai zai iya kiran kansa ɗan jam’iyya, kamar yadda dokar zaɓen Najeriya ta tanada.

Source: Facebook
A wani bidiyo da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Sanata Kwankwaso ya jaddada muhimmancin yin rajista da jam’iyyar NDC gabanin babban zaɓe mai zuwa.
Kiran Kwankwaso ga magoya baya kan NDC
A cikin bidiyon, Sanata Kwankwaso ya zaburar da jama'a da su tabbata sun yi rajista daga yanzu zuwa ranar 26 ga watan Mayu, 2026 domin a mika sunayensu cikin cikakkun yan jam'iyya.
A kalamansa:
“A nan na ke kira ga dukkanin al’umma, waɗanda suke masoya da magoya baya, da su yi rajista da wannan jam’iyya tamu ta NDC ba tare da ɓata lokaci ba.”
Ya ƙara da cewa:
“Kamar yadda aka sani, ranar 26 ga wata, idan Allah Ya kai mu, wannan jam’iyya da sauran jam’iyyu duka za su shigar da rajistocinsu. Wanda sunansa ke kan rajista shi ne zai iya shiga zaɓe na wannan jam’iyya, kamar yadda yake a cikin dokokin zaɓe a wannan ƙasa.”

Kara karanta wannan
Ganduje ya kara tsokano Kwankwaso, ya kwatanta shi da 'tsuntsu' a siyasar Najeriya
Kiran Kwankwaso ga sauran ‘yan Najeriya
Sanata Kwankwaso ya kuma bayyana buƙatar dukkanin masu kishin ƙasa da masu son ganin an samu canji a Najeriya su taru a ƙarƙashin jam’iyyar NDC.
Ya ce akwai muhimmanci jama’a su cika ka’idojin da ake buƙata domin samun damar shiga zaɓe mai zuwa da ba su damar gudanar da harkokin siyasa.
A cewarsa:
“Saboda haka ina kira ga al’umma baki ɗaya, musamman waɗanda suke son shiga zaɓe, su tabbatar sun cika dukkan sharuɗɗa kafin ranar 26 ga wannan wata.”
Ya ƙara da cewa yana son jawo hankalin ‘yan Najeriya, musamman masu sha’awar ci gaban ƙasa, da su rungumi wannan dama domin kawo sauyi mai ma’ana.

Source: Twitter
Kwankwaso ya bayyana cewa sauyin da ake nema ya haɗa da inganta zaman lafiya, bunƙasa ilimi, samar da ayyukan yi ga matasa, da kuma haɓaka walwalar jama’a.
Ya sake nanata kira ga talakawa da marasa ƙarfi da kada su yi wasa da wannan dama, yana mai cewa haɗin kai da shigar jama’a cikin tsarin siyasa ne zai tabbatar da samun ci gaba mai dorewa a Najeriya.
An cimma matsaya kan NDC a Kano
A baya kun samu labarin cewa NDC ta warware rikicin shugabanci a Kano, bayan wasu kalamai da shugaban jam'iyyar Hon. Husaini Isah Mai Riga ya fara jawo rikici a cikinta.
Hon Mai Riga ya fito kafafen yada labarai yana zargin Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya shigo NDC da mutanensa kuma za a tura su gefe bayan sun gama rainon jam'iyyar ta kawo yanzu.
Wannan al'amari ya sa uwar jam'iyyar ta kasa ta yi gaggawar kiran wani muhimmin taro, inda aka gaggauta shawo kan matsalar sannan Mai Riga ya ba da hakuri ga mutanen da ya sosa wa rai.
Asali: Legit.ng

