An Taso Atiku a Gaba kan Takara, Jigon ADC Ya Faɗa Masa kan Zaben 2027

An Taso Atiku a Gaba kan Takara, Jigon ADC Ya Faɗa Masa kan Zaben 2027

  • Ana ci gaba da ba tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar shawara game da niyyar neman takararsa a zaben 2027
  • Atiku na ci gaba da fuskantar kiraye-kiraye da ya janye daga takarar shugaban kasa a zaben da za a yi a farkon shekara mai zuwa
  • Wani tsohon ɗan takara a ADC ya ce bayan yunkurin Atiku tun daga 1992, lokaci ya yi da zai zama dattijon siyasa mai ba matasa damar jagoranci

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Abuja - Wani tsohon ɗan takarar karamar hukuma a ADC, Collins Osuagwu ya shawarci Atiku Abubakar kan takara a zaben 2027.

Jigon jam’iyyar ADC a Imo, ya bukaci Atiku Abubakar ya sake tunani kan takarar shugaban kasa a 2027 da ake tunkara.

An shawarci Atiku ya bar wa Obi takara a ADC
Jiga-jigan jam'iyyar ADC, Peter Obi da Atiku Abubakar. Hoto: Mr Peter Obi, Atiku Abubakar.
Source: Facebook

An shawarci Atiku Abubakar ya hakura da takara

Kara karanta wannan

Tsohon sufeta janar ya zargi APC da neman hana shi takarar gwamna

Osuagwu ya bayyana hakan ne cikin wata budaddiyar wasika inda ya ce Atiku ya kamata ya koma matsayin dattijon siyasa maimakon sake neman shugabanci, cewar Punch.

Ya ce kamata ya yi Atiku ya marawa matashi baya domin tabbatar da zaman lafiyar kasa da ci gaban dimokuradiyya.

Jigon jam'iyyar ADC ya yabawa irin gudunmawar da Atiku ya bayar lokacin da ya kasance mataimakin shugaban kasa daga 1999 zuwa 2007.

Ya ce duk da Atiku ya bayyana a fili cikin koshin lafiya da kuzari yana da shekaru 79, hakan ya kamata ya nuna lokacin sauya matsayi.

Osuagwu ya ce bayan yunkurin shugaban kasa tun daga 1992, siyasar yanzu na iya bambanta da baya.

Tsohon dan takarar ya ce janyewar Atiku daga neman takara zai nuna hikima da kokarin gina kyakkyawan tarihi a siyasarsa.

Ya kara da cewa hakan zai iya ba shi damar zama abin koyi da “uban dimokuradiyya” a Najeriya.

An ba Atiku shawara kan takara a zaben 2027
Tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar. Hoto: Atiku Abubakar.
Source: Facebook

2027: Ɗan ADC ya zaɓi Obi kan Atiku

Osuagwu ya kuma yi magana kan sauyin siyasar da ake gani kafin zaben 2027, yana mai jaddada muhimmancin tsarin karba-karba da bai wa matasa dama.

Kara karanta wannan

Kwamishinan Ganduje ya amsa kiran masoya Tinubu, zai nemi kujerar sanata a Kano

Ya bayyana Peter Obi a matsayin dan takara mai yawan magoya baya musamman a yankunan kudancin Najeriya.

Ya gargadi cewa idan dan takarar shugaban kasa daga Arewa ya hada kai da shugaban jam’iyya daga Arewa, hakan na iya haifar da rikicin siyasa irin wanda PDP ta taba fuskanta, ya ce sake faduwa a zabe na iya shafar tarihin Atiku a siyasa.

Osuagwu ya bukaci Atiku ya yi abin da zai amfani kasa gaba daya idan zai yanke hukuncin shiga takarar shugaban kasa.

Ya ce matakin da zai dauka zai yi tasiri sosai ga makomar dimokuradiyyar Najeriya da tarihinsa a siyasa.

Atiku ya yi gargadi kan shirin hana jihohi kamfe

Mun ba ku labarin cewa tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar ya yi gargadi game da fara maganar hana yakin neman zabe a wasu jihohin Arewa.

Ya bayyana cewa bai kamata a yi amfani da wani uzuri ba wajen tauye hakkin jama'a na shiga harkokin dimokuradiyya a 2027.

An fara maganar hana yakin neman zabe a wasu jihohin Najeriya ne saboda yadda ake kara samun hare-haren 'yan ta'adda a cikinsa.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.