Gobarar Titi: Jigon ADC Ya Hango Alherin Sauya Shekar Kwankwaso ga 'Yan Adawa
- Daya daga cikin matasan ADC kuma tsohon hadimin gwamnan Kano, Salihu Tanko Yakasai ya ce kada a karaya da sauya shekar Rabi'u Musa Kwankwaso
- Sanata Kwankwaso da tsohon dan takarar shugaban kasa Peter Obi da sun jagoranci magoya bayansu zuwa jam'yyar NDC a ranar Lahadin da ta gabata
- A martaninsa, Salihu Tanko Yakasai ya bayyana cewa hakan zai iya jawo wani alheri mai gwabi da dukkanin yan adawa a Najeriya gababin zaben 2027
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Jagora a tafiyar hamayya ta ADC a Kano, Salihu Tanko Yakasai ya bayyana cewa akwai wani sabon yanayi na siyasa na kunno kai a Najeriya.
Ya ce an samu wannan sauyi ne bayan sauya sheƙar manyan ‘yan siyasa da suka hada Peter Obi da Rabiu Musa Kwankwaso zuwa jam’iyyar NDC.

Source: Facebook
A cikin sanarwar da ya wallafa a shafinsa na X, Salihu Tanko Yakasa da aka fi sani da Dawisu ya bayyana cewa wannan rarrabuwar na iya zama wata dama da ba a zata ba ga ɓangaren adawa.
ADC: An hango alheri a sauya shekar Kwankwaso
A cikin sakon, Dawisu ya bayyana cewa idan yan adawa suka cure a ADC, Shugaban kasa Bola Tinubu zai iya yin amfani da damar da ke hannunsu wajen hana su tsayar da 'dan takara.
Sai dai yanzu da aka samu rabuwar kai tsakanin ADC da NDC, lissafin siyasar ya sauya, wanda zai ba yan adawa damar tunkarar zaben 2027.
A cewarsa idan har aka ci gaba da matsa wa ADC kaɗai, hakan na iya barin NDC a matsayin babbar jam’iyyar adawa ɗaya tilo, musamman ganin goyon bayan da take samu daga Obi da Kwankwaso.
Ya bayyana cewa wannan na iya jefa gwamnati cikin ƙalubalen siyasa mai tsanani yayin da ake shirin gudanar da babban zabe mai zuwa.
Takure NDC, ADC zai jawo magana
A gefe guda kuma, Salihu Tanko Yakasai ya ce idan aka ɗauki matakin makure ADC da NDC, hakan na iya jawo ce-ce-ku-ce a cikin gida da kuma a idon ƙasashen waje, musamman dangane da sahihancin dimokuraɗiyyar Najeriya.

Source: Facebook
Sai dai ya bayyana fargabar cewa akwai yiwuwar duka jam’iyyun ADC da NDC su shiga zaɓe, wanda hakan zai haifar da rarrabuwar ƙuri’u a tsakanin ‘yan adawa a zaɓen 2027.
Dawisu ya ce idan hakan ta tabbata, ana iya sake ganin irin tsarin zaɓen shugaban ƙasa na 2023, wanda rarrabuwar ƙuri’un adawa ta bai wa jam’iyya mai mulki dama.
Sai dai duk da haka, ana sa ran jam’iyyun ADC da NDC za su iya samun gagarumin nasara a zaɓen ‘yan majalisar dokoki, musamman a yankunan Arewa da Gabasshin Najeriya.
Duk da wannan yanayi, ya jaddada biyayyarsa ga jam’iyyar ADC, tare da kira ga bangarorin biyu su rage zafin rikici su mayar da hankali kan yan adawa.
Kwankwaso, Obi sun sauya sheka
A baya, mun wallafa cewa manyan ƴan adawa, Peter Obi da Rabiu Musa Kwankwaso, sun bayyana komawarsu jam’iyyar NDC a hukumance, bayan fice wa daga hadakar yan adawa ta ADC.
Sun yi kira ga 'yan jam’iyyar da su guji yawan shari’o’in kotu, su mayar da hankali kan ci gaban ƙasa da kuma haɗin kan al’ummar Najeriya yayin da ake kokarin fafata wa da APC a babban zabe mai zuwa.
A bikin shigarsu jam'iyyar NDC a babban birnin tarayya Abuja, Peter Obi da Rabiu Kwankwaso sun aika muhimmin sako ga magoya bayansu yayin ake tunkarar babban shirin fara neman zaben 2027.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng


