Fadar Shugaban Kasa na Neman Hada Obi Fada da Ƙabilarsa, Ta Fadi yadda Zai Cutar da Su
- Fadar Shugasa ta yi magana game da alƙawarin da Peter Obi ya yi na yin wa'adi daya kacal idan ya ci mulki
- Ta ce burin shugaban ƙasa ga kabikar Igbo ya fi karfin mutum ɗaya, yana bukatar haɗin kai, shiri mai kyau da amincewar manyan yankunan ƙasa
- Fadar Shugasa ta yi zargin tikitin Obi da Kwankwaso ba zai samu isasshen goyon baya ba, tana mai shawartar a gina yarjejeniya mai ɗorewa kafin takara
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Fadar Shugasa ta sake mayar da martani kan alkawarin da ɗan takarar shugaban kasa a NDC, Peter Obi ya yi na wa'adin mulki daya.
Fadar ta ce wannan mataki da ya dauka zai kawo wa ƴan kabilar Igbo matsala a burinsu na shugabantar Najeriya.

Source: Twitter
Alkawarin da Obi ya yi kan wa'adin mulki
A cikin shirin Politics Today, tsohon gwamnan Anambra ya bayyana cewa a shirye yake ya yi wa'adin mulki na shekara huɗu kacal.
Rahotanni sun nuna cewa tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na NNPP, Rabiu Kwankwaso, wanda ake hasashen zai zama mataimakin Obi, ana kallonsa a matsayin wanda zai gaje shi a 2031 idan NDC ta lashe zaɓen 2027.
Martanin Fadar shugaban kasa ga Peter Obi
Da yake mayar da martani, Babban Mataimaki na Musamman ga Shugaban Ƙasa kan Yaɗa Labarai a Ofishin Mataimakin Shugaban Ƙasa, Stanley Nkwocha, ya ce wannan shiri na mutum ɗaya ne.
Ya ce amincewar Obi da wa'adin mulki guda ɗaya za ta tauye dogon burin al'ummar Ndigbo na ganin ɗaya daga cikinsu ya shugabanci Najeriya, cewar Tribune.
Nkwocha ya ce tun bayan dawowar mulkin dimokuraɗiyya a 1979, fitattun 'yan siyasar Ndigbo da dama sun yi ƙoƙarin zama shugaban ƙasa amma ba su yi nasara ba.
Ya ƙara da cewa burin samun shugaban ƙasa daga Kudu maso Gabas ya fi Peter Obi girma, domin batu ne da ke buƙatar haƙuri, haɗin kai da amincewar sauran yankunan ƙasar.

Kara karanta wannan
Peter Obi ya tsage gaskiya ya bayyana alkawarin da ba zai daukarwa 'yan Najeriya ba

Source: UGC
An kalubalanci Obi kan alkawarin wa'adin mulki
A cewarsa, ya kamata a tambayi ko Peter Obi ya tuntubi shugabannin siyasa, na gargajiya, 'yan kasuwa da masana daga yankinsa kafin ya amince da wa'adin shekara huɗu.
Nkwocha ya kuma ce bayan wa'adin shekaru takwas na Muhammadu Buhari daga Arewa, mulki ya koma Kudu a 2023 ƙarƙashin Bola Tinubu, kuma mutane da dama na ganin Kudu ya kamata ya kammala shekaru takwas.
Ya yi zargin cewa tikitin Obi da Kwankwaso ba zai samu isasshen goyon baya daga Kudu maso Yamma da Arewa ba, saboda ba shi da cikakkiyar karɓuwa a faɗin ƙasa.
A cewarsa, nasarar zaɓen shugaban ƙasa tana buƙatar ƙawance, tsari, yawan ƙuri'u da amincewa daga yankuna daban-daban, ba kawai farin jini a kafafen sada zumunta ba.
An yi wa Obi rubdugu da ya taba Tinubu
Kun ji cewa Fadar Shugaban Ƙasa da Sanata Adams Oshiomhole sun soki Peter Obi bayan hirarsa ta talabijin inda ya yi suka ga shugaba Bola Tinubu.

Kara karanta wannan
Fadar shugaban kasa ta hango kura kurai a kalaman Obi, ta yi masa zazzafan martani
Mai ba shugaban ƙasa shawara, Bayo Onanuga, ya ce Obi ya sha sauya jam'iyyu, yana mai cewa tafiyarsa ta siyasa ba ta yi kama da ta Tinubu ba.
Oshiomhole kuma ya zargi Obi da rashin fahimtar tattalin arzikin Najeriya, yana mai kare manufofin tattalin arzikin gwamnatin Tinubu.
Asali: Legit.ng
