Matakin da Gwamnatin Oyo Ta Dauka bayan an Ceto Dalibai 44

Matakin da Gwamnatin Oyo Ta Dauka bayan an Ceto Dalibai 44

  • Gwamnatin jihar Oyo ta fara daukan wasu muhimman matakai bayan yan bindiga sun shiga jihar, sun kora dalibai dazuka har na tsawon makonni
  • Gwamnan Oyo, Seyi Makinde, ya bayyana takaici da mamakin yadda aka samu gibi a bangaren tsaron jihar da aka samu kafar garkuwa da daliban
  • Daga cikin matakan da ya dauka akwai kafa wani muhimmin kwamiti da zai yi aikin samar da bayanai game da gibin da aka samu wajen sace daliban

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Oyo – Gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, ya kafa kwamitin bincike na shari'a domin binciken sace dalibai da malamai da aka yi a al'ummomin Esiele da Yawota da ke karamar hukumar Oriire.

An sanar da hakan ne a cikin wata sanarwa da Kwamishinan Yada Labarai da Wayar da Kan Jama'a na jihar, Dotun Oyelade, ya fitar a ranar Alhamis, 30 ga watan Yuli, 2026.

Kara karanta wannan

Sojoji sun gwabza da yan bindiga karkashin Aleiro, an kashe rayuka a Zamfara

Gwamnatin Oyo ta waiwayi matsalar tsaro
Gwamna Seyi Makinde na jihar Oyo Hoto: Seyi Makinde
Source: Instagram

The Cable ta kawo labarin cewa lamarin ya faru ne a ranar 15 ga watan Mayu, 2026 lokacin da wasu 'yan bindiga suka kai hare-hare wasu makarantu a jihar.

Matakan da aka dauka bayan harin Oyo

Jaridar Punch ta kawo labarin cewa bayan harin, gwamnatin jihar ta rufe makarantu a kananan hukumomi hudu yayin da jami'an tsaro suka fara kokarin ceto wadanda aka sace.

Sanarwar Oyelade ta ce za a kaddamar da kwamitin a ranar Juma'a,31 Yuli, 2026 inda zai binciki yadda aka kai ga sace daliban har cikin makarantunsu.

Haka kuma kwamitin zai tantance yadda hukumomin da abin ya shafa suka mayar da martani, tare da gano musabbabin gibin tsaro da ya jawo harin.

Haka kuma, kwamitin zai gabatar da shawarwari kan hanyoyin inganta tsaro da kare makarantu da al'ummomi a fadin jihar Oyo, domin kauce wa sake aukuwar irin wannan lamari nan gaba.

Gwamnatin Makinde ta lallashi yan Oyo

Kara karanta wannan

An yi wa dan APC mai tallata Tinubu jina jina, za a farauci wadanda suka daka shi

Oyelade ya ce kafa kwamitin ya yi daidai da kudurin gwamnatin Makinde na tabbatar da cikakken bincike mai zaman kansa kan wannan mummunan lamari.

A ranar 10 ga watan Yuli, Fadar Shugaban Kasa ta sanar da cewa an kubutar da dukkan daliban da malaman da aka sace.

Kwamiitingwamantin Oyo zai zakulo matsaloli a bangaren tsaro
Taswirar jihar Oyo inda aka sace dalibai Hoto: Legit.ng
Source: Original

Sai dai Makinde ya bukaci Majalisar Ɗinkin Duniya da kungiyoyin kare hakkin bil'adama na kasa da kasa su gudanar da bincike mai zaman kansa kan lamarin.

Gwamnan ya ce yanayin yadda satar ta faru yana da matukar muni kuma ba irin abin da aka saba gani ba, saboda haka ya dace a gudanar da bincike mai zaman kansa fiye da na hukumomin cikin gida.

Gwamnan Oyo ya mika mulki ga mataimakinsa

A baya, mun kawo labarin cewa majalisar dokokin jihar Oyo ta amince da hutun shekara da Gwamna Seyi Makinde zai fara daga 10 ga Agusta, 2026 lamarin da ya sa aka dauki matakin cike gibin da zai bari.

Mataimakin gwamna Bayo Lawal ne zai jagoranci harkokin gwamnatin jihar har zuwa lokacin da Makinde zai dawo daga hutun, kuma yan majalisar sun bayyana kwarin gwiwar cewa ayyukan gwamnati za su ci gaba ba tare da tsaiko ba.

Da yake jawabi bayan amincewar majalisar, Mataimakin Kakakin Majalisar, Muhammed Fadeyi, ya yi wa Gwamna Makinde fatan samun hutun lafiya, natsuwa da kuma dawowa bakin aiki cikin koshin lafiya.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng