An Maka Shugabannin APC 35 a Kotu kan 'Ɓata' Sunan Gwamna da Kwamishinarsa

An Maka Shugabannin APC 35 a Kotu kan 'Ɓata' Sunan Gwamna da Kwamishinarsa

  • Shugabannin APC har mutum 35 sun jawo wa kansu matsala bayan maka su a kotu da aka yi a Ondo wanda ya jawo maganganu
  • Lauyan masu ƙara ya ce an kai su kara ne saboda kiran wata kwamishina da sunan da bai dace ba duk da cewa suna gwamnati daya
  • Kotu ta ɗage shari'ar zuwa 8 ga Oktoba, 2026, yayin da waɗanda ake ƙara suka nuna suna son sasanci tare da ƙalubalantar hurumin kotun

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.

Akure, Ondo - Kwamishinar Kudi ta Ondo, Omowunmi Isaac ta kai karar shugabannin APC 35 a kotu saboda wasu kalamai da suka yi marasa dadi gare ta.

Isaac tare da ɗan'uwanta Kunle Odide, sun shigar da ƙarar batanci a babbar kotun Ondo da ke Akure kan shugabannin APC mai mulki a jihar.

Kara karanta wannan

Fadar shugaban kasa na neman hada Obi fada da ƙabilarsa, ta fadi yadda zai cutar da su

Kwamishina ta maka shugabannin APC 35 a kotu
Gwamna Lucky Aiyedatiwa na jihar Ondo. Hoto: Hon. Lucky Aiyedatiwa.
Source: Facebook

Umarnin alkalin kotu kan shari'ar da ake yi

A zaman kotun na ranar Talata, Mai Shari'a Yemi Fasanmi ya umarci kowane mai ƙara ya biya Naira 100,000 ga kowane daga cikin waɗanda ake ƙara, cewar Punch.

An yanke wannan hukunci ne bayan an gabatar da buƙatar gyara wasu kura-kurai da ke cikin takardun farko da aka shigar kotu game da shari'ar.

Lauyoyin waɗanda ake ƙara sun kuma bayyana cewa za su shigar da ƙorafi na farko domin ƙalubalantar hurumin kotun da kuma ingancin shari'ar gaba ɗaya.

Mai Shari'a ya ɗage sauraron ƙarar zuwa ranar 8 ga Oktoba, 2026, domin ci gaba da sauraron shari'ar da kuma duba sauran buƙatun ɓangarorin biyu.

Shugabannin APC sun fusata kwamishina a Ondo
Gwamna Lucky Aiyedatiwa na jihar Ondo yayin taro a Akure. Hoto: Hon. Lucky Aiyedatiwa.
Source: Twitter

Musabbabin rikicin tsakanin kwamishina da shugabannin APC

Tsohon Antoni Janar na Ondo, Adekola Olawoye, ya ce rikicin ya samo asali ne daga wasiƙar da ya aika wa shugaban APC na ƙasa a matsayinsa na ɗan jam'iyya.

Olawoye ya ce wasiƙar ta kasance ta sirri ce, ba a rubuta ta domin jama'a ba, kuma sun shirya yin sasanci a wajen kotu idan hakan zai yiwu, kamar yadda Vanguard ta ce.

Kara karanta wannan

'Yan ta'adda sun shiga Kaduna da dare, sun kashe rayuka 30 sun kona gidaje

Lauyan masu ƙara, Olaoluwa Imoru, ya ce wata wallafa da Nigerian Tribune ta buga ta kira kwamishinar "mama" a wurin Gwamna Lucky Aiyedatiwa, abin da suka ce ya bata mata suna tare da nuna tana da tasiri fiye da kima.

Ya ce suna neman kotu ta ayyana wallafar a matsayin batanci, ta ba su diyya, sannan ta umarci a janye wallafar tare da neman afuwa a fili.

Oluremi Tinubu ta magantu kan yunwa a ƙasa

A wani labarin, an ji cewa uwargidan Shugaban Ƙasa, Oluremi Tinubu, ta ce gwamnatin tarayya za ta ƙara ƙaimi wajen yaƙi da yunwa da ƙarancin abinci mai gina jiki .

Ta bayyana cewa shirin rarraba kayan abinci da bankunan abinci na al'umma na tallafa wa masu buƙata, nakasassu da yara.

Gwamna Lucky Aiyedatiwa na jihar Ondo ya yaba da shirin, yana mai cewa Ondo ta amince da takarar Bola Tinubu a zaɓen 2027 da ake tunkara.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 5 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.