An Gano Jihohi 19 ne za Su Yi Tasiri a Zaben 2027 ba Yawan Gwamnoni ba

An Gano Jihohi 19 ne za Su Yi Tasiri a Zaben 2027 ba Yawan Gwamnoni ba

  • Bayanan kididdiga sun nuna jihohi 19 ne a Najeriya, ba tasirin gwamnoni ba, ke nuna yadda sakamakon zaɓen shugaban ƙasa zai iya kasancewa
  • An fitar da hasashen ne yayin da 'yan siyasan kasar da jam'iyyu ke cigaba da shirye-shirye domin tunkarar babban zaben 2027 da ke tafe
  • Wani kamfani da ya saba bincike game da yadda jama'a ke kada kuri'a a jihohin Najeriya ne ya fitar da rahoton bayan wani dogon nazari da ya yi

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

FCT, Abuja - An bayyana cewa jihohi 19 ne za su fi tasiri wajen samar da sakamakon zaɓen shugaban ƙasa na 2027 a Najeriya, a cewar wani sabon rahoto da aka yi bisa bayanan kididdiga wanda ya nazarci tsarin zaɓe na shekaru 20.

Kara karanta wannan

INEC ta shirya yin zabe a Kano da wasu jihohi 5 a watan Yuni

Hakan na zuwa ne a lokacin da hankulan 'yan Najeriya da dama ya karkata kan yadda zaben 2027 zai gudana da sakamakon da za a samu.

Wani mutum na kada kuri'a a Abuja
Yadda aka kada kuri'a a zaben kananan hukumomi a Abuja. Hoto: INEC Nigeria
Source: Facebook

Kamfanin VIISAUS mai gudanar da bincike da ya yi nazari kan sakamakon zaɓen shugaban ƙasa daga 2003 zuwa 2023 ne ya fitar da rahoton.

Rahoto kan zaben Najeriya

Binciken ya raba dukkan jihohi 36 zuwa rukuni uku bisa yadda suke jefa kuri’a daidai da jam’iyyar gwamnoninsu da kuma 'yan adawa.

A yanzu, jam’iyyar APC mai mulki na rike da jihohi 31 cikin 36 na Najeriya, wani babban rinjaye da ake ganin yana ƙara karfafa damar Shugaba Bola Tinubu na sake lashe zaɓe a 2027.

Duk da cewa ana ganin gwamnoni a matsayin muhimman masu tasiri, rahoton ya nuna suna taimakawa ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyarsu ne kawai da kashi 57.8.

Jihohin da suka zabi gwamnoninsu

Jihohin da aka lissafa a kasa sun goyi bayan jam’iyyar gwamnoninsu a kalla sau hudu cikin zaɓuka biyar na shugaban kasa da aka yi.

  • Kudu maso Kudu: Akwa Ibom, Bayelsa, Cross River, Delta
  • Kudu maso Gabas: Abia, Ebonyi, Enugu
  • Kudu maso Yamma: Ogun, Osun
  • Arewa maso Gabas: Taraba
  • Arewa maso Yamma: Zamfara

Kara karanta wannan

2027: Shettima ya yi gargadi kan rusa APC bayan zaben fitar da gwani

Rahoton Business Day ya nuna cewa Akwa Ibom, Bayelsa da Taraba sun yi fice, inda suka zabi jam'iyyar gwamnoninsu a duk zaɓuka biyar da suka gabata.

Jihohi 19 da za a fafata a 2027

Mafi girma kuma mafi muhimmanci a rukunin shi ne jihohin da ke sauya wanda za su zaba a duk lokacin zabe tsakanin goyon baya da rashin goyon bayan jam'iyyar gwamnoninsu.

  • Arewa ta Tsakiya: Benue, Kogi, Kwara, Nasarawa, Niger, Plateau
  • Kudu maso Yamma: Ekiti, Lagos, Oyo
  • Kudu maso Kudu: Rivers
  • Kudu maso Gabas: Imo
  • Arewa maso Gabas: Adamawa, Borno, Yobe
  • Arewa maso Yamma: Jigawa, Kaduna, Kano, Kebbi, Sokoto

A cewar rahoton, ana tabbatar da wanda zai ci zaben shugaban kasa ne a wadannan jihohi saboda yanayinsu na kada kuri'a, saukin sauyawa bisa halayen ‘yan takara, yanayin ƙasa da kuma al’amuran yankuna.

Wani mutun na kada kuri'a a wajen zabe
Yadda aka kada kuri'a yayin wani zabe a Abuja. Hoto: INEC Nigeria
Source: Facebook

INEC za ta yi zabe a watan Yuni

A wani labarin, kun ji cewa hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa ta bayyana cewa ta shirya zaben cike gurbi a wasu jihohin Najeriya a watan Yunin 2026.

Kara karanta wannan

An fitar da hotunan bindigogi da wukaken da aka so kashe Trump da su

Rahotanni sun bayyana cewa shugaban INEC, Farfesa Joash Amupitan ya ce za a yi zaben cike gurbi a Kano, Kebbi, Enugu da sauransu.

Farfesa Joash Amupitan ya kara da cewa hukumar INEC na cigaba da shirye-shiryen gudanar da zaben shugaban kasa a shekarar 2027.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng