Gwamnonin Arewa 7 Sun Cimma Matsaya kan Tattaunawa da 'Yan Bindiga
- Gwamnan jihar Sokoto, Ahmad Sokoto, ya yi tsokaci kan batun tattaunawa da 'yan bindigan da suka addabi jama'a
- Ahmad Aliyu ya bayyana cewa gwamnonin jihohin Arewa maso Yamma sun cimma matsaya guda kan tattaunawa da 'yan bindiga
- Gwamnan ya jaddada cewa abin da kawai za su yarda da shi wajen 'yan bindiga shi ne su ajiye makamansu ba tare da wani sharadi ba
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Katsina - Gwamnan jihar Sokoto, Ahmad Aliyu, ya bayyana cewa gwamnonin shiyyar Arewa maso Yamma ba za su tattauna da ’yan bindiga ba.
Gwamna Ahmad Aliyu ya jaddada cewa mika wuya ba tare da sharadi ba ne kawai abin da za a amince da shi daga wajen kungiyoyin 'yan bindiga da ke gudanar da ayyukansu a yankin.

Source: Facebook
Jaridar The Punch ta ce Gwamna Ahmad Aliyu ya yi wannan furucin ne a birnin Katsina ranar Asabar, 2 ga watan Mayun 2206 yayin ƙaddamar da titin Yandaki–Shinkafi–Kofar Sauri mai tsawon kilomita 8.1, wanda Gwamna Dikko Umaru Radda ya gina a kan kuɗi Naira biliyan 12.6.
Ba za a tattauna da 'yan bindiga ba
“Ba za mu tattauna da kowane mai laifi ba, kuma ba za mu karɓi kowane tayi daga gare su ba sai dai idan sun miƙa wuya ba tare da wani sharaɗi ba."
- Gwamna Ahmad Aliyu
Ya bayyana cewa gwamnonin Arewa maso Yamma suna haɗe a kan ƙudurin ganin an kawo ƙarshen rashin tsaro, inda ya ƙara da cewa gwamnatocin jihohi suna kashe dukiya mai yawa domin yaƙar 'yan bindiga da sauran laifuffuka masu alaƙa da hakan.
Gwamna Ahmad Aliyu ya ba da tabbaci
Gwamna Ahmad Aliyu ya tabbatar wa mazauna yankin cewa gwamnatocin jihohi suna aiki kafa-da-kafa da jami’an tsaro domin ƙarfafa dabarun da nufin maido da zaman lafiya a faɗin shiyyar.
Haka kuma ya yi kira ga jama'a da su goyi bayan yaƙin da ake yi da ’yan bindiga ta hanyar tona asirin masu ba su bayanan sirri a cikin kauyukansu, jaridar Vanguard ta kawo rahoton.

Kara karanta wannan
Zambar N1.5bn: Gwamnatin Kano za ta hukunta jami'an da suka tsakure albashin ma'aikata
“Dole ne mu yi abin da ya kamata a matakin al’umma ta hanyar kasancewa cikin shiri da sa ido kan zirga-zirgar mutanen da ba a amince da su ba."
- Gwamna Ahmad Aliyu
Akwai masu taimakon 'yan bindiga
Gwamnan ya lura cewa nasarar hare-haren da ’yan bindiga ke kaiwa sau da yawa tana samun goyon baya ne daga wasu mutanen gari, don haka ya buƙaci mazauna yankin da su ɗauki alhakin kare al’ummominsu.

Source: Facebook
Ya kuma yi kira ga jama’a da su ci gaba da addu’ar neman nasara kan ƙoƙarin da ake yi na magance rashin tsaro a Arewa maso Yamma da ma ƙasa baki ɗaya.
Gwamna Ahmad Aliyu ya yaba wa gwamnan jihar Katsina, Dikko Radda, saboda kasancewa sahun gaba wajen kafa rundunar tsaron jihar (C-Watch) domin tallafa wa jami’an tsaro.
'Yan bindiga sun farmaki sansanin 'yan sanda
A wani labarin kuma, kun ji cewa wasu 'yan bindiga dauke da makamai sun farmaki sansanin 'yan sanda a jihar Kwara.
'Yan bindiga sun hallaka jami'an 'yan sanda uku tare da raunata wasu guda biyu a harin da suka kai a yankin Tenebo cikin karamar hukumar Kaiama.
Majiyoyi sun ce maharan sun afka wa sansanin ne da dambin yawa, inda wasu daga cikinsu suke kan babura yayin harin da suka kawo.
Asali: Legit.ng
