Netanyahu Ya Fadi Matakin da Sojojin Isra'ila za Su Dauka idan aka Cafke Shi

Netanyahu Ya Fadi Matakin da Sojojin Isra'ila za Su Dauka idan aka Cafke Shi

  • Firaministan Isra'ila Benjamin Netanyahu ya ce dakarun musamman na ƙasarsa za su kuɓutar da shi idan aka kama shi a wata ƙasar Turai
  • Netanyahu ya bayyana haka ne yayin wata, yana mai magana kan sammacin kama shi da Kotun Hukunta Manyan Laifuffuka ta Duniya (ICC) ta fitar
  • Kalaman nasa sun zo ne yayin da ake ci gaba da ce-ce-ku-ce kan yiwuwar kama shi idan ya shiga ƙasashen da ke cikin mambobin ICC

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Tel Aviv, Isra'ila – Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu, ya ce dakarun musamman na ƙasarsa za su shiga tsakani domin ceto shi idan aka kama shi a wata ƙasa.

Netanyahu ya bayyana hakan ne yayin wata hira, inda ya yi ishara da tsohuwar hidimarsa a rundunar soji tare da cewa za a iya ba wa tsohuwar rundunarsa sabon aiki na kuɓutar da shi idan aka tsare shi a ƙasar waje.

Kara karanta wannan

An goyi bayan harbe 'yan ta'adda da zarar an gan su ba tare da jiran izini ba

Benjamin Netanyahu a kasar Isra'ila
Firaministan Isra'ila, Benjamin Netanyahu. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Middle East Monitor ta rahoto cewa kalaman sun zo ne a daidai lokacin da ake ci gaba da tattaunawa kan sammacin kama shi da Kotun Hukunta Manyan Laifuffuka ta Duniya (ICC) ta fitar.

Abin da Netanyahu ya ce

Da yake tuna lokacin da ya yi aiki a rundunar sojin Isra'ila, Netanyahu ya bayyana cewa akwai matakin da za su dauka idan aka kama shi:

"Na yi aiki a wannan runduna na tsawon shekara biyar, kuma za mu iya ba su sabon aiki."

Ya yi nuni da cewa za a iya tura rundunar domin ceto shi idan wata ƙasar Turai ta kama shi bisa sammacin ICC.

Sai dai bai bayyana yadda irin wannan aiki zai gudana ba, duk da cewa masana sun ce duk wata shiga ƙasar wani ba tare da amincewarsa ba na iya jawo babban rikicin diflomasiyya da kuma karya dokokin ƙasa da ƙasa.

Dalilin neman kama Netanyahu

Kara karanta wannan

Farashin mai ya sauka sosai bayan dakatar da yakin Amurka da Iran

Kotun Hukunta Manyan Laifuffuka ta Duniya (ICC) ta fitar da sammacin kama Netanyahu ne bisa zargin aikata laifin yaƙi da kuma cin zarafin bil'adama a yakin da Isra'ila ke yi a Zirin Gaza.

Rahoton Independent ya nuna cewa sammacin ya sanya Netanyahu cikin jerin mutanen da ake nema a duniya, kuma ƙasashe 124 da ke mambobin ICC na iya kama shi idan ya shiga yankunansu.

Donald Trump da Benjamin Netanyahu
Benjamin Netanyahu da Donald Trump a White House. Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Haka kuma, magajin garin birnin New York, Zohran Mamdani, ya bukaci gwamnatin tarayyar Amurka ta aiwatar da sammacin da ICC ta fitar kan Netanyahu, duk da cewa Amurka ba mamba ba ce a kotun.

Shirin kwance damarar Hamas

A wani labarin, mun ruwaito cewa shugaban Amurka Donald Trump ya sanar da cewa an cimma yarjejeniya kan kwance damarar kungiyar Hamas da sauran kungiyoyin masu dauke da makamai a Zirin Gaza.

Wani babban jami'in Hamas ya tabbatar da cewa kungiyar ta amince da shirin kwance damarar gaba daya, tare da cewa za ta fitar da sanarwa a hukumance nan gaba.

Shirin na cikin mataki na biyu na yarjejeniyar tsagaita wuta da Amurka ta shiga tsakani, wanda ya kunshi kwance damarar Hamas, janyewar sojojin Isra'ila da kuma sake gina Gaza.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng