"Za Mu Yi Cikakkiyar Biyayya": NDC Ta Mika Sakonni ga Kwankwaso bayan Sauya Sheka

"Za Mu Yi Cikakkiyar Biyayya": NDC Ta Mika Sakonni ga Kwankwaso bayan Sauya Sheka

  • Jam’iyyar NDC a Kano ta aika sakonni ga jiga-jigan siyasa a Najeriya, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso da Peter Obi
  • Haka kuma ta aika sako na daban ga Kwankwaso wanda ta bayyana da uba a siyasar Najeriya, kuma musamman Kano
  • Shugaban jam'iyyar reshen jihar Kano, Hon Husaini Isah Mai Riga ya kuma yi magana game da rabon madafun iko a NDC

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Shugaban jam’iyyar NDC na jihar Kano, Hon. Husaini Isah Mai Riga, a madadin jam’iyyar, ya bayyana farin cikinsa tare da yin maraba ga wasu fitattun siyasar Najeriya da suka sauya sheka.

Jam’iyyar ta yi maraba ga Injiniya Rabiu Musa Kwankwaso, tsohon gwamnan jihar Kano, tsohon sanata, kuma tsohon ministan tsaro, inda ta yabawa irin gagarumar gudunmawarsa ga ƙasa.

Kara karanta wannan

"Umarnin jagora": Jigo a Kwankwasiyya ya fice daga jam'iyyar ADC a jihar Kano

NDC ta yi wa Kwankwaso da Obi maraba
Jagoran NDC na kasa Serieke Dickson, Peter Obi, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso da manyan ADC a Abuja Hoto: Saifullahi Hassan
Source: Facebook

A sakon maraba da jam'iyyar ta wallafa a shafinta na Facebook, jam’iyyar ta yi maraba ga ɗan takarar shugaban ƙasa na jam’iyyar LP a zaɓen 2023 kuma tsohon gwamnan jihar Anambra, Peter Obi.

NDC ta yi maraba da Kwankwaso

A cikin wani saƙon murya da aka wallafa a shafin Facebook na jam’iyyar, Hon Mai Riga ya bayyana cikakken goyon baya da biyayya ga tsohon gwamnan Kano, yana mai bayyana shi a matsayin uba a siyasa a jihar.

Ya ce:

“Mun yi alƙawarin za mu kasance masu cikakkiyar biyayya ga Rabiu Musa Kwankwaso, uban siyasa a Kano."

Dangane da yadda za a tafiyar da mukamai da sauran al’amuran cikin gida na jam’iyyar, shugaban ya jaddada cewa ba za a riƙa bayyana su a bainar jama’a ba.

A cewarsa:

“Wannan lamari yana tsakaninmu da shi ne kawai. Jam’iyyar NDC ba ta bayyana harkokinta na cikin gida ba.”

Kara karanta wannan

Zambar N1.5bn: Gwamnatin Kano za ta hukunta jami'an da suka tsakure albashin ma'aikata

NDC za ta haɗa kai da su Kwankwaso

Ya bayyana shugabanni biyu a matsayin mutane nagari masu ƙwazo, waɗanda suka taka muhimmiyar rawa wajen ci gaban ƙasa.

NDC za ta yi wa Kwankwaso biyayya
Manyan ADC a yayin tarbar Peter Obi da Rabi'u Musa Kwankwaso a Abuja Hoto: Nigeria Democratic Congress NDC Kano Chapter
Source: Facebook

Hon. Husaini Isah Mai Riga ya nuna matuƙar godiya ga jagoran jam’iyyar na ƙasa, Sanata Seriake Henry Dickson; da shugaban jam’iyyar na ƙasa, Sanata Moses Cleopas Zuwoghe. Ya kuma gode wa mataimakin shugaban jam’iyyar na yankin Arewa maso Yamma, Alhaji Muhammad Sabo Bakin Zuwo; da kuma dukkannin ‘ya’yan jam’iyya da masu ruwa da tsaki da suka yi aiki tuƙuru domin cimma wannan nasara.

Shugaban ya yi addu’o’i na zaman lafiya, haɗin kai da ci gaba a Najeriya, yana kira ga ‘yan ƙasa da su mara wa duk wani yunƙuri da ke nufin kare da ƙarfafa ƙasar nan baya, domin fuskantar ƙalubalen da ke gabanta.

Obi ya bar ADC zuwa NDC

A baya, kun ji cewa tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa na jam'iyyar LP, Peter Obi, ya tabbatar da cewa ba zai iya ci gaba da zama a cikin jam’iyyar ADC ba.

Kara karanta wannan

Ganduje, manyan APC sun saya wa Abba fam, an tara N50bn don takarar Tinubu a 2027

Peter Obi ya bayyana cewa yanayin siyasar Najeriya yanzu ya koma tamkar guba da ke barazana ga duk masu son yin shugabanci na gaskiya domin kawo canji.

Yayin da yake bayyana dalilin ficewarsa daga ADC, Peter Obi ya ce matakinsa ba shi da alaƙa da David Mark ko kuma Atiku Abubakar, Sai dai ra'ayin mai nemo mafita.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng