Ta Faru Ta Kare: Kwankwaso da Peter Obi Sun Sauya Sheka zuwa Jam'iyyar NDC

Ta Faru Ta Kare: Kwankwaso da Peter Obi Sun Sauya Sheka zuwa Jam'iyyar NDC

  • Manyan ƴan adawa, Peter Obi da Rabiu Musa Kwankwaso, sun bayyana komawarsu jam’iyyar NDC a hukumance, bayan fice wa daga ADC
  • Sun yi kira ga mambobin jam’iyyar da su guji yawan shari’o’in kotu, su mayar da hankali kan ci gaban ƙasa da kuma haɗin kan al’ummar Najeriya
  • A bikin shigarsu NDC, Peter Obi da Rabiu Kwankwaso sun aika muhimmin sako ga magoya bayansu yayin ake tunkarar babban zaben 2027

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza ƙwararren edita ne a fannin nishaɗi, al'amuran yau da kullum, da kuma siyasa, wanda ke da shekaru sama da biyar a aikin jarida.

Abuja – A ranar Lahadi ne aka karɓi manyan ƙusoshin siyasar ƙasar nan, Peter Obi da tsohon gwamnan jihar Kano, Rabiu Musa Kwankwaso, cikin jam’iyyar NDC a hukumance a birnin Abuja.

Peter Obi ya bayyana komawarsa NDC ne jim kaɗan bayan ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar ADC.

Kara karanta wannan

"Za mu yi cikakkiyar biyayya": NDC ta mika sakonni ga Kwankwaso bayan sauya sheka

Sanata Rabiu Kwankwaso da Peter Obi sun sauya sheka zuwa jam'iyyar NDC
Hagu zuwa dama: Peter Obi, Seriake Dickson, da Sanata Rabiu Kwankwaso. Hoto: @ADCVanguard
Source: Twitter

Kwankwaso, Obi sun koma jam'iyyar NDC

Jaridar TheCable ta ruwaito Peter Obi ya bayyana cewa sun zaɓi NDC ne domin samun jam'iyya mai zaman lafiya wadda ba ta fama da rikice-rikicen cikin gida ko katsalandan daga hukumomin gwamnati.

A yayin da yake magana lokacin karɓar katin shaidar shiga NDC, Peter Obi ya jaddada cewa burinsu shi ne gina ƙasa mai tsaro da wadata inda kowane yaro zai iya zama wani ba tare da sanin kowa ba.

Ya zargi gwamnatin yanzu da rura wutar rikici a cikin jam’iyyun adawa, wanda ke tilasta ƴan siyasa shiga shari’o’in kotu marasa ƙarewa.

Obi ya buƙaci dukkan ƴan Najeriya da su shigo cikin wannan "jirgi" domin magance matsalolin da ke damun talaka.

Peter Obi ya ce:

“Ba ma son ɓata lokacinmu a kotu. Za mu yi amfani da lokacinmu ne wajen tattauna al’amuran da suka shafi talakan Najeriya.”

Manufofin Kwankwasoda Kwankwasiyya a NDC

Kara karanta wannan

Zance ya kare: Peter Obi ya fice daga jam'iyyar ADC, ya bayyana dalili

A nasa ɓangaren, Rabiu Musa Kwankwaso ya bayyana cewa sun gano cewa NDC tana da akida ɗaya da su, musamman ta fuskar son samar da ilimi, tsaro, da haɗin kan ƙasa.

Ya yi kira ga magoya bayansa na ƙungiyar Kwankwasiyya da tsohuwar jam’iyyarsa ta NNPP da su garzaya su yi rajista da NDC kafin rufe rajistar a ranar 6 ga watan Mayu.

Ya bayyana cewa shi da Peter Obi suna kan shafi ɗaya dangane da tsarin samar da ayyukan yi ga matasa da kuma ƙarfafa mata.

Kwankwaso da Peter Obi sun koma NDC bayan ficewa daga ADC
Hagu zuwa dama: Sanata Aisha Binani, Peter Obi, Seriake Dickson, Atiku Abubakar. Hoto: @RakaFatima
Source: Facebook

Sabon fasalin siyasar 2027

Manyan mutanen biyu sun karɓi katin mambobin jam’iyyar NDC ne a gaban dandazon magoya bayansu bayan sun fito daga wani taron sirri da shugabannin jam’iyyar.

Ana kallon wannan haɗin gwiwa tsakanin Obi da Kwankwaso a matsayin wani babban ƙalubale ga jam’iyyar APC mai mulki. in ji rahoton Punch.

Ficewar Obi daga ADC ta zo ne sakamakon abin da ya kira "guba" a cikin tsarin siyasa, inda ya bayyana cewa an mayar da mutunci wani abu da ba a darajawa.

Dalilin ficewar Obi daga jam'iyyar ADC

A wani labari, mun ruwaito cewa, tsohon ɗan takarar shugaban ƙasa, Peter Obi, ya tabbatar da cewa ba zai iya ci gaba da zama a cikin jam’iyyar ADC ba.

Kara karanta wannan

Dalilin da ya sa Kwankwaso da Peter Obi ke shirin barin ADC

Peter Obi ya bayyana cewa yanayin siyasar Najeriya yanzu ya koma tamkar guba da ke barazana ga duk masu son yin shugabanci na gaskiya.

Yayin da yake bayyana dalilin ficewarsa daga ADC, Peter Obi ya ce matakinsa ba shi da alaƙa da David Mark ko kuma Atiku Abubakar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza (Hausa Editor) Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i. Imel: sanihamzafuntua@gmail.com