Ana Wata ga Wata: Yayin da Zaben 2027 ke Karatowa, Atiku Ya Maka Tinubu a Kotu
- Tsohon mataimakin shugaban kasa Atiku Abubakar ya shigar da karar Bola Tinubu a kotu ana shorye-shiryen zaben shekarar 2027
- Atiku da jam’iyyar ADC sun zargi Tinubu da gabatar wa INEC takardar shaidar NYSC da ke dauke da suna “Tinubu Bola Adekunle”
- Sun bukaci kotu ta binciki takardun, tare da duba ko bambancin sunan ya shafi cancantar takarar Bola Tinubu takararsa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Abuja - Tsohon mataimakin shugaban Najeriya kuma dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar ADC, Atiku Abubakar, ya maka Bola Tinubu a kotu.
Atiku ya gabatar da takardar shaida a matsayin hujja wajen karar da ya shigar domin kalubalantar cancantar Shugaba Bola Ahmed Tinubu na neman takarar shugaban kasa a zaben 2027.

Source: Facebook
Hujjojin Atiku na maka Tinubu a kotu
Atiku da ADC sun shigar da karar ne kan Tinubu, jam’iyyar APC mai mulki da Hukumar Zabe Mai Zaman Kanta ta Kasa (INEC), cewar Punch.
Matakin ya dogara da wasu tanade-tanaden Kundin Tsarin Mulkin Najeriya na 1999, da aka yi wa kwaskwarima, da kuma wasu tanade-tanaden Dokar Zabe ta 2026.
A cikin muhimman batutuwan karar akwai sashe na 137(1)(j) na Kundin Tsarin Mulki, wanda ya tanadi cewa mutum ba zai cancanci tsayawa takarar shugaban kasa ba idan ya gabatar wa INEC takardar shaidar bogi.
Masu karar sun bukaci kotu ta tantance ko ya kamata a hana Tinubu da APC shiga zaben shugaban kasa na 2027 bisa zargin cewa Tinubu ya gabatar da takardar shaidar NYSC ta bogi a lokacin zaben 2023 da kuma shirin zaben 2027.
Bayan ya rantse, Atiku ya ce ya halarci kotun da kansa ne domin batun da ke gabanta ya shafi Kundin Tsarin Mulki da mutuncin ofishin shugaban kasa.
Ya ce:
“Na zo nan da kaina ne saboda batutuwan da ke gaban kotu sun shafi tushen Kundin Tsarin Mulkinmu da mutuncin ofishin shugaban kasa.
Saboda haka, na sanya sunana, sa hannuna da rantsuwata a kan bayanan da muke gabatarwa a kotu, yanzu lokaci ya yi da Shugaba Tinubu zai ba da amsarsa."

Source: Facebook
Karin zarge-zargen Atiku kan Tinubu
A cikin takardar rantsuwarsa, Atiku ya yi zargin cewa Tinubu ya gabatar wa INEC da takardar shaidar sallamar NYSC mai dauke da suna “Tinubu Bola Adekunle”, wanda masu karar suka ce ya bambanta da sunan shugaban kasa, Bola Ahmed Tinubu.
Takardar rantsuwar ta kuma yi zargin cewa an sake gabatar da wannan takardar shaidar a lokacin shirin zaben shugaban kasa na 2027, masu karar sun ce takardar ba takardar shaidar da Tinubu ya samu ba ce.
Atiku ya kuma bukaci INEC ta gabatar da Form CF001 da Tinubu ya cike domin zaben shugaban kasa na 2023 da kuma 2027.
Ya ce wannan ne dalilin da ya sa suka garzaya kotu, domin ba sa son ’yan Najeriya su yanke hukunci kan lamarin ta kafafen sada zumunta.
Atiku ya ce ba sa neman INEC ta zama kotu, sai dai hukumar da ke rike da bayanan ta gabatar da su, sannan kotu ta binciki hujjojin ta yanke hukunci.
Ya kara da cewa:
“Idan takardar shaidar ta Bola Ahmed Tinubu ce, a tabbatar da hakan a gaban kotu. Idan ‘Tinubu Bola Adekunle’ da ‘Bola Ahmed Tinubu’ mutum daya ne dangane da wannan takardar, hujjoji su tabbatar da hakan."
Atiku ya ce wadannan batutuwa sun cancanci samun amsa, maimakon a mayar da su rikicin siyasa ko zagi, cewar The Guardian.
Baya ga batun takardar shaidar, Atiku da ADC sun kuma kalubalanci wasu tanade-tanaden Dokar Zabe ta 2026.
Sun yi ikirarin cewa dokar da Majalisar Dokoki ta Kasa ta kafa ba za ta iya hana aiwatar da wani tanadi kai tsaye da Kundin Tsarin Mulki ya tanada ba.
Zaben Osun: Atiku ya gargadi Tinubu, INEC
An ji cewa Atiku Abubakar ya gargadi INEC da hukumomin tsaro kan yawaita jami’an tsaro a zaben gwamnan Osun, yana mai cewa zaben gwaji ne ga Najeriya.
Dan takarar shugaban kasa na ADC ya ce zabe aikin farar hula ne, ba aikin soja ba, yana mai neman a tabbatar da gaskiya da adalci.
Atiku ya kuma bukaci a fayyace bambance-bambancen da aka ruwaito a takardar shaidar karatun Tinubu da aka gabatar wa INEC.
Asali: Legit.ng


