Hukumar EFCC Ta Fada wa Sanatoci Yadda Suka Tatso Naira Biliyan 200

Hukumar EFCC Ta Fada wa Sanatoci Yadda Suka Tatso Naira Biliyan 200

  • Hukumar EFCC ta gudanar da bincike a kan kamfanoni fiye da 40 inda ta gano gaskiyar cewa ana bin kamfanoni 24 bashin haraji
  • An riga an mika mafi yawan kudaden da aka kwato ga hukumar NDDC domin gudanar da ayyuka yadda ta saba a yankin Neja-Delta
  • Wannan mataki ya biyo bayan binciken kwamitin Majalisar Dattawa a kan rahoton NEITI game da kudin da aka kashe daga 2021-23

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada

Abuja - Hukumar EFCC mai yaki da rashin gaskiya ta ce ta karbo N83.59bn da $98.07m na bashin da ake bin wasu kamfanoni dabam-dabam.

Hukumar NDDC tana bin wadannan kamfanoni na mai bashin harajin 3% da ake tatsa daga hannunsu kamar yadda dokar kasa ta tanada.

EFCC.
Shugaban hukumar EFCC wajen karbar lambar yabo Hoto: Economic and Financial Crimes Commission (EFCC)
Source: Facebook

Kwamitin Majalisar dattawa ya zauna da EFCC

The Cable ta rahoto Francis Usani yana bayanin nasarar da aka samu yayin da ya zauna gaban kwamitin binciken asusun gwamnati.

Kara karanta wannan

Ma'aikatar gwammatin tarayya ta gaza bayanin yadda aka kashe tiriliyoyin Naira a Najeriya

Francis Usani shi ne mataimakin hukumar na musamman wajen tabbatar da bin ka’ida.

Kwamitin Majalisar dattawa yana bincike a kan rahoton kudin da aka batar wajen harkokin mai da hukumar NEITI ta fitar kwanakin baya.

NEITI ta bi yadda aka kashe kudi a bangaren mai da gas tun daga shekarar 2021 zuwa 2023.

Sanata Dankwambo yana jagorantar bincike a majalisa

Shugaban kwamitin da ke wannan aiki a Majalisar Tarayya shi ne sanata mai wakiltar Gombe ta Arewa, Ibrahim Hassan Dankwambo.

Sanata Ibrahim Hassan Dankwambo da abokan aikinsa suna kokarin duba bashin da yake kan manyan kamfanonin mai a kasar nan.

A cewar binciken EFCC, hukumar NEITI ta gano N90.046bn da $229.534m da ya kamata a biya tsakanin shekarun 2015 da 2020.

Bayan abin da ta NEITI ta gano, Mista Usani ya ce EFCC ta gayyaci kamfanoni 43 da ke harkar mai a Neja Delta in ji jaridar This Day.

Kara karanta wannan

Gwamntin Tinubu na neman 'ƙaryata' rahoton da ƙasar Amurka ta fitar kan Najeriya

Gayyatar da EFCC ta yi ya nuna mata kamfanoni 24 suna da bashin kudi a wuyansu sannan akwai 19 da ba a bin su bashin ko kobo.

Hukumar EFCC
Wani jami'in kasar waje tare da shugaban hukumar EFCC a Abuja Hoto: Economic and Financial Crimes Commission (EFCC)
Source: Facebook

Kamfanoni 24 sun soma biyan bashin da ake binsu

EFCC ta samo N76.884bn da $81.077m kai-tsaye daga kamfanonin 24, kuma aka biya kudin a asusun karbo bashi da yake CBN.

Bayan haka ne hukumar ta saki N73.373bn da $67.071 ga NDDC da ke aiki a Neja-Delta.

Rahoton ya ce NDDC ta kuma samu N6.7bn da $17m da wasu kamfanonin man suka biya kai-tsaye cikin asusunta na tattara haraji.

Zuwa ranar 31 ga watan Yuli, EFCC ta ce akwai N3.510 da $14.006m da suka rage a wannan asusu na musamman a bankin CBN.

An nemi a yi waje da shugaban EFCC

Rahoto ya ce jam'iyyun adawa na buƙatar Shugaban EFCC, Ola Olukoyede, ya yi murabus ko kuma Shugaba Bola Tinubu ya kore shi.

Wannan matsin lamba ya biyo bayan daskarar da asusun gwamnatin jihar Osun da hukumar ta yi ana shirin gudanar da zaben gwamna.

Sai dai Shugaba Tinubu ya umarci a buɗe asusun, inda ya bayyana matakin hukumar a matsayin abin kunya a wani jawabi da ya yi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Muhammad Malumfashi avatar

Muhammad Malumfashi (Hausa writer) M. Malumfashi ya samu Digirin farko a ilmin komfuta a ABU Zaria. Baya ga haka ya yi Digirgir a fannin kula da bayanai da wani Digirgir a ilmin aikin jarida duk daga jami'ar. Malumfashi ya kan kawo labaran siyasa, addini, wasanni da al’ada. Ya halarci taron karawa juna sani iri-iri. Imel: muhammad.malumfashi@corp.legit.ng