"Umarnin Jagora": Jigo a Kwankwasiyya Ya Fice daga Jam'iyyar ADC a Jihar Kano
- Fitaccen jagora a tafiyar Kwankwasiyya, Kabiru Adamu Abdullahi ya fice daga jam'iyyar haɗakar adawa da ADC a Kano
- Ya bayyana rabuwa da jam'iyyar a lokacin da ake raɗe-raɗin Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso da tawagarsa za su bar ADC
- Kabiru Adamu Abdullahi ya bayyana cewa wannan sauya sheka da ya yi umarnin jagora ne, sannan ya yi wa ADC fatan alheri
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Jihar Kano – Wani jigo a tafiyar Kwankwasiyya a ƙaramar hukumar Dala ta jihar Kano, Hon. Kabiru Adamu Abdullahi, ya sanar da ficewarsa daga jam’iyyar ADC.
Ya bayyana haka ne a lokacin da maganganu suka yi yawa game da yiwuwar sauya shekar Sanata Rabi'u Musa kwankwaso da mutanensa a cikin ƴan kwanakin nan.

Source: Facebook
Wannan na kunshe a cikin wata wasiƙar murabus da ya wallafa a shafinsa na Facebook mai ɗauke da kwanan watan 1 ga Mayu, 2026, da ya aika wa shugaban jam’iyyar a mazabar Kofar Ruwa.
Babba a Kwankwasiyya ya ba jam'iyyar ADC
A cikin wasikar, Hon Adamu Abdullahi ya bayyana cewa ya fice daga jam’iyyar hamayya ta ADC nan take ba tare da ɓata lokaci.
Ya ce:
“Ina sanar da ficewata daga jam’iyyar ADC a mazabar Kofar Ruwa a hukumance, kuma nan take.”
Hon Kabiru Adamu Abdullahi ya kara da cewa ya na godiya ga damar da aka ba shi na kasancewa cikin jam’iyyar, tare da yi musu fatan alheri a gaba.

Source: Facebook
Ya ce:
“Ina matuƙar godiya da damar da aka ba ni na kasancewa cikin wannan jam’iyya, kuma ina yi muku da jam’iyyar fatan alheri a dukkannin al’amuranku na gaba.
Dalilin Kabiru Adamu ya bar ADC
Kabiru Adamu Abdullahi na daga cikin fitattu kuma jiga-jigan Kwankwasiyya a Dala, kuma yana cikin masu neman takarar kujerar majalisar dokokin jihar Kano.
A sakonsa, Hon Adamu Abdullahi ya danganta matakin da ya ɗauka da umarnin jagoran tafiyar Kwankwasiyya.
Ya rubuta cewa:
"Umarnin Jagora.”
Bayan wadannan kalamai ne kuma ya sanya hoton da wasikar murabus daga jam'iyyar ADC da suka koma kwanaki kadan da suka gabata.
Ya yi addu'ar Allah Ya sa rabuwa da ADC da ya yi ya zama mafi alheri a gare su baki daya.
Kwankwaso da Obi za su bar ADC
A wani labarin, kun ji cewa alamu sun nuna cewa 'yan Kwankwasiyya da ke shirin hada kai da Peter Obi na iya sauya sheka daga babbar jam'iyyar adawa ta ADC.
Manyan 'yan Kwankwasiyya, Dr Yusuf Kofarmata da Sanata Rufa'i Hanga sun nuna cewa har yanzu jam'iyyar ADC na cikin rikici Duk da hukuncin kotun koli.
Masana da dama sun fara gargadin Sanata Rabiu Kwankwaso da Peter Obi kan shirin sauya sheka da ake hasashen za su yi kafin babban zaben 2027 da ke tafe.
Asali: Legit.ng

