Gwamntin Tinubu na Neman 'Karyata' Rahoton da Kasar Amurka Ta Fitar kan Najeriya
- Fadar shugaban kasa ta yi fatali da rahoton Amurka, wanda ya nuna damuwa kan yadda ake tafiyar da harkokin kudin Najeriya
- Rahoton da kasar Amurka ta fitar ya ce Najeriya ta gaza cika mafi karancin ka’idojin bayyana bayanan kasafin kudi
- Gwamnatin Tarayya ta ce tana ci gaba da gyare-gyare domin inganta kudaden shiga da kashe-kashen gwamnati
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Abuja, Nigeria - Mai ba Shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu shawara na musamman kan yada labarai da sadarwar jama’a, Sunday Dare, ya maida martani kan rahoton Amurka.
Ya ce sabon rahoton Amurka kan bayyana harkokin kudin Najeriya bai yi cikakken nazari da tantance sauye-sauyen da gwamnatin kasar ke aiwatarwa ba.

Source: Twitter
Dare ya bayyana hakan ne a wata sanarwa da ya fitar a shafinsa na X, inda ya mayar da martani kan rahoton mai taken, '2026 Fiscal Transparency Report' na Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka.

Kara karanta wannan
Amurka ta daina boye boye, ta bayyana manufofi 2 da take son cimmawa a yaki da Iran
Rahoton ya ce Najeriya ba ta cika mafi karancin bukatun Amurka na bayyana cikakkun bayanan harkokin kudin gwamnati ba, tare da cewa kasar ba ta samu wani gagarumin ci gaba ba a lokacin da aka gudanar da binciken.
Fadar shugaban kasa ta yi martani
Dare ya ce ya kamata a fahimci rahoton bisa tsarin da aka yi amfani da shi wajen tantance kasashen.
A cewarsa, rahoton na duba kasashe ne bisa wasu takamaiman bukatun Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka, musamman yadda ake fitar da bayanan kasafin kudin kasa, kwangilolin gwamnati da lasisin albarkatun kasa.
Ya ce:
“Rahoton Amurka kan bayyana harkokin kudi wani takaitaccen bincike ne da aka yi bisa mafi karancin ka’idojin bayyana alkaluman kudi da Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ta gindaya.”
Dare ya ce saboda haka bai kamata a dauki rahoton a matsayin cikakken bayanin dukkan gyare-gyaren da Najeriya ke aiwatarwa a fannin tafiyar da kudaden gwamnati ba.
Ya ce Najeriya na samun ci gaba
Mai ba shugaban kasa shawarar ya ce rahoton da kansa ya amince cewa Najeriya na samun ci gaba wajen kasafin kudin gwamnati da bayanan basussukan kasa.
Ya ce bangarorin da rahoton ya nuna akwai gibi a kansu, ciki har da fito da bayanan sayen kayayyaki da ayyukan gwamnati, rahoton yadda aka aiwatar da kasafi da kuma tsarin binciken kudi, na daga cikin abubuwan da gwamnatin Tarayya ke kokarin gyarawa.
Dare ya ce:
“Bayyana wa jama'a harkokin kudi, rikon amana da ingantaccen tsarin tafiyar da kudaden gwamnati na daga cikin muhimman abubuwan da gwamnatin Tarayya ta sa a gaba.”
Gwamnati na aiwatar da sauye-sauye
Dare ya ce Najeriya ta samar da wasu tsare-tsare kamar Open Treasury Initiative, bayyana bayanan kasafin kudi da bayanan basussuka domin inganta gaskiya da bayyana yadda ake tafiyar da kudaden gwamnati.

Source: Twitter
Ya kara da cewa gwamnati na kuma karfafa tsarin sayen kayayyaki ta hanyar fasahar zamani da sauran hanyoyin inganta samun bayanan kudin gwamnati cikin sauki da inganci.

Kara karanta wannan
Tinubu zai wallafa yadda aka kashe kudin da aka samu daga cire tallafin man fetur
A cewarsa, rahoton zai iya zama wata ma’auni daga waje da za ta taimaka wajen kara karfafa sauye-sauyen da ake gudanarwa.
Atiku ya kafa hujja da rahoton Amurka
A wani labarin, kun ji cewa Atiku Abubakar ya ce wani rahoton Ma’aikatar Harkokin Wajen Amurka ya tabbatar da korafe-korafen da ya yi kan gwamnatin Bola Tinubu.
Atiku ya ce rahoton, wanda ma'aikatar harkokin wajen Amurka ta fitar, ya tabbatar da damuwar da ya dade yana bayyana wa kan rashin gaskiya da cikakken bayani wajen tafiyar da kudaden Najeriya.
Asali: Legit.ng
