Amurka Ta Daina Boye Boye, Ta Bayyana Manufofi 2 da Take Son Cimmawa a Yaki da Iran

Amurka Ta Daina Boye Boye, Ta Bayyana Manufofi 2 da Take Son Cimmawa a Yaki da Iran

  • Mataimakin shugaban Amurka JD Vance ya ce manufofin Amurka a yaƙin Iran sun ta’allaka ne kan tattalin arziki da soji
  • Vance ya ce Amurka na son dawo da daidaiton farashin makamashi bayan rufe mashigar Hormuz na tsawon lokaci
  • Mataimakin shugaban kasar na Amurka ya kuma yi hasashen yadda yakin wanda ya shafe watanni zai zo karshe

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Birnin Washington, Amurka - Mataimakin Shugaban Amurka, JD Vance, ya bayyana cewa manufofin Amurka a yakin da take yi da Iran sun kasu gida biyu.

JD Vance ya bayyana manufofin guda biyu da Amurka ke son cimmawa a yaki da Iran shafi tattalin arziki da soji.

Vance ya fadi manufofin Amurka kan Iran
JD Vance na jawabi a wajen taro Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Vance ya bayyana hakan ne yayin wata hira da mai gabatar da shirin Fox News, Will Cain, inda ya yi bayani kan abin da gwamnatin Amurka ke son cimmawa a rikicin da Iran.

Kara karanta wannan

Ana wata ga wata: Rahoton Amurka ya tabbatar da zargin Atiku kan gwamnatin Tinubu

Menene manufar Amurka ta farko?

Vance ya ce manufar farko ita ce tabbatar da cewa kasashen yankin Gulf sun ci gaba da fitar da mai da iskar gas zuwa kasuwannin duniya.

A cewarsa, rufe mashigar Hormuz na tsawon lokaci ya kawo barazana ga tattalin arzikin duniya saboda muhimmancin mashigar wajen jigilar makamashi.

Ya ce Amurka na son tabbatar da samun wadataccen mai da iskar gas domin samun daidaiton farashin makamashi a duniya, musamman ga Amurkawa.

Vance ya ce wannan na daga cikin manyan abubuwan da gwamnatin Trump ke son cimmawa yayin da take fuskantar rikicin Iran.

Hana Iran samun makamin Nukiliya

Ya ce manufa ta biyu ta shafi bangaren tsaro, inda Amurka ke son tabbatar da cewa Iran ba ta mallaki makamin nukiliya ba.

Vance ya bayyana kwarin gwiwar cewa Amurka na samun nasara wajen cimma manufofin biyu.

Sai dai ya amince cewa lamarin na da rashin tabbas saboda, a cewarsa, Iran ba ta da saukin hasashe kuma a wasu lokuta tana iya kin cika alkawuran da ta dauka.

Kara karanta wannan

Trump ya sake cika baki kan mashigar Homruz da ake takaddama a kai da Iran

Yadda yakin zai kare

Da aka tambaye shi yadda yakin zai kare, musamman ganin cewa tattaunawar zaman lafiya tsakanin Amurka da Iran ta tsaya cak, Vance ya ce Amurka na son kawo karshen rikicin ne daga matsayi mai karfi.

Ya bayyana cewa abin da Amurka ke nema shi ne Iran ta kasance ba tare da makamin nukiliya ba, sannan a sake bude mashigar Hormuz cikin yanayin da zai ba da damar samun daidaiton farashin mai da iskar gas.

Vance ya ce sakamakon da Amurka ke fata shi ne kawo karshen rikicin tare da tabbatar da tsaron makamashi da kuma hana Iran mallakar makamin nukiliya.

Vance ya yi magana kan yaki da Iran
Mataimakin shugaban kasar Amurka, JD Vance Hoto: Getty Images
Source: Getty Images

Amurka ta soki Israila

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnatin kasar Amurka ta ragargaji takwararta ta Israila kan kin janye sojojinta daga kasar Lebanon.

Gwamnatin Amurka ta soki kalaman Ministan Tsaron Isra’ila, Israel Katz, bayan ya ce sojojin ƙasar za su ci gaba da kasancewa a yankunan tsaro da ke kudancin Lebanon.

Israei Katz dai ya bayyana cewa Isra’ila ba za ta janye sojojinta daga yankunan da ta kira na tsaro ba daga Kudancin Lebanon.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng