Alƙawarin da Garo Ya Yi wa Abba da 'Yan Kano bayan Zabo Ya Shi Ya Zama Mataimakin Gwamna

Alƙawarin da Garo Ya Yi wa Abba da 'Yan Kano bayan Zabo Ya Shi Ya Zama Mataimakin Gwamna

  • Murtala Sule Garo da Abba Kabir Yusuf ya nemi ya zama mataimakin gwamnan Kano ya yi magana bayan tura sunansa majalisa
  • A sakonsa na farko, Murtala Sule Garo ga gode wa Allah SWT da gwamna Abba Kabir Yusuf kan nadinsa a matsayin mataimaki
  • Ya bayyana aniyar da ke ransa ta tabbatar da ci gaban Kano tare da yaba wa ayyukan Abba Kabir Yusuf na ci gaban kasa

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Kano – Murtala Sule Garo da ake shirin nada wa a matsayin mataimakin gwamnan Kano ya bayyana matukar godiya ga Allah Madaukakin Sarki da ya ba aka zabe shi.

Garo ya bayyana haka ne a sakon farko da ya fitar tun da aka fara batun nada shi a matsayin mataimakin gwamna Abba Kabir Yusuf a Kano.

Kara karanta wannan

2027: Kano da wasu jihohin Arewa 7 da majalisa ke son haramta wa yin kamfen

Murtala Garo ya aika sako ga Abba
Gwamna Abba Kabir Yusuf tare da Murtala Sule Garo Hoto: @Minikothe3rd
Source: Twitter

A sakon da ya wallafa a shafinsa na Facebook, Garo ya mika godiya ta musamman ga zababben gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, bisa amincewa da ya yi na mika sunansa ga majalisar dokokin jihar domin tantancewa da tabbatar da shi a matsayin mataimakin gwamna.

Murtala Garo ya gode wa Gwamnan Kano

A hira da ya yi siyasarmu TV da aka wallafa a Facebook, Garo ya bayyana wannan mataki a matsayin babban abin alfahari da karramawa, yana mai cewa ba zai taba mantawa da wannan karamci ba.

Haka kuma, ya gode wa shugabannin jam’iyya, masu ruwa da tsaki da daukacin al’ummar Kano bisa kauna, addu’o’i da goyon bayan da suka nuna masa.

A cewarsa:

“Dole ne na jaddada godiyarmu mara iyaka ga Allah SWT, sannan mu jaddada godiya ga zaɓaɓɓen gwamna Alhaji Abba Kabir Yusuf, da kuma Uba Dr. Abdullahi Umar Ganduje, da mutane kamar Sanata Kawu Sumaila.”

Kara karanta wannan

Dalilan da suka sanya Abba zabar Garo a mataimakin gwamnan Kano

Ya kuma kama sunayen jiga-jigan APC daga ciki har da Abdullahi Tijjani Gwarzo da ya fito neman kujerar Sanata Barau Jibrin a Kano, amma bai kama sunan mataimakin shugaban majalisar dattawan ba.

'Dan siyasar ya godewa irinsu Abdulmumin Jibrin da wasu manyan Kano da ke majalisar tarayya.

Garo ya yi wa Kanawa alƙawari

Murtala Sule Garo ya jaddada cewa nadin da aka yi masa ba karramawa ba ce kawai, babban nauyi ne da ke bukatar sadaukarwa domin yi wa al’ummar Kano hidima.

Ya yi kira ga dukkannin shugabanni da ƴan jam’iyya, har da wadanda suka nemi wannan mukami, da su hada kai domin cigaban jihar.

Ya ce:

“Ina so yin amfani da wannan dama wajen yin kira na musamman ga dukkannin shugabanni da ƴan jam’iyyarmu, daga ciki har da wadanda suka nemi wannan matsayi, da mu kara hada kai cikin kauna da ’yan uwantaka, mu yi aiki tare domin cigaban jahar Kano mai albarka.”

Garo ya kuma tabbatar da cewa zai ci gaba da sadaukar da kai wajen karfafa hadin kai da kuma tallafawa manufofi da shirye-shiryen ci gaban da gwamna ya assasa.

Kara karanta wannan

Majalisar dokokin Kano ta fara aiki kan nadin sabon mataimakin gwamna, Mutala Garo

Murtala Sule Garo ya yi alkawarin aiki tukuru
Fitaccen ɗan siyasa a Kano, Murtala Sule Garo Hoto: Majidadin Murtala Sule Garo
Source: Facebook

Ya ce:

"Ina tabbatar muku da cewa zan cigaba da sadaukar da kai, biyayya da aiki tukuru domin karfafa hadin kai da tallafawa manufofin da shirye-shiryen ci gaba da Maigirma Gwamna ya assasa.”

Ya yi alkawarin bayar da gudunmawarsa domin tabbatar da cewa gwamnan ya sauke nauyin da ke kansa tare da bunkasa ayyukan raya jihar Kano.

“Da yardar Allah, zan yi duk me yiwuwa wajen bayar da gudunmawa ta wajen ganin mai girma gwamna ya sauke nauyin shugabancin da Allah ya dora masa da kuma kara bunkasa ayyukan raya Jihar Kano."

Abba ya zaɓi mataimakin gwamna

A baya, mun wallafa cewa Gwamna Abba Kabir Yusuf ya tura sunan Murtala Sule Garo ga majalisar Kano a matsayin mataimakin gwamna da za a tantance.

Hakan na zuwa ne bayan murabus da tsohon mataimakinsa, Aminu Abdulsalam Gwarzo ya yi da komawa jam'iyyar adawa ta ADC bayan zargin da majalisa ta yi masa.

Kara karanta wannan

Murtala Garo: Abubuwan sani game da mai iya zama sabon mataimakin gwamnan Kano

Kwamred Aminu Gwarzo ya koma ADC tare da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso yayin da Abba Kabir Yusuf ya shiga jam'iyyar APC mai mulkin Najeriya.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng