Tallata Tinubu Ya Kusa Aika Mawaki Barzahu bayan Matasa Sun Dura Kansa a Legas

Tallata Tinubu Ya Kusa Aika Mawaki Barzahu bayan Matasa Sun Dura Kansa a Legas

  • Wani mai tallata mawaka, Ijoba Danku ya bayyana cewa ya sha da kyar bayan wasu fusatattun matasa sun kai masa hari a Legas
  • Da ya ke magana daga gadon asibiti, Danku ya ce an kai masa harin ne kawai saboda goyon bayan Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu
  • Ya bayyana cewa an jikkata shi tare da lalata motarsa a kusa da New Afrika Shrine a lokacin da matasan suka dura a kansa

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Jihar Lagos – Shahararren mai tallata mawaka a Najeriya, Ijoba Danku, ya bayyana halin da ya shiga bayan wasu matasa sun kai masa hari a birnin Legas.

Ya bayyana cewa matasan sun kai masa harin ne saboda goyon bayan da yake nuna wa Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da kuma jam’iyya mai mulki ta APC.

Kara karanta wannan

'Yan bindiga sun shiga Kano da makamai cikin dare, sun yi kisa

Ijoba Danku ya ce ya daku a hannun fusatattun matasa
Fitacce a harkar waƙa, Ijoba Danku kwance a asibiti, Shugaba Bola Tinubu Hoto: Ijoba Na Danku/Bayo Onanuga
Source: Facebook

Nigerian Tribune ta wallafa cewa Danku, wanda aka fi sani da taka rawar gani wajen tallata sababbin mawaka a fagen wakokin street-hop, ya ce lamarin ya faru ne a ranar farkon makon nan.

An kai wa mai tallata Tinubu hari

Premium Times ta wallafa cewa lamarin ya faru ne a yankin Illeshu, kusa da sanannen wurin nishaɗi na New Afrika Shrine da ke jihar Legas.

Fitaccen ɗan harkar waƙa da ke kwance a gadon asibiti ya musanta rade-radin da ke cewa lamarin fashi da makami ne ya rutsa da shi.

A cewarsa, harin yana da alaka da siyasa ne kai tsaye da kuma yadda ya tsaya yana tallata Bola Tinubu da APC.

Ya ce:

“An kai mani hari jiya a kan titin Illeshu daga wasu matasa kawai saboda ina goyon bayan APC da Asiwaju 2027.”

An jikkata mawaki a Legas

Sannan ya kara da cewa maharan sun jikkata shi tare da lalata motarsa, abin da ya kara jefa damuwa a tsakanin mabiyansa da masu bibiyar harkokin nishadi a Najeriya.

Kara karanta wannan

A yi hattara: NNPCL ya fitar da gaskiya kan zargin gwanjon kayan matatun Najeriya

Sai dai, har zuwa lokacin hada wannan rahoto, babu wata sanarwa a hukumance daga jami’an tsaro da ke tabbatar da ainihin abin da ya faru ko kuma gano wadanda ake zargi da aikata harin.

Danku ya ce babu ruwan ƴan fashi a harin da aka kai masa
Ijoba Danku, Shugaban Najeriya Bola Tinubu Hoto: Ijoba Na Danku/Bola Tinubu
Source: Instagram

Lamarin ya jawo cece-kuce a kafafen sada zumunta, inda wasu ke nuna damuwa kan yadda siyasa ke iya haddasa tashin hankali, yayin da wasu ke kira ga hukumomi da su gudanar da bincike mai zurfi domin gano gaskiyar abin da ya faru.

Tinubu: 'Dan fim ya magantu kan lallasa shi

A baya, mun wallafa cewa a kwanakin bayan nan aka rika yada rade radin cewa an yi wa jarumin fim, Musa Mai Sana'a duka kan tallata shugaba Bola Tinubu.

'Dan fim din ya fito ya yi bayani kan hakikanin abin da ya faru da kuma halin da ya ke ciki bayan yada jita-jitar cewa an masa dukan tsiya a unguwarsu da ke jihar Kano.

Ya kuma bayyana dalilan da suka sanya shi cigaba da goyon bayan Shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu a hirar duk da zargin da wasu ke yi na cewa ya gaza.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano. aisha.ahmad@corp.legit.ng