Cikakken Jerin 'Yan Takara da Jam'iyyunsu da Ke Fafatawa a Zaben Gwamnan Osun

Cikakken Jerin 'Yan Takara da Jam'iyyunsu da Ke Fafatawa a Zaben Gwamnan Osun

  • Yayin da zaben gwamnan Osun ya zo, INEC ta ce mutane 2,339,233 ne suka yi rajistar kada kuri’a a jihar
  • Jam’iyyu 15 ne suka tsayar da ’yan takara, amma uku ne suka fi jan hankalin masu kada kuri’a yayin da aka kammala yakin neman zabe
  • Ademola Adeleke, Bola Oyebamiji da Najeem Salam ne ke kan gaba a fafatawar zaben gwamnan Osun na ranar Asabar, 15 ga watan Agustan 2026

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

​​​​​​​​​​​​​​Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi

Jihar Osun - Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa (INEC) za ta gudanar da zaben gwamnan a jihar Osun.

Hukumar INEC ta ce mutane 2,339,233 ne suka yi rajistar kada kuri’a jihar da ke yankin Kudu maso Yamma na Najeriya.

Yan takara na neman kujerar gwamnan Osun
Najeem Salam na ADC, Gwamna Ademola Adeleke na Accord da Bola Oyebamiji na APC Hoto: Najeem Salam, Ademola Adeleke, Bola Oyebamiji
Source: Twitter

Jaridar The Punch ta ce jam’iyyu 15 ne ke fafatawa a zaben, sai dai ’yan takara kalilan ne suka gudanar da yakin neman zabe mai karfi.

Kara karanta wannan

Osun 2026: Muhimman abubuwa 8 da ya kamata kowane mai katin zabe ya sani

Manyan ’yan takara uku

Duk da kasancewar ’yan takara daga jam’iyyu 15 a zaben, sunaye uku ne suka fi fitowa a matsayin manyan masu neman kujerar gwamna.

Su ne Ademola Adeleke na jam’iyyar Accord, wanda ke kan kujerar gwamna a yanzu; Bola Oyebamiji na All Progressives Congress (APC); da Najeem Salam na African Democratic Congress (ADC).

Adeleke na neman wa’adi na biyu

Ga Adeleke, zaben wata dama ce ta kare wa’adin da ya samu a shekarar 2022 tare da neman sake zama gwamna na tsawon shekaru hudu.

Gwamna Adeleke dan asalin Ede ya kasance dan kasuwa kuma mai gudanar da harkokin kamfanoni a Najeriya da Amurka kafin ya shiga siyasa.

Adeleke ya fara neman kujerar gwamnan Osun a shekarar 2018 a karkashin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP), amma ya sha kaye a hannun dan takarar APC, Adegboyega Oyetola.

Bayan shekaru hudu, Adeleke ya sake fafatawa da Oyetola, wanda a lokacin shi ne gwamnan jihar, inda ya yi nasara a zaben. An rantsar da Adeleke a matsayin gwamnan Osun a ranar 27 ga Nuwamba, 2022.

Kara karanta wannan

Muhimman abubuwan sani 11 kan jihar Osun yayin da ake gudanar da zaben gwamna

Jerin 'yan takarar gwamnan Osun

'Yan takarar da ke neman kujerar gwamnan jihar sun hada da:

  • Ademola Adeleke - Accord Party (AP
  • Bola Oyebamiji - All Progressives Peoples Congress (APC)
  • Najeem Salam - African Democratic Congress (ADC)
  • Farinloye Olarenwaju – Action Alliance (AA)
  • Esan Olajide – African Action Congress (AAC)
  • Adeagbo Opawoye – African Democratic Party (ADP)
  • Mustapha Adeniyi – Social Democratic Party (SDP)
  • Adesina Aseyemi-Doro – All Progressives Grand Alliance (APGA)
  • Adewale Adebayo – Allied People Movement (APM)
  • Clement Adesuyi – Action Peoples Party (AAP)
  • Masilo Adeleke – Boot Party (BP)
  • Taofeek Adeleke – New Nigeria Peoples Party (NNPP)
  • Saliu Oyelami – Peoples Redemption Party (PRP)
  • Ogunsakin Olalekan – Young Progressives Party (YPP)
  • Adefemi Adesuyi – Zenith Labour Party (ZLP)

An tsaurara matakan tsaro

Rundunar 'yan sandan Najeriya ta kara kaimi wajen shirye-shiryen samar da tsaro, insa ta tura manyan jami'ai.

Sufeto-Janar na ’Yan Sandan Najeriya, Olatunji Disu, ya hana Amotekun, da sauran kungiyoyin tsaro na sa-kai da kamfanonin tsaro masu zaman kansu shiga aikin tsaron zaben, cewar rahoton Channels tv.

Kara karanta wannan

Rana ba ta karya: Umarnin da Tinubu ya ba INEC da 'yan sanda kan zaben Osun

An kai jami'an tsaro jihar Osun
Shugaban rundunar 'yan sandan Najeriya, Olatunji Rilwan Disu Hoto: @PoliceNG
Source: Twitter

Disu ya kuma sake jaddada dokar hana ’yan rakiya dauke da makamai, mataimakan tsaro da sauran mutanen da ba a ba su izini ba rakiyar ’yan siyasa ko manyan baki zuwa rumfunan zabe da cibiyoyin tattara sakamakon zabe.

Sufeto-Janar din ya gargadi ’yan siyasa, magoya bayansu da masu shirin tayar da zaune tsaye cewa satar akwatin zabe, tsoratar da masu kada kuri’a, dabaibayar siyasa da sauran laifukan zabe za su jawo kama mutum da gurfanar da shi a gaban kotu.

Dabarar APC kan zaben Osun

A wani labarin kuma, shugaban masu rinjaye na majalisar dattawa, Sanata Opeyemi Bamidele, ya bayyana cewa APC za ta lashe zaben gwamnan jihar Osun.

Sanata Opeyemi Bamidele ya bayyana cewa APC za ta lashe zaben ne ta hanyar tsarin siyasarta, ba tare da dogaro da tasirin gwamnatin tarayya ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal (Hausa Editor) Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng