‘Ba Su Yi Mana Ta’aziyya Ba’: Hadimim Marigayi Ɗan Majalisar Tarayya Ya Soki ADC
- Mutuwar dan majalisar tarayya Yaya Bauchi Tongo ta jawo ce-ce-ku-ce a siyasar Gombe, yayin wani hadimansa ya bayyana rashin jin dadinsu
- Hadimin marigayin ya zargi jam’iyyar ADC da rashin halartar jana’izar Yaya Bauchi Tongo, yana mai cewa hakan ya bata musu rai sosai
- Ya bayyana cewa za su goyi bayan dan takarar gwamnan APC, Dr Jamilu Isiyaku Gwamna, a zaben 2027
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Gombe - Mutuwar dan majalisar tarayya daga Gombe ya bar baya da kura a bangaren siyasa yayin da aka fara tone-tone.
Wani daga cikin hadimansa, Abubakar Jauro Yaya ya bayyana irin rashin mutunci da jam'iyyar ADC ta nuna masu bayan rasuwar Yaya Bauchi Tongo.

Source: Twitter
Hakan na cikin wata hira da aka yi da shi a shafin El-Shalami TV ya wallafa a Facebook wanda wakilin Legit Hausa ya bibiyi hirar tasu a faifan bidiyo.
Yaron Yaya Bauchi ya yi mamakin ADC
Jauro Yaya ya ce sun yi mamaki babu dan ADC da ya zo ta'aziyyar marigayi Yaya Bauchi Tongo duk da cewa suna cikin jam'iyyar.
Ya ce:
"Mun lura ADC mu ke kaunarta ba ita ke kaunar mu ba, saboda haka mun yanke hukuncin da dukan magoya bayansu domin barranta kanmu, mun fita ne saboda cin mutuncin da aka yi masa ba wai domin marigayi baya nan ba ne.
"Jam'iyyar muna cikinta, marigayi Yaya Bauchi Tongo yana cikinta Allah ya karbi ransa, amma duk yan jam'iyyar a matakin jiha mu dai ba mu ga wani danta da ya zo ya halarci jana'izarsa ba.
"Daga jam'iyyun da muka fita har ma da mambobin majalisar jiha sun zo muka dauki gawarsa har zuwa mahaifarsa Tongo inda za a yi masa jana'aiza, a filin jirgin sama ba mu ga dan ADC kama daga jigo har karamin alhaki a wurin sai mu kadai makusantansa, babu wanda ya zo wannan wurin."

Source: Original
Yaya Jauro ya yaba Jamilu Gwamna
Hadimin marigayin ya ce amma sun ji dadi kan abin da Dr Jamilu Isiyaku Gwamna ya yi masu saboda ya nuna shi dattijo ne.
Daga bisani ya bayyana cewa za su goyi bayan dan takarar gwamnan APC a Gombe, Dr Jamilu Isiyaku Gwamna domin samun nasararsa a zaben 2027.
"Dan takarar jam'iyyar APC na gwamna, Dr Jamilu Isiyaku Gwamna bai Gombe amma ya taso da jirgi da jama'a suka zo suka yi mana ta'aziyya amma jam'iyyar da muke ciki sai bayan kwanaki mun yi sadaka suka zo.
"Wai suka ce mana ai ba su nan sai a wannan lokaci suka samu suka dawo har suka zo domin yi mana gaisuwa."
Ya shawarci al'ummar Gombe ta Arewa da su goyi bayan dan takarar gwamnan APC, Dr Jamilu Isiyaku Gwamna domin samun jagoranci nagari.
Jigon ADC ya koma PDP a Gombe
A baya, an ji cewa sakataren yada labaran ADC na ƙaramar hukumar Gombe ya yi murabus daga jam'iyyar tare da komawa PDP domin mara wa Farfesa Isa Ali Pantami baya.
Ya ce ya sauya sheka ne saboda ya yi imanin Pantami na da ƙwarewa, gogewa da nagartar jagoranci wajen ciyar da Gombe gaba.
Sauyin sheƙar tasa na daga cikin jerin sauye-sauyen siyasa bayan Pantami ya zama ɗan takarar gwamna na PDP a zaɓen shekarar 2027.
Asali: Legit.ng


