Da Gaske Gwamnatin Abba Ce Ta ba Mata Dan Kamfai a Kano? An Gano Gaskiya
- An yi ta yada wasu rahotanni cewa gwamnatin Kano ce karkashin Abba Kabir Yusuf ta raba dan kamfai a wasu mata a jihar
- An gano hotunan wasu mata dauke da jajayen dan kamfai wanda suke rawa da kuma tura sakonni ga Sanata Rabiu Musa Kwankwaso
- Wani binciken gaskiya ya ƙaryata jita-jitar cewa gwamnatin Kano ta raba kayan ga mata, inda aka gano an gyara hotunan da ake yadawa
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru biyar.
Kano - Wani binciken gaskiya ya yi karin bayani game da jita-jitar da ke cewa gwamnatin Kano ta raba dan kamfai ga mata a matsayin tallafi ko kyauta.
Ganin wasu mata da jajayen dan kamfai a Kano suna rawa da wakoki da ake ganin cin mutunci ne ga Rabiu Kwankwaso ya jawo maganganu.

Source: Facebook
Daily Trust ta yi amfani da fasahar binciken hoto ta ELA wadda ta gano cewa an gyarahotunan ne da Abba Kabir a jiki saboda kawo rudani da kawar da hankali.
Sakamakon bincike kan yada mata da dan kamfai
Rahotanni sun nuna cewa hotunan da aka yada a shafukan sada zumunta an gyara su ne domin ƙirƙirar wannan labari mara tushe.
Binciken ya kuma nuna cewa an saka hoton gwamna Abba Kabir Yusuf a cikin hotunan ne domin ya zama kamar shi ne ya bayar da kayan.
Asalin bidiyon da wani Bello King Khan ya wallafa a Facebook ya fito ne daga wasu matasa magoya bayan siyasa da suka taru a gaban gidan gwamnatin Kano suna yin waka da barkwanci.
A cikin bidiyon, an ga suna daga kayan ciki ja suna yi wa wani ɗan siyasa ba’a a cikin yanayin siyasa.
Bayan haka ne aka karkatar da bidiyon da hotunan domin ƙirƙirar labarin cewa gwamnati ta raba kayan ciki ga mata.
Binciken ya kammala da cewa wannan ikirari ƙarya ne, kuma an yi amfani da gyaran hoto da rubuce-rubuce masu ruɗarwa domin yaudarar jama’a.

Source: Twitter
An samu bambancin ra'ayoyi kan lamarin
Mutane da dama daga ciki da wajen jihar Kano sun caccaki matan da cewa siyasa ba cin mutunci ba ne ya kamata a yi ta ba tare da gaba ba.
Duk da haka, akwai wadanda suke ganin matan sun yi daidai saboda ake ci gaba da sukar juna tsakanin bangaren Gwamna Abba Kabir da tsohon mai gidansa, Rabiu Kwankwaso.
Wasu malamai da masu ruwa da tsaki sun yi Allah wadai da hakan inda suke ganin bai dace rashin da'a a siyasa irin haka ta rika faruwa a Kano da ma yankin Arewacin Najeriya ba.
Malami ya caccaki mata masu daga dan kamfai
A baya, kun ji cewa ana cigaba da sukar yadda wasu mata suka fito kan titi dauke da dan kamfai wajen taron jam'iyyar APC mai mulki a jihar Kano.
Malamin addinin Musulunci, Sheikh Ibrahim Aliyu Kaduna ya yi tir da matakin da matan suka dauka, har ya ce hakan fada ne da addini.
Shehin ya nuna cewa suna Allah wadai da duk wadanda suka dauki nauyin matan da abin da suka yi, yana rokon Allah ya kawo mafita ga jihar.
Asali: Legit.ng

