Jamilu Gwamna Ya Fada wa Pantami da Sauran ‘Yan takara yadda Ake Cin Zabe
- Dandalin sada zumunta hanyoyin sadarwa ne kawai, amma ba ya maida farin jinsu ya zama kuri'u a zabe
- Wannan ce hudubar da Ibrahim Shawai ya yi wa masu neman takarar gwamnan jihar Gombe a shekara mai zuwa
- Ubangidan Shawai wato Jamilu Gwamna zai kece raini da ‘yan takara kamar su Isa Ali Ibrahim Pantami
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
M Malumfashi ya shafe shekaru 10 yana kawo labaran Hausa musamman na siyasa, addini, tarihi, wasanni da al’ada
Gombe - Ibrahim Shawai hadimi ne ga Jamilu Isyaku Gwamna, ya yi magana game da abin da yake kai ‘yan takara ga nasara.
Jamilu Isyaku Gwamna shi ne ‘dan takaran APC a zaben sabon gwamnan Gombe, zai gwabaza da irinsu Isa Ali Ibrahim Pantami.

Source: Facebook
Hadimin Jamilu Gwamna ya saki maganganu
Jaridar Punch ta kawo rahoton Ibrahin Shawai yana cewa a rumfar zabe za a goge raini a zaben 2027 ba a dandalin sada zumunta ba.
Bayanin Malam Ibrahim Shawai ya fito ne a ranar Juma’a, lokacin da yake magana game da nasarorin da Jamilu Gwamna yake samu.
Hadimin yana ganin mai gidansa yana kara samun karbuwa gabanin zaben gwamna da za a yi a jihar Gombe a farkon shekarar badi.
Ya ce duk da dandalin sada zumunta suna da muhimmanci a yau wajen tallata takara, sai dai farin jini a kafofin bai nufin yin nasara a zabe.
"Akwai wani muhimmin lamari na gaskiya game da siyasa; dokin shafukan sada zumunta a yau yana suna sa mu manta; ba a yanar gizo ake cikin zabe ba.
"Ana lashe zabe ne ta hanyar mutanen da suka fito rumfar zabe su kada kuri’arsu."
- Ibrahim Shawai
Jawabinsa ya cigaba da cewa ba a Facebook, X, Instagram ko kuwa Tik Tok za a zabi wanda zai mulki mutanen jihar Gombe a 2027 ba.
Shawai yake cewa samun karbuwa a shafukan sada zumuntan ba zai taba maye gurbin samun goyon bayan al’umma a garuruwa ba.
Ya ce:
“A 2027, ba a Facebook, X, Instagram ko TikTok za a zabi sabon gwamna na jihar Gombe ba.
"A rumfunan zabe da ke fadin kananan hukumomin jihar Gombe mutane za su dauki wannan mataki."
- Ibrahim Shawai

Source: Facebook
Abin da yake taimakon Jamilu Gwamna a Gombe
Sannan ya tuna wa jama’a cewa gwaninsa ya fi shekaru 20 yana neman zama gwamna. Sai dai 'dan siyasar bai taba yin galaba a zabe ba.
Shawai ya kuma ce aikin da Gwamna ya yi a gwamnati, kamfanoni, harkokin siyasa da taimakon marasa karfi sun taimaka masa a jihar.
Gwamna sun ziyarci Sanatan Gombe
A kwanaki aka ji labari Gwamnan Gombe, shugaban APC na kasa da Dr Jamilu Gwamna sun ziyarci Sanata Bayero Nafada na jam'iyyar PDP.
Ma girma Inuwa Yahaya, da ɗan takarar gwamna na jam'iyyar APC, Jamilu Gwamna, sun kai ziyara gidan tsohon sanaan ne domin samun goyon baya.
APC tana son hada-kai da Sanata Usman Bayero Nafada na jam'iyyar PDP domin neman kuri'u da ƙarfafa APC gabanin zaɓen da za a yi a 2027.
Asali: Legit.ng

