Majalisar Dokokin Kano Ta Fara Aiki kan Nadin Sabon Mataimakin Gwamna, Mutala Garo
- Majalisar dokokin Kano ta fara bin matakan da kundin tsarin mulkin Najeriya ya dora mata kan batun nadin sabon mataimakin gwamna
- Hakan dai na zuwa ne bayan Gwamna Abba Kabir ya mika sunan Murtala Sule Garo a matsayin wanda zai maye gurbin Aminu Gwarzo
- A zamanta na yau Laraba, Majalisa ta kafa kwamitin wucin gadi da zai tantance Garo kuma ya kawo mata rahoto cikin kwanaki biyar
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Kano, Nigeria - Majalisar dokokin jihar Kano ta kafa kwamitin wucin gadi domin tantance Hon. Murtala Sule Garo, wanda aka nada a matsayin sabon mataimakin gwamna.
Wannan na zuwa ne bayan da Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya aika sunan Garo ga majalisar domin tantancewa da kuma amincewa da shi kamar yadda doka ta tanada.

Source: Facebook
Rahoton Daily Trust ya nuna cewa Majalisar dokokin ta dora wa kwamitin aikin tantance sabon mataimakin gwamnan, sannan ya mika rahoto a makon gobe.
Abba ya tura sunan Garo zuwa Majalisa
A cikin wasikar da Abba ya aike wa kakakin majalisar, Rt. Hon. Jibril Ismail Falgore, da aka karanta a zaman yau Laraba, ya ce an yi nadin ne bisa tanadin sashe na 191(3) na kundin tsarin mulkin Najeriya na 1999.
Nadin ya biyo bayan murabus din tsohon mataimakin gwamna, Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo, wanda ya ajiye mukaminsa a ranar 27 ga Maris, 2026.
Gwamna Abba ya bayyana cewa nadin Garo ya biyo bayan tuntubar masu ruwa da tsaki a fadin jihar, yana mai cewa gogaggen shugaba ne da ke da kwarewa a harkokin mulki.
Mukaman da Garo ya rike a baya
Garo ya taba rike mukamai da suka hada da mai ba gwamna shawara kan harkokin jam’iyyu, shugaban karamar hukumar Kabo, shugaban kungiyar kananan hukumomi ta Najeriya (ALGON) reshen Kano, da kwamishinan kananan hukumomi da masarautu.
Abba Kabir ya kara da cewa kwarewa da biyayya da fahimtar siyasar Kano da Garo ke da ita za su taimaka wajen inganta gudanar da mulki da samar da ayyuka ga al’umma.
Majalisar Kano ta kafa kwamitin tantancewa
Bayan karanta wasikar, kakakin majalisar ya sanar da kafa kwamitin wucin gadi domin tantance Murtala Garo.
Kwamitin, karkashin jagorancin mataimakin kakakin majalisa, ya kunshi shugaban masu rinjaye, babban mai kula da doka, mataimakin shugaban masu rinjaye, da sauran mambobi daga mazabu daban-daban.

Source: Facebook
Ana sa ran kwamitin zai gayyaci Garo domin tantance shi, sannan ya mika rahotonsa ga majalisa a ranar Litinin mai zuwa, kamar yadda Leadership ta ruwaito.
Majalisar ta bayyana cewa za ta hanzarta aikin domin tabbatar da ci gaba da gudanar da harkokin gwamnati ba tare da tsaiko ba.
Abubuwan sani game da Murtala Garo
A baya, mun kawo muku muhimman abubuwan sani game da Mutala Sule Garo, wanda gwamnan Kano yake so ya nada a matsayin sabon mataimakinsa.
Nadin Garo ya girgiza siyasa jihar Kano duk da dai masana da masu bibiyar siyasa sun yi hasashen faruwar hakan tun bayan murabus din Kwamared Aminu Abdussalam Gwarzo.
Tun bayan da Kwamared Gwarzo ya yi murabus, sunan Murtala Garo ya rika karade lungu da sakon Kano, ana ganin shi ne ya fi dacewa da kujerar mataimakin gwamna.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng

