Abba Kabir Yusuf Ya Zabi Sabon Mataimakin Gwamna a Jihar Kano
- Gwamna Abba Kabir Yusuf ya tura sunan Murtala Sule Garo ga majalisar Kano a matsayin mataimakin gwamna da za a tanatance
- Hakan na zuwa ne bayan murabus da tsohon mataimakinsa, Aminu Abdulsalam Gwarzo ya yi da komawa jam'iyyar adawa ta ADC
- Aminu Gwarzo ya koma ADC tare da Sanata Rabiu Musa Kwankwaso yayin da Abba Kabir Yusuf ya shiga jam'iyyar APC mai mulki
CHECK OUT: How to Start Earning with Copywriting in Just 7 Days – Even if You’re a Complete Beginner
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Jihar Kano - Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya mika sunan Murtala Sule Garo ga majalisar dokokin jihar domin tantancewa da amincewa a matsayin mataimakin gwamna.
An sauya mataimakin gwamna a Kano ne bayan tsohon mataimakin Abba Kabir Yusuf, Aminu Abdulsalam Gwarzo ya yi murabus bayan ya ki sauya sheka zuwa APC.

Source: Facebook
Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da Sanusi Bature D-Tofa ya wallafa a Facebook, wacce babban sakataren yada labaran gwamnan, Mustapha Muhammad, ya sanya wa hannu.
Matakin nada Murtala Garo da Abba ya yi
Gwamnatin Kano ta ce nadin ya yi daidai da sashe na 191(3) na kundin tsarin mulkin shekarar 1999, wanda ke bai wa gwamna ikon nada mataimakin gwamna idan aka samu gurbi.
An samu gurbi a matsayin ne bayan murabus din tsohon mataimakin gwamna, Abdussalam Gwarzo, a ranar 27 ga Maris, 2026.
Bayan tattaunawa da masu ruwa da tsaki, gwamnan ya bukaci majalisar jihar Kano ta amince bukatar nada Murtala Garo a matsayin mataimakin Abba Kabir Yusuf.
Daily Trust ta wallafa cewa sanarwar ta ce:
"Bayan gudanar da tattaunawa mai fadi da masu ruwa da tsaki, gwamnan ya bukaci majalisar da ta amince da bukatar nadin Garo."
Murtala Sule Garo mai shekaru 48 gogaggen mai gudanar da harkokin siyasa ne, wanda ya shafe sama da shekaru 29 yana aiki a mukamai na zabe da na nada.

Kara karanta wannan
Mataimakin gwamna ya gina sababbin masallatai 50 don taimakawa addinin musulunci a Najeriya
Wane ne Mutala Garo a siyasar Kano?
An ce Murtala Sule Garo mai shekaru 48 gogaggen mai gudanar da harkokin siyasa ne, wanda ya shafe sama da shekaru 20 yana aiki a mukamai daban-daban.
Ya taba rike mukamin sakataren shirye-shirye na jam’iyyar APC a jihar, mai ba gwamnan Kano shawara na musamman, da kuma zababben shugaban karamar hukumar Kabo.

Source: Facebook
Haka kuma ya taba zama shugaban ALGON a Kano, kwamishinan kananan hukumomi da harkokin sarauta, da kuma dan takarar mataimakin gwamna na jam’iyyar APC a zaben 2023.
Abba Kabir ya ce nadin nasa na daga cikin kokarin karfafa shugabanci da ci gaba da inganta ayyukan yi wa jama’a hidima a jihar Kano.
An daga shari'ar masarautar Kano
A wani labarin, mun kawo muku cewa babbar kotun tarayya ta dage sauraron shari'ar da aka shigar game da masarautun Kano zuwa bayan zaben 2027.
Rahotanni sun nuna cewa an daga shari'ar ne bayan wani korafi da wadanda aka shigar da kara suka yi, inda aka ba masu kara lokaci domin su kare kansu.
Babba Dan Agundi da ya shigar da karar ya bayyana cewa sun amince da matakin kotun kuma za su shirya kare kansu idan lokaci ya yi.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng
