Wata Sabuwa: Gwamna Ya Gano Shirin da APC Ta Yi wajen Tattara Sakamakon Zaben Osun

Wata Sabuwa: Gwamna Ya Gano Shirin da APC Ta Yi wajen Tattara Sakamakon Zaben Osun

  • Gwamnan Osun, Ademola Adeleke, ya zargi APC da shirin kai sakamakon zaɓe kai tsaye zuwa cibiyar tattarawa maimakon bin tsarin da aka tanada
  • Adeleke ya kuma zargi wani ɗan sanda da aka kira “London” da zuwa Ede domin kawo cikas ga zaɓen gwamnan da ke gudana
  • Gwamnan ya yi kira ga jami’an tsaro da su binciki zargin tare da tabbatar da tsaron masu zaɓe

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum

Osun, Nigeria - Gwamnan Osun, Ademola Adeleke, ya zargi jam’iyyar APC da shirin kauce wa tsarin tattara sakamakon zaɓe da aka tanada yayin zaɓen gwamnan jihar da ake gudanarwa yau Asabar.

Adeleke ya bayyana hakan ne jim kaɗan bayan ya jefa ƙuri’arsa a rumfar zaɓe ta 9, Ward 2, a ƙaramar hukumar Ede North.

Gwamna Adeleke.
Gwamnan jihar Osun, Ademola Adeleke yayin ganawa da yan Accord Hoto: Ademola Adeleke
Source: Facebook

Jaridar Leadership ta rahoto cewa gwamnan ya isa rumfar da ƙarfe 8.29 na safe, minti ɗaya kafin lokacin da aka tsara fara zaɓe.

Kara karanta wannan

Abubuwa 9 da za su yi tasiri wajen nuna wanda ya yi nasara a zaben Osun

Ya jefa ƙuri’arsa da ƙarfe 8.32 na ssfiya, yayin da masu zaɓe da jami’an wucin gadi na INEC tuni suka hallara a rumfar.

Me Adeleke ya ce game da sakamako?

Da yake magana bayan jefa ƙuri’a, Adeleke ya ce ya samu labarin cewa akwai shirin ɗaukar sakamakon zaɓe kai tsaye daga rumfunan zaɓe zuwa cibiyar tattara sakamako.

A cewarsa, hakan zai kauce wa tsarin da ya kamata a bi daga rumfunan zaɓe zuwa mazabu sannan zuwa ƙananan hukumomi kafin a kai sakamakon cibiyar tattara sakamakon.

“Na samu sahihin bayani cewa ba sa son bin tsarin da aka saba, wato daga rumfunan zaɓe zuwa mazabu, sannan zuwa ƙananan hukumomi. Maimakon haka, suna son kai sakamakon kai tsaye zuwa cibiyar tattarawa.”

Ya ce bai kamata a bar irin wannan abu ya faru ba, yana mai kira ga jama’ar jihar su sanya ido kan yadda ake gudanar da tattara sakamakon zaɓen.

Kara karanta wannan

Zaben Osun: Ana rige rigen sayen kuri'un talakawa da kudi da abinci

“Wannan ba abin karɓa ba ne. Dole ne su bi ƙa’idojin da aka tanada, shi ya sa nake sanar da jama’ata su sanya ido,” in ji Adeleke.

Me ya ce game da ɗan sandan?

A rahoton Vanguard, gwamnan ya kuma yi zargin cewa wani ɗan sanda da ya bayyana da suna “London” daga Fatakwal na iya kasancewa an kawo shi Ede domin kawo cikas ga zaɓen.

Tutar APC.
Tautar jam'iyyar APC mai mulki a Najeriya Hoto: @APCNig
Source: Twitter

Adeleke ya yi kira ga Sufeto Janar na ’Yan Sanda, Kwamishinan ’Yan Sandan jihar da sauran jami’an tsaron da aka tura domin kula da zaɓen su binciki batun tare da ɗaukar matakin da ya dace.

“Na fahimci cewa APC ce ta kawo shi jihar Osun domin ya yi wani aiki na musamman da kuma kawo cikas a garina, Ede, don ya hana mutane su samu damar jefa ƙuri’a,” in ji shi.

Abubuwan da za su yi tasiri a zaben Osun

A baya, mun kawo muku muhimman abubuwan da za su iya yanke wanda zama gwamnan jihar Osun na gaba bayan zaben 2026.

‘Yan takara 14 ne ke neman kujerar, amma uku ne suka fi jan hankali, wato Gwamna Ademola Adeleke na Accord, Bola Oyebamiji na APC da Najeem Salam na ADC.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ahmad Yusuf avatar

Ahmad Yusuf (Hausa editor) Ahmad Yusuf ma'aikacin jaridar Legit.ng sashin Hausa ya fara aiki a 2021, ya kware wajen kawo labarai da rahotanni da suka shafi siyasa da al'amuran yau da kullum. Matashin ɗan jaridar ya koyi Lissafi a digirinsa na farko a Jami'ar Kimiyya da Fasaha da ke Wudil, Kano (KUST) ya kuma samu shaidar kwarewa a fannin aikin jaridar zamani daga Reuters a 2022. Kafin fara aiki da Legit Ahmad ya yi aiki da jaridu da dama na turanci da Hausa tun 2012. Mail: ahmad.yusuf@corp.legit.ng 07032379262