Gobar Daji Ta Mayar da Sama Ja Wur, ana Ceto Mutanen da Suka Makale
- Wata gobara ta mamaye gidaje a wani shahararren wurin yawon buɗe ido a Croatia, inda mutum ɗaya ya mutu, 40 suka jikkata, sannan aka kwashe mutane 1,200
- Haka kuma, an kwashe daruruwan mutane daga wani wurin yawon buɗe ido a arewacin Girka da wani ƙauye a kudu maso yammacin Faransa saboda gobarar daji
- Hukumar Tarayyar Turai ta yi gargadin cewa wasu sassan nahiyar na fuskantar matsanancin yanayi da ke ƙara haɗarin gobarar daji sakamakon tsananin zafi da fari
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Omis – Wata mummunar gobara ta mamaye gidaje a garin Omis da ke gabar tekun Dalmatian a Croatia cikin daren Alhamis, inda mutum ɗaya ya mutu, yayin da wasu 40 suka samu raunuka.
An tilasta wa kusan mutane 1,200, ciki har da mazauna yankin da masu yawon buɗe ido, barin gidajensu domin tsira daga gobarar.

Source: Facebook
Reuters ta rahoto cewa gobarar ta haifar da rudani yayin da mutane suka yi ta guduwa cikin motocinsu, yayin da harshen wutar ya mamaye hanyoyi da wuraren da ke kewaye da garin.
Barnar da gobarar ta yi
Wani mazaunin yankin mai suna Ljubica Uglesic ya bayyana yadda lamarin ya kasance, yana cewa wutar ta rika cinye bangarorin hanya, har ta kai ga motarsa ta kama da wuta.
Gobarar ta kuma sanya sararin samaniya ya koma ja saboda tsananin tashin harshen wutar.
Babban kwamandan kashe gobara na Croatia, Slavko Tucakovic, ya ce gobarar ta fara raguwa a safiyar Juma'a.
Jami'ai sun gano gawar mutum ɗaya da gobarar ta ƙone, yayin da daga cikin mutane 40 da aka kai asibitin Split, bakwai ke cikin mawuyacin hali.
An kwashe mutane 300 a Girka
A arewacin Girka, gobara ta tilasta wa sama da mutane 300 barin garin Siviri ta hanyar teku.
Mutanen da suka hada da mata da yara da masu ɗauke da dabbobin gida sun yi amfani da ƙananan jiragen ruwa da kwale-kwale wajen tserewa daga gobarar da ta mamaye dajin da ke kusa da garin.

Source: Getty Images
Jami'an tsaron gabar teku sun ce an kwashe sama da mutane 300 ta jiragen ruwa daga yankin, wanda ke kan wani yanki mai cike da dazuzzuka, itatuwan zaitun da rairayin bakin teku.
An tura jami'an kashe gobara sama da 140, jiragen sama tara da jirage masu saukar ungulu bakwai domin yaƙar gobarar.
Haka kuma, wasu jiragen kamun kifi sun shiga aikin kwashe mutanen daga yankin.
Ga bidiyon gobarar da shafin Globe Update ya wallafa a X:
An yi girgizar ƙasa a Masar
A wani labarin, mun ruwaito cewa wata girgizar ƙasa mai ƙarfin maki 5.0 ta afku a gabar tekun Masar da sanyin safiyar Litinin a makon da ya wuce.
Binciken Hukumar Binciken Yanayin Ƙasa ta Amurka (USGS) ya nuna cewa girgizar ta afku ne da misalin ƙarfe 3:00 na safe, inda cibiyarta take kimanin kilomita 36 daga arewa maso gabashin birnin Suez.
Cibiyar Binciken Kimiyyar Ƙasa ta Jamus (GFZ) ta auna girgizar da maki 5.4, tare da bayyana cewa zurfinta ya kai kilomita 10, yayin da ba a samu rahoton mace-mace ko asarar dukiya nan take ba.
Asali: Legit.ng

