"Ba Za Ta Tsira ba": Tsohon Kakakin PDP Ya Hango babbar Musibar da Ke Tunkaro APC
- Kola Ologbondiyan ya ce jam’iyyar APC mai mulki a kasa za ta fuskanci rikicin sauyin sheƙa, kamar yadda PDP ke fama da matsalar a yanzu
- Sauya shekar Gwamna Sheriff Oborevwori da Sanata Ifeanyi Okowa zuwa APC ya jefa PDP cikin ruɗani, bayan mulkin shekaru 26 a jihar Delta
- Ologbondiyan ya yi hasashen cewa jam'iyyun ACN da CPC da suka kafa APC sun fara samun sabani, alamar rikicin da zai rusa jam'iyyar APC
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Tsohon mai magana da yawun jam’iyyar PDP na ƙasa, Kola Ologbondiyan, ya bayyana cewa jam’iyyar APC mai mulki ba za ta tsira daga rikicin sauyin sheƙa ba.
Ologbondiyan na martani ne kan sauya shekar manyan shugabannin siyasa a jihar Delta, ciki har da Gwamna Sheriff Oborevwori da Sanata Ifeanyi Okowa, zuwa jam’iyyar APC.

Asali: Twitter
Wannan sauya shekar ya bar jam’iyyar PDP, wadda ta yi mulki a jihar fiye da shekaru 20, cikin rudani, ba tare da wata madafa ba, inji rahoton Vanguard.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ologbondiyan ya magantu kan sauya sheka a PDP
Bayan kwana biyu da wannan lamari, Gwamna Umo Eno na jihar Akwa Ibom, ya nuna alamar cewa shi ma ya na shirin barin PDP.
Duk da cewa wannan guguwar sauyin sheƙa daga PDP na girgiza shugabancin jam’iyyar, Ologbondiyan ya ce wannan ba abin damuwa ba ne.
A cewar tsohon kakakin PDP, irin wannan sauyin sheka ya zama tamkarar al’ada a siyasar kasar, a duk lokacin da ake shirye-shiryen zaɓe.
Yayin wata tattaunawa a Arise Television a ranar Laraba, jigon PDP ɗin ya bayyana cewa yanzu haka guguwar sauyin sheƙa na tasowa a cikin jam’iyyar APC.
Akwai matsala a APC inji Kola Ologbondiyan
Ologbondiyan ya yi nuni da cewa tuni wasu daga cikin jiga-jigan 'yan siyasa da suka kafa APC sun fara zazzafar muhawara kan zama a cikinta ko su sauya sheka.
Ya ambato bangaren CPC, wadda tsohon shugaban ƙasa Muhammadu Buhari ya jagoranta, ya na cewa wasu daga cikin mambobinta sun fara shiri na ficewa daga APC.
A cewar Ologbondiyan:
“Yanzu karar gangar PDP ce ke tashi, kowa na magana kan sauyin sheƙar 'ya'yanta. Amma ina tabbatar muku da cewa nan ba da daɗewa ba, za a fara kada wannan gangar a APC.
“Idan kana bibiyar abin da ke faruwa a APC, za ka fahimci cewa bangaren ACN wanda Shugaba Bola Tinubu ya jagoranta wajen kafa APC, yanzu ya fara tarwatsewa."

Asali: Twitter
"Alamar rushewar APC" - Ologbondiyan
Tsohon mai magana da yawun PDP din ya kara da cewa:
“Kuma na tabbata kun gani a kwanakin baya lokacin da CPC, bangaren da tsohon shugaban ƙasa Buhari ya kawo cikin APC, suka fara zanga-zanga.
"Wasu suna cewa za mu tsaya, ba za su bar APC ba; Wasu kuma suna cewa ba wanda ya isa ya yimagana da yawunsu. Wannan duk alama ce cewa rushewar APC a nan gaba."
A cewar Ologbondiyan, wannan guguwar sauya sheka daga PDP “al’ada ce ta siyasa” da ke bukatar ‘yan siyasa su dinga haɗewa da warwatsewa don shirin zaɓe.
PDP ta kira taron gaggawa kan sauya sheka
A wani labarin, mun ruwaito cewa, jam’iyyar PDP za ta gudanar da taron gaggawa a Abuja a ranar Talata, 29 ga Afrilu, 2025 domin duba matsalolin da suke addabarta.
Rahotanni sun bayyana cewa jam’iyyar ta rasa fiye da manyan 'ya'yanta 300 zuwa APC tsakanin Fabrairu 2024 da Fabrairu 2025 sakamakon rikicin cikin gida.
Majiyoyi sun ce za a tattauna batun sauya sheƙa, shirye-shiryen babban taron zaɓe, da kuma shawarwarin da gwamnonin PDP suka gabatar kwanan nan.
Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.
Asali: Legit.ng