Shirin Ficewar Gwamna daga PDP Ya Girgiza Jam'iyyar, Ta ba Shi Shawara

Shirin Ficewar Gwamna daga PDP Ya Girgiza Jam'iyyar, Ta ba Shi Shawara

  • Jam'iyyar PDP ta nuna takaicinta kan yiwuwar sauya sheƙar gwamnan jihar Akwa Ibom, Fasto Umo Eno zuwa wata jam'iyya
  • Mataimakin shugaban matasan PDP na ƙasa ya bayyana cewa bai kamata gwamna Eno ya fice daga jam'iyyar tasu ba
  • Timothy Osadolor ya nuna cewa kamata ya yi gwamnan ya maida hankali wajen kawo sauye-sauye a harkar zaɓe maimakon sauya sheƙa

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - Jam’iyyar PDP ta yi magana kan yiwuwar ficewar gwamnan jihar Akwa Ibom, Umo Eno, daga cikinta.

PDP ta buƙaci Gwamna Umo Eno, da ya fi mayar da hankali kan sauye-sauyen tsarin zaɓe maimakon komawa wata jam’iyya, mai yiwuwa APC.

Gwamna Umo Eno
PDP ta bukaci Gwamna Umo Eno ka da ya fice daga jam'iyyar Hoto: Pastor Umo Eno
Asali: Twitter

Mataimakin shugaban matasan PDP na ƙasa, Timothy Osadolor, ya bayyana hakan yayin wata hira ta musamman da jaridar Vanguard ranar Laraba a Abuja.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Me PDP ta ce kan yiwuwar ficewar Umo Eno?

Osadolor ya bayyana yiwuwar ficewar gwamnan daga jam’iyyar a matsayin abin takaici ƙwarai da gaske.

Mataimakin shugaban matasan ya soki yiwuwar ficewar gwamnan, ya jaddada cewa Gwamna Eno, wanda ya amfana daga jam’iyyar PDP sama da shekaru 25, yana da alhakin kare tsarin dimokuraɗiyya a Najeriya.

"Idan kana ɗaukar mutum yana da ƙima da daraja, abin takaici ne idan daga baya ya bayyana a matsayin ƙaramin mutum da ke cikin manyan kaya."
“Abin takaici ne idan waɗanda ka dauka da girma da ƙima, suka zama masu rauni a ainihi. Ina mamakin irin uzurin da gwamnan Akwa Ibom zai bayar dangane da ficewarsa daga jam’iyyar."

- Timothy Osadolor

Shugaban matasan PDP ya bada shawara

Ya ci gaba da cewa, ya kamata shugabannin siyasa su tsaya tsayin daka da al’ummar Najeriya wajen ganin an samu gyare-gyare masu muhimmanci a harkar zaɓe, maimakon su yi ta sauya sheƙa saboda tsoro.

Wannan kiran ya zo ne a daidai lokacin da ake raɗe-raɗin cewa Gwamna Eno na ƙoƙarin komawa APC domin gujewa yiwuwar murɗe masa zaɓe a zaɓen 2027 mai zuwa.

Osadolor ya nuna cewa Gwamna Eno wanda ya daɗe a PDP, yanzu yana tunanin ficewa daga jam’iyyar ne saboda fargabar cewa za a yi masa maguɗi.

"A gaskiya wannan gwamna ya shafe fiye da shekaru 25 yana cikin PDP, mutumin da aka bai wa dama sau da yawa domin ya bar wani tarihi mai kyau a dimokuraɗiyyar mu. Yanzu saboda tsoro kawai, yana tunanin tserewa kafin zaɓen 2027."

- Timothy Osadolor

Gwamna Umo Eno
PDP ta ba Gwamna Umo Eno shawara Hoto: Pastor Umo Eno
Asali: Facebook

Wace shawara aka ba Gwamna Eno?

Osadolor ya bukaci Gwamna Eno da ya yi tunani mai zurfi game da irin tarihi da yake son ya bari, da kuma amfani da matsayinsa a matsayin gwamnan jiharsa mai arzikin man fetur don kare adalci da gaskiya a harkar zaɓe.

"Ina kira ga gwamnan da ya sake tunani. Yana da damar barin wani tarihi da za a riƙa tunawa da shi a cikin shekarun da ke tafe."

“A matsayinsa na gwamna mai ƙarfi, ya kamata ya jagoranci ƴan Najeriya wajen neman sauye-sauye masu inganci a tsarin zaɓe, da tabbatar da cewa zaben 2027 ya kasance sahihi."

- Timothy Osadolor

Gwamna Umo Eno ya goyi bayan Tinubu

A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Akwa Ibom, Umo Eno, ya nuna goyon bayansa ga tazarcen Bola Tinubu a 2027.

Gwamna Umo Eno ya bayyana cewa Shugaba Tinubu ya cancanci ya yi shekara takwas yana mulkin Najeriya.

Hakazalika ya nuna cewa ya kamata a bari shugaban ƙasan ya kammala ayyukan alherin da yake yi a faɗin ƙasar nan.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng