2027: Gwamnan Delta Ya Sauya Sheka daga PDP zuwa APC

2027: Gwamnan Delta Ya Sauya Sheka daga PDP zuwa APC

  • Gwamnan jihar Delta, Sheriff Oborevwori, ya sauya sheƙa daga jam’iyyar PDP zuwa APC a wani babban sauyin siyasa da ke ɗaukar hankula
  • Ya sanar da haka ne a wata ganawar sirri da aka gudanar a gidan gwamnati da ke Asaba, inda manyan shugabannin APC suka karɓe shi hannu biyu biyu
  • Sauyin jam’iyyar ya zo daidai lokacin da ake fuskantar sauye-sauye a siyasar jihar Delta, tare da shirye-shiryen murza gashin baki domin zaɓen 2027

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Delta - A wata sanarwa da ke da ɗaukar hankali, Gwamnan jihar Delta, Hon. Sheriff Oborevwori, ya sanar da sauya sheƙarsa daga jam’iyyar PDP zuwa APC mai mulki.

Sanarwar ta fito ne bayan wata ganawa ta sirri da aka yi a gidan gwamnati da ke Asaba, babban birnin jihar, a ranar Laraba, inda manyan shugabannin APC suka tarbe shi.

Sheriff Oborevwori
Gwamnn Delta ya koma APC. Hoto: Delta State Government
Asali: Twitter

Jaridar Arise News ta wallafa cewa a zaben 2023 Sheriff Oborevwori ya lashe zaben gwamna a karkashin PDP.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Vanguard ta walllafa cewa Sheriff Oborevwori ya bayyana sauya shekar a matsayin matakin da zai ƙarfafa haɗin gwiwar siyasa da tabbatar da ci gaban jihar Delta a matakin ƙasa.

'Yan APC sun sun yi hasashen sauya shekar

Tun kafin sanarwar a hukumance, wasu fitattun shugabannin APC na yankin Ijaw a jihar Delta sun yi hasashen cewa gwamnan zai fice daga PDP zuwa APC.

A wata ganawa da suka yi a Effurun, karamar hukumar Uvwie, sun jaddada cewa Oborevwori yana dab da komawa APC.

Jagoran ganawar, High Chief Michael Johnny, ya bayyana cewa:

“Sheriff zai koma APC. Kada ku damu da abin da ake cewa a kafafen sada zumunta—zai shiga APC.”

Ya ƙara da cewa APC tana maraba da kowa, musamman 'yan Ijaw da ke son shigowa domin ƙarfafa jam’iyyar a jihar.

Jagoran jam'iyyar ya ce:

“Duk lokacin da kuka shirya, muna nan za mu karɓe ku hannu bibbiyu,”

Taron da aka yi a Effurun ya zama wani gagarumin taron ƙarfafa hadin kai da nuna ƙarfin APC a yankin.

Daga cikin manyan ’yan siyasar da suka halarci taron akwai Raymos Guana, High Chief Mike Seikegba, Mr. Joe Ekiyor, Sir Theodore Ezonfade, Chief Davi Omare, Hon. Ebitonmo Alapala.

Haka zalika akwai Chief Promise Lawuru, Hon. Wurus Fortune, Injiniya Joseph Izonowei Sozaowei da kuma Kwamared Blackman Edisemi Mule.

Ganduje
APC ta yi hasashen sauya shekar gwamnan Delta. Hoto: Abdullahi Umar Ganduje
Asali: Twitter

Sauya shekar Gwamna Oborevwori ta zo ne a daidai lokacin da ake ta samun ficewar wasu jiga-jigan PDP zuwa APC a yankin Delta ta Kudu.

Tinubu ya gana da Fubara a London

A wani rahoton, kun ji cewa gwamnan jihar Rivers da aka dakatar a watan Maris, Siminalayi Fubara ya gana da shugaban kasa Bola Tinubu a London.

Rahotanni sun nuna cewa ganawar Bola Tinubu da Siminalayi Fubara ta mayar da hankali ne a kan yadda za a samu cikakken zaman lafiya a jihar Rivers.

Ana hasashen cewa Bola Tinubu zai yi wata ganawa da Fubara, 'yan majalisar jihar, Nyesom Wike domin dawo da gwamna ofis bayan dakatar da shi.

Wanda ya tantance Muhammad Malumfashi, babban edita a Legit.ng.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng