Ba Atiku ba Obi ba: 'Dan Takarar Shugaban Kasa da Cancanci 'Yan Adawa Su Tsaida a 2027'
- Jam’iyyar APM mai reshen jihar Legas ta ce gwamnan Oyo, Seyi Makinde, ya fi dacewa ya zama dan takarar shugaban kasa na hadakar ‘yan adawa a 2027
- Jam’iyyar ta ce Makinde na da kwarewa, nagartaccen tarihin shugabanci da karbuwar da za su taimaka wajen hada kan ‘yan adawa
- A cewar APM, yadda Makinde ke tafiyar da gwamnatin Oyo ya nuna cewa gwamnati na iya yi wa jama’a aiki yadda ya kamata
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da kwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishadi
Jihar Legas - Jam’iyyar APM reshen jihar Legas ta ce gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, shi ne dan takarar shugaban kasa da ya fi dacewa hadakar jam’iyyun adawa za ta iya tsayarwa a babban zaben 2027.
Gwamna Seyi Makinde shi ne dan takarar shugaban kasa na jam’iyyar APM a zaben shekarar 2027.

Source: Twitter
Jaridar TheCable ta ce a wata sanarwa da ya fitar ranar Litinin, 3 ga watan Agustan 2026 a Legas, sakataren yada labarai na APM a jihar, Ayodele Kazeem, ya ce Makinde na da halayen shugabanci na gari.
Ya ce Gwamna Makinde na da kwarewa da karbuwar kasa da ake bukata domin hada kan ‘yan adawa tare da bai wa ‘yan Najeriya zabin da za su iya yarda da shi.
Kazeem ya ce matsayar APM ta samo asali ne daga tarihin shugabancin Makinde, salon mulkinsa da irin nasarorin da ya samu, ba wai saboda son zuciya ko wata manufa ta siyasa ba.
APM ta goyi bayan Makinde
“APM a Legas ta yi imanin cewa idan da gaske ‘yan adawa suka himmatu wajen bai wa ‘yan Najeriya sahihin zabi a 2027, to Gwamna Seyi Makinde ya fi kowa cancanta, kwarewa da iya hada kan jama’a domin ya daga tutar hadakar."
“A cikin shekarun da suka gabata, Gwamna Makinde ya gina suna a matsayin jagoran da ke gudanar da mulki cikin taka-tsantsan, gaskiya da sakamakon da ake iya gani."
“A karkashin gwamnatinsa, jihar Oyo ta samu manyan zuba jari a bangaren tituna, kiwon lafiya, ilimi, noma da tsaro, tare da inganta yadda ake tafiyar da harkokin kudi da bunkasar tattalin arziki.”
- Ayodele Kazeem
Abin da Najeriya ke bukata
Kazeem ya ce a wannan lokaci, ‘yan Najeriya na bukatar shugaban kasa da ya fahimci yadda ake gudanar da mulki yadda ya kamata. Ya ce Gwamna Makinde ya nuna cewa gwamnati na iya aiki domin amfanin jama’a.
“Ya nuna a kai a kai cewa ana iya tafiyar da dukiyar jama’a cikin rikon amana ba tare da almubazzaranci ba. Ya tabbatar da cewa ana iya samun ci gaba ta hanyar kyakkyawan tsari, ba farfaganda ba."
"Ya kuma nuna cewa gwamnati na iya aiwatar da ayyukan da jama’a za su gani tare da kiyaye tsari mai kyau wajen tafiyar da harkokin kudi."
“Baya ga irin nasarorin da ya samu a jihar Oyo, Makinde na da halayen da suka sa ya dace musamman wajen hada kan ‘yan adawa."
“Yana da kyakkyawar alaka da ‘yan siyasa daga jam’iyyu daban-daban. Haka kuma, gwamnonin jihohi na girmama shi ba tare da la’akari da jam’iyyunsu ba.”
Makinde na da karbuwa a fadin kasa
Kazeem ya bayyana Makinde a matsayin jagoran da ke iya hada bangarori, yana mai cewa ya gina dangantakar siyasa a yankuna daban-daban na Najeriya.
Ya ce halin natsuwar Makinde, iya sauraron jama’a da salon gina matsaya ta hanyar fahimtar juna su ne abubuwan da Najeriya ke bukata bayan shekaru na rikice-rikicen siyasa da rarrabuwar kawuna.
“Ba kamar wasu ‘yan siyasa da karbuwarsu ta takaita ga yanki daya ba, Gwamna Makinde na da halin dattako da amincin da za su iya jawo masa goyon baya a fadin Najeriya." In ji sanarwar

Source: Facebook
Makinde ya sayo jirage
A wani labarin kuma, kun ji cewa gwamnan jihar Oyo, Seyi Makinde, ya karɓi jiragen leƙen asiri guda biyu da gwamnatinsa ta saya domin inganta tattara bayanan sirri.
Makinde ya bayyana cewa jiragen za su taimaka wajen sa ido kan manyan yankuna na jihar cikin sauri, domin tallafa wa jami'an tsaro.
Asali: Legit.ng


